SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Ok Sir ” ta faɗi ta fita tana ƙunƙuni…

…………………

Farida ta zaunar da Baaba Sabuwa ta yi ma ta bayanin abinda ke faruwa tsakanin AbdulWahab da Maijiddah. Da kuma ƙudurin AbdulWahab ɗin na son turo iyayen sa.
Baaba Sabuwa ta ce idan dai da gaske ne za ta sanar da Baffa Musa sai ya basu lokaci.
Farida ta ce ” yanzu Baaba Sabuwa ba ki yarda ba kenan?”

“Farida na fi kowa damuwa da rashin auren Maijiddah, sai dai maganar AbdulWahab ɗin ne ta zo kamar almara”

“Addu’arta ne ya ƙarbu. Kin san tunda na zo gidan nan kullum dare Maijiddah sai ta fi awa ɗaya tana sallah tana roƙon Allah ya bata miji. Ko ba ta sallah sai ta tashi ta roƙeshi. To Ubangiji mai jin ƙan bayinsa sai ya kawo ma ta wanda ba ta taɓa tsammani ba. Baaba Sabuwa ki godewa Allah kawai ki cigaba da yi ma ta addu’a”

Cikin satin Alhaji Bello Hassan Kachako da wa su wakilan AbdulWahab su ka zo. Bakin Baffa Musa kasa rufuwa yai, shi ba dan ya gani zahiri ba ko lokacin da Baaba Sabuwa ta gaya ma sa bai gama yarda ba. Su zuwan da su ka yi idan an basu Maijiddah su na so bikin kar ya ɗau lokaci.

Baffa Musa kam zani ne ta tadda muje. Dan haka ya amince da sauri.
Sati na zagayowa aka kawo sadakin Maijiddah, dubu ɗari da hamsin. Wata uku aka sa biki su ka nemi a dawo da shi wata biyu Baffa Musa ya amince. Duk da kuwa bashida kuɗi a ƙasa dan ya gama kashe kuɗi wajen bikin su Salima. Sai dai ba zai bari damar da ya ke nema tun da jimawa ya kuɓuce ma sa ba. Allah na gani ya so a haɗa bikin Maijiddah da Farida sai dai hakan bai yiwu ba. ‘Yan uwan Rayyan sun ce Rayyan yana so ya haɗa ginin sa kafin ayi biki…

Wannan babban al’amari ya sa kishiyoyin Baaba Sabuwa kowa yai tsit dan abin ya ba su mamaki, duk cikin yaran da aka aurar ba mai sa’an Maijiddah. A gaba ɗaya yaran ma Yayar Maijiddah wadda ita Maijiddan ta biyo wato Bilkisu ita kaɗai ta auri wanda yai boko sosai kuma ya ke da hali yana aiki a kamfanin insurance, sai gara-gara mijin Kulthum wanda shima ma’aikacin Kamfanin Airtel ne.

Abu kamar mafarki fa yadda su ke tsokanarta da Matar Custom sai ga shi har sadakinta an bayar saura a ɗaura aure kawai.

………………….

Tana kwance wayarta ya fara ringing tana ɗagawa ta ga Sir Najeeb. Mi zai sa ya kira a wannan lokaci? Ta dai ɗauki kiran.

“Miss Salihu, i asked you to send me a copy of the proposal before you leave. What happen?”

“Ya Allah! Na manta zan turo ma ka yanzu”…

Yana zaune yana sipping tea ɗin sa ta turo ma sa saƙon. Sai da ya duba ya ga aikin bai yi kyau ba akwai gyararraki. Nan ya sake kiran ta.
Tana amsa waya ya fara faɗa “Miss Salihu what is this? Mi ki ka turomin? Haka na ce ki yi?” Jin ƙorafin yai yawa ya sa ta ce

“Domin kai ƙorafi danna ɗaya, domin neman ƙarin bayani gameda aikin da aka maka danna biyu, domin magana da Aisha Farida kai tsaye danna uku….”

Ba ta gama ba ya kashe wayar.
Farida ta yi tsaki, ” shi agidan ma ba za ka huta ba aiki, ya san da ya na yi wannan ɗin. Wallahi ba za ka kasheni da aiki ba”

Najeeb ya cillar da wayar yana cize leɓen sa na ƙasa. He’s waiting for the perfect time ya aiwatar da ƙudurinsa, just a perfect time. Yarinyar nan sai ta raina kanta…

????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Free page

0️⃣0️⃣8️⃣

Washegari a office Najeeb bai ma ta maganar shaƙiyancin da ta ma sa ba, iya kaci tana nuna ma sa proposal ɗin ya ce ta je ta gyara.

Tana aiki sai ga Sister Munibat ta shigo.

“Sister Farida ya aiki”

“Alhamdulillah”

“Sir Najeeb yana ciki?”

“Eh ki shiga”

Minti biyar sai ga ta ta fito har za ta wuce ta ce ” Sister Farida ɗan bani ruwa mai sanyi ma na, fridge ɗin office ɗina ya ɓaci”

Farida ta miƙa ma ta satchet water mai sanyi.

“Na gode sister” har za ta tafi Farida ta ce ” yawwa idan kina son zoɓo ko kunun aya, gobe zan fara zuwa da shi”

Sister Munibat ta ɗan yi dariya ta ce ” a cafeteria za ki dinga ajiyewa?”

“A’a anan office ɗina, mai so sai ya zo ya siya”

“Toooo, ke da Sir Najeeb kunfi kusa, amma bana tunanin zai amince da haka”

“Sister Munibat ke dai ki sanar da ‘yan wajen kun nan kawai”

Sister Munibat tace “Allah ya kawo kasuwa” Farida ta amsa da Amin…

Washe gari Farida ta haɗa zoɓo gora shabiyar da kunun aya gora goma. Tun kan ta shigo ta ɗan bibbiya wajen mutanenta ta sanar da su, wasu a lokacin su ka ƙarɓa dan wa ya ke da garajen zuwa har Office ɗin Sir Najeeb siyan zoɓo…

Tana aiki a computer Najeeb da Anas su ka fito.

” ‘yar uwa sannu da aiki ko”

“Na gode Yayana”

Har zai shige ta ce ” Ya Anas ga zoɓo fa, harda kunun aya”

” ƙanwata kenan, kina sha’aninki”

“Yaya ai mai neman kuɗi kam kowani ƙofar samu ya gani shiga ya ke”

“Well Hakane, Allah ya kawo kasuwa”

“Na kawo ma ka zoɓo ko kunun?”

“Ki bari anjima yanzu zamu fita wani waje nida mutumunki ne”

Kafin ya gama surutun sa Najeeb kam ya yi gaba…

…………………

Tana tsugunne gaban fridge tana duba sauran zoɓonta wanda na Anas ne da na Sir Najeeb da ta ajiye mu su, yanzu Yakubu ya zo ya ƙarɓi na sa.

“Miss Salihu”

A firgice ta juyo dan ba ƙaramin tsorata ta yi ba.
“Ya Allahu! Sir Najeeb ai sai ka sa hawan jinin mutum ya tashi. You scared the hell out of me”

“To my office, Now”

Yana shigewa ta fara mimicking na sa ” Miss Salihu, to my office now nnnnnnaa. Mtsww”

Ta ɗau zoɓo ɗaya wanda yai sanyi sosai ta shiga da shi.
Tana zuwa ta ajiye ma sa akan table ta ce “Sir na san kafi son shan tea ko coffee amma wannan zoɓon one in town ne. Albarkacin haƙƙin maƙotaka za ka dinga samun kyautar goran zoɓo ɗaya”

Tunda ta fara magana ya zuba ma ta ido har sai da ta kai aya. Duk yadda ya ke jin tsanar yarinyar nan wannan quality na ta na rashin tsoro yana impressing na shi. Idan ka cire Anas duk girman Kamfanin nan babu wanda ke iya tsayawa gaban sa ya faɗi magana son ransa sai ita. People fear him, but this skinny girl idonta ƙyam ya ke duk lokacin da ta ke gabansa babu tsoro ko fargaba a tattare da ita.

“Sir ka taɓa zoɓon ka ji, Allah sai ka yi santi”

“Miss Salihu, duk wani rules and regulations na wannan Kamfani yana da muhimmanci. But na ga alama ba ki ɗauke su da daraja ba. You dont wear cooperate clothes, you eat in the office you… you… you and only you Miss Salihu”

“Haba Sir, tun ranan da kace na dena cin abinci a Office fa na dena”

“Oh really, and that yellow thing you ate in the morning yersterday?”

“Kai Sir ya akayi ka gani? Ban karya ba na fito shine na karya a office”

“I see. And this” ya nuna goran zoɓo da ta ajiye”

“Alakoro na kawo ma ka fa. Tunda dai Allah ya haɗamu maƙotaka”

“Look Miss Salihu, get this in to your dumb skull. Office ba wajen ciye-ciye ko kasuwanci bane, you keep on doing it i keep on cutting your salary. Now out of my office”

Ji take kaman ta make shi amma ba hali. Ta juya a hankali tana tafiya.
“Miss Salihu” dama a kufule ta ke ta juyo da sauri ta ce ” Sir yanzu kuma mi na yi”

“Take this stupid thing out of my sight”

Ta kalli zoɓon ta kalle shi tace “idan ka ga dama ka wanke bahayarka da shi”

“Wait what?” Ai da sauri ta fice daga office ɗin…

Sana’ar zoɓo da kunun aya kam Farida ba ta fasa ba sai dai ta chanja salo. Duk mai so zai yi booking ne tana zuwa tun kafin ta shiga office za ta bi ta rarraba ta ƙarɓi kuɗinta wani lokaci kuma sai an kusa tashi ta biya ta karɓi kuɗi. Anas na ɗaya daga cikin ma su son zoɓonta kullum sai ya sha gora biyu. Najeeb bai sake ma ta maganar sana’ar da ta ke ba duk da ya san bata dena ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button