SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Yau wani ƙaton kula ta fito da shi daga keke saboda sana’ar zoɓo da ya ƙarɓe ta. Dan ko gora hamsin ta yi sai ya ƙare.
Tana faman ɗauka sauke da kular Najeeb ya zo wucewa, a lokacin ta sauke ta na ƙoƙarin murza hannunta saboda zafi, ya tsaya yana kallonta. Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Yarinyar nan da garaje ta ke ina ita ina wannan ƙaton abu. Ya wuceta ba tareda ta ganshi ba, yana zuwa bakin ƙofa ya ce da security da ke wajen ya je ya ɗauka ma ta kayan…

Yau ɗan wake ta zo da shi dan haka da su ka je Cafeteria ita da Sister Munibat ta wuce wajen su Anas.

“Yayana ban san ko kanacin ɗanwake ba?”

Anas ya ce ” ci kai. Ai duk lokacin da mu ka je gidan Hajiya Mama sai ta sa an yi min”

“To barin zubo ma ka”
Ta je ta zubo ma sa a plate harda dafaffiyar ƙwai akai da ɗan ganyen lettuce da albasa sai ƙamshi ya ke yi.

“Gaskiya na gode sweet sister. Allah ya miki albarka”

Ta yi murmushi ta tafi. Ko kallon inda Najeeb ya ke ba ta yi ba.
Anas ya fara haɗa ɗanwake da shinkafa yana ci yana santi.

“Are you flirting with her?”

Anas ya ɗago da mamaki ya kalli Najeeb.

“Wannan shine dalilin da ya sa yarinyar nan ta ke abinda ta ga dama a office. Because of you”

“Dude are you….are you jealous?”

” im serious Anas stop flirting with her”

Tashi yai ya bar wajen ya bar Anas da baki buɗe.

Idan dai idon sa ya ga dai-dai to tabbas kishi ya gani a idon Najeeb. But why?…. ko dai…..
Ya juya ya kalli Farida da ke ta zuba uwa surutu cikin zuciyar sa ya ce ” indai abinda na ke tunani ne to, Farida kin ciri tuta. I wish ke za ki maye gurbin Sabreen a zuciyarsa”…

…………………

Tana ɗaki tana cin abinci taji alert na kuɗi ya shigo ma ta daga wajen aiki. Sai dai tashi ta yi cikin sauri saboda abinda ta gani. Ba abinda aka ce za’a biyata ba kenan, kusan kaso sittin kawai aka biyata cikin albashinta.
Cikin tashin hankali ta fara kiran numbar Najeeb sai dai bai ɗauka ba.

Ta kira numbar Anas shima bai ɗauka ba.
“Lallai ma! Kan Uba. Wallahi ba zai yiwuba na yi uwa ayyukan nan ba dare ba rana ace wannan kuɗin za’a turomin. Ta tashi ta fara shiryawa.

Maijiddah da ta shigo ɗaki ta ce ” Anty ina zuwa haka”

“Wajen aiki zan je. Yau Sir Najeeb ya taɓo ni”

“Anty ba yanzu ki ka dawo ba”

“Ke dai bari zamu yi maganar idan na dawo”

A hanya Anas ya kirata akan ta yi haƙuri ɗazu suna meeting ne shiyasa bai ɗau kiran ba.

“Yayana kuna tareda Sir Najeeb ne?”

“Eh tare mu ka yi meeting ɗin amma ni na fito na barshi a office yana ƙarasa wasu ayyuka. Lafiya dai ko?”

“Ba lafiya ba Ya Anas 60% na albashina kawai na gani”

“60% kuma?”

“Eh. Na san Sir Najeeb ne yamin haka, dan haka yau ni da shi, sai ya bani cikaton kuɗina ko yaga bala’i” ta kashe wayar tana huci.

Kamfanin yai tsit saboda an riga an tashi. ID card ta nuna aka bari ta shiga duk da kuwa ma su gadin sun santa. Ba ta wuce ko’ina ba sai office ɗin Sir Najeeb. Ba ya main office ɗin sa dan haka ta je wani ɗaki da ya ke yin ayyukan sa na zane acikin office ɗin. Ta ƙwanƙwasa ƙofar.
Yana tsaka da zane ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Who could it be? Dan ya san Anas ya tafi tuntuni.

Na’urar computer da ke gabansa ya danna nan da nan Farida ta bayyana. Yadda ya ganta ya san maganar albashi ne ya kawota. Wajen da ya ke waje ne da bayan shi sai Anas babu wanda ya ke da access na shiga, work place na shi kenan. Anan ya ke duk wani zane-zanen sa. Wajen zagaye ya ke da glass. Glass ɗin daga ciki za ka ga mutum amma daga waje mutum ba zai ga na ciki ba. Kana shigowa ɗakin idan ba ka da katin buɗe ƙofar glass ɗin to ba tayadda zai buɗu…

Tana tsaye ya buɗe ƙofar ya fito.
“Sir Najeeb ban gane manufarka ba. Me na yi aka cire 40% na albashina?”

Yadda ta ke maganar kamar za ta doke shi.

Bai kulata ba ya je ya zauna a kujerar sa.

“Sir Najeeb i demand an explanation”

“Ofcourse Miss Salihu. Ni na cire 40% na albashinki as a compensation for all your irrational behaviours in this company”

“Sir Najeeb idan ma yaren China ka ke gara ka dena dan ni banjin wannan yare. Ka tura min cikaton kuɗina kawai, abinda na sani kenan”

Murmushin yaƙe yai sannan ya ce ” next month ma ki dinga take dokokin kamfani and i’ll keep on cutting your salary”

“Cabɗi! Wallahi ba ka isa ba”

Tasowa yai ya nufi kanta ta fara ja da baya.
“Mi za ki yi idan na cire? Yau ma hugging ɗina za ki yi? Go ahead and i’ll make sure you get what you are looking for”

Ganin ta kai jikin bango ya sa ta haɗiyi miyau.

“Come on hug me. Na san abinda ki ke so kenan, well yau ba Anas ba yayanki, nobody is here just me and you”

“Idan ma giyan wake ka sha. Wallahi na fika hauka. Kkkka matsa min”

Kallonta ya ke yi yadda take fitar da numfashi da sauri-sauri har yanajin bugun kirjinta.

“Scary bitch…”

Buɗe ƙofar da akayi ya sa yai saurin juyawa to his dismay sai ga Joseph biye dashi kuma wasu zaratan maza guda uku.

“What the hell are you doing here Joseph?”

Bindiga su ka fito da shi Farida ta ƙwalla ƙara ta ɓoye a bayan Najeeb jikinta na rawa tana salati.

“If you comply, nobody gets hurt” a cewar Joseph

Najeeb ya ce “Let the girl go”

“Shut up” ɗaya daga cikin guys ɗin ya daka ma sa tsawa

“Tie them both”

Farida na jin haka ta ƙwalla ƙara ta ƙara ƙanƙame Najeeb….

……………………..

A yadda ya tsara sai ƙarshen wata idan Aneesa ta zo Lagos zai ma ta bayanin komai sai dai ko a ina Aneesar ta ji labari?.

Yana zaune a office su na waya da gimbiyarsa, Aneesa ta shigo fuuuu.

“You liar, sai yaushe ka ke son sanar da ni? Bayan an ɗaura aure?. You evil son of a bitch”

“Anny minene haka kuma”

“Munafuki, asirinka ya tonu ai. Wato har sadaki ka kai. To barin gaya maka Abdul wannan auren ba zai taɓa yiwuwaba”

“Aneesa kenan. Dama abinda ya taso da ke daga Abujan kenan. To ki sani aure babu fasawa tunda dama na gaya miki ai”

“Abdul Wallahi ba zai yiwuba. Idan ma wasa ka ke gara ka janye, i will never share you with anyone”

“Ina son ki Aneesa amma duk abinda ya faru ke ki ka jawo. Ba ni da ra’ayin mata biyu sai da ki ka zaɓi aikin ki fiye da ni”

“Wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita dan ba zan zauna da kishiya ba”

“Its too late Aneesa. Wata biyar da su ka wuce da na gaya miki saƙon Hajiyata what did you say?”

“Haka za ka ce ko. To mu zuba mu gani and i’m taking my kids with me”

“Tunda daga gidan ku ki ka zo da su ba”

Ficewa ta yi daga office ɗin kamar wata zararriya…

……………………….

Har ƙarfe tara na dare ba Farida ba dalilinta ga numbarta ba ya shiga. Maijiddah ta je ɗakin su Yakubu lokacin shima ya dawo daga hira kenan zai ci abinci.

“Amarya Amarya, ya akayi?”

“Yaya Yakubu Anty Farida ta kira ka ne?”

” Farida kuma. Ai ni tun da mu ka dawo daga wajen aiki rabona da ita”

“Yaya numbarta ba ya shiga kuma ta ce za ta je Kamfani wajen Oganta”

“Sir Najeeb”

“Eh”

“To barin kira Anas na ji”
Sai da ya sake gwada numbar Farida still baya shiga kafin ya kira Anas.
Anas ya sanar ma sa yadda su ka yi da Farida sannan ya ƙara da cewa shima ya yi ta gwada numbar Najeeb amma ba ta shiga.

Yakubu ya ajiye waya ya kalli Maijiddah ya ce ” barin je Kamfani in dubata. Ko tana chan dan numbar Sir Najeeb ma ba ta shiga”…

Anas ne ya riga shi isa Kamfanin, lokacin da Yakubu ya iso a wajen motar Najeeb ya tarar da Anas da wasu securities su na magana.

“An ganta kuwa?” Yakubu ya faɗa a kiɗime

Anas ya girgiza kai ya ce ” Yaks i think they have been kidnapped”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button