SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Are you crazy?”
Larry ya ce” the girl too hot Oga. I feel….”
“Will you shut up. You want to ruin my business abi”
Ce wa ɗayan yai ya maida Farida ɗakin da Najeeb ya ke.
Da ɗingishi ta shigo ɗakin saboda har lokacin kwalbar da ta caketa na ƙafar.
Tunda aka fita da Farida hankalinsa ya tashi yasan ba kasheta za’ayiba amma ba makawa sai sun yi raping ɗinta. Lokacin da ya ji ƙaran da ta yi sandarewa yai a wajen jikinsa ya fara ƙyarma yana ayyana abinda zai yiwa Joseph da crew ɗin sa idan sun fita anan. Ganin yadda aka shigo da ita ya sa yai kan ta da sauri. For the first time tun jiya da aka kawo su ya ma ta magana.
“Miss Salihu are you Ok. Mi su ka miki?”
Shiga jikinsa ta yi tana kuka jikinta na rawa. Ta gama tsorata dan ta sadakar Larry shigarta zai yi. Tausayinta ya mamayeshi dan ya san saboda shi ta shiga wannan haɗarin dan Joseph da shi yake gaba. Cuddling ɗin ta yai so tight yana ba ta haƙuri. ” I’m sorry, i’m very sorry Miss Salihu”
Sun jima a haka shi kan sa ya rasa dalilin da ya sa ya ji wani nitsuwa ya shigeshi farat ɗaya, like kada ya saketa su cigaba da tsayuwa a haka.
Zafin da ta ji a ƙafarta ya sa ta tuno da kwalbar da ta taka. Cikin sheshsheƙar kuka ta ce “Sir Najeeb ƙafa na” sai alokacin ya saketa ya fara duba ƙafan wanda ke ta zubar da jini.
Zaunar da ita yai sannan ya ɗaura ƙafar a cinyarsa ya ce ” zan cire mi ki kwalbar, sorry it will hurt”
Girgiza kai ta yi tareda rufe idonta, ta cize leɓe. A hankali ya cire kwalbar tareda ɗaure ƙafarta da farin hankerchief sannan ya sake jawo ɗankwalinta wanda ya faɗi lokacin da Larry ya fita da ita. Ya yaga ya sake ɗaure ƙafar sosai.
“Are you Ok?” Ya tambaya yana kallonta.
Girgiza kai ta yi ta ce nagode.
Bayan minti shabiyar aka kawo mu su abinci, ko kallon wajen Farida ba ta yi ba duk da kuwa yunwar na cinta.
“Ki tashi ki ci abinci” ya faɗi lokacin da ya ga ta share abincin.
“Ba zan ci ba. Wataƙila ma sun sa magani”
Zuwa yai ya ɗau take away ɗaya da ruwa ya kawo gabanta. ” ba abinda za su sa aciki, because they need us alive. Besides na san yunwa ki ke ji”
Ta kalleshi ta kalli abincin ta ce ” to kai ma ka ci, tunjiya ba abinda ka ci”
“Na saba da rashin cin abinci”
“Ana sabo da yunwa ne?” Bai amsa ma ta ba sai sokalin abinci da ya kawo dai-dai bakinta ya ɗaga ma ta kai alamar ta ci. Ba tai musu ba ta fara ci. Haka ya dinga bata abincin a baki har ta cinye.
“Kin ƙoshi?”
Ta gyaɗa ma sa kai…
Da dare zazzaɓi ya rufeta, tsoratar da tayi da kuma ciwon da taji su suka haɗu su ka sa mata ciwon kai da zazzaɓi. Tana kwance ta fara rawan sanyi harda kakkarwa. Daga inda ya jingina ya jiwo nishinta.
“Miss Salihu are you OK?”
Jin shiru ya sa ya taso ya je wajenta. Jikinta yai zafi sosai ga ba ruwa balle ya dinga shafa ma ta.
A hankali ya ɓalle buttons ɗin shirt ɗin sa ya mannata da ƙirjin sa. Thats the only option he can think of…
Ta jima a haka kafin zazzaɓin ya saketa amma bai janyeta daga jikinsa ba har bacci ya tafi da ita. Shi kam ya manta yaushe rabon da yai bacci without his pills.
Farkawan da za ta yi ta jita ajikinsa. For the first time tun haɗuwarsu sai ta ji kunyar sa. Da ƙyar ta iya tashi, nan ma sai da ya tallafa ma ta saboda ƙafarta da ya kumbura yana ma ta zogi.
Suna buƙatar ruwa dan haka ya je ya fara bubbuga ƙofa.
“What do you want?” Aka faɗa da kakkausar murya.
“Water”
“Una no go get any water for here ooo”
” please, give Us some water” Najeeb ya rintse ido saboda tuno matsayinsa ada da kuma matsayinsa a yanzu wai shi ke roƙon ruwa.
Da ƙyar wanda ke gadin ƙofar ya kawo mu su ruwa biyu, nan ma sai da ya cire belt ɗin Najeeb wai itama designer ce idan ya sayar zai samu kuɗi…
Ƙarfe shabiyu na rana Emeka da Joseph su ka zo mu su da albishirin yau za a sake su idan har an biya cikakken kuɗin da aka buƙata.
A fili Farida ta ce ” miliyan hamsin ɗin. Kai amma karayar arziƙi ta sameka Sir Najeeb”
Dariya ta bashi saboda bata san networth na shi a shekara ba. Ko za a cire miliyan hamsin sau goma ba zai girgiza ba. Balle ya san idan har da gaske za a biya waɗannan kuɗaɗe to Dad ɗin sa ne zai biya, ba sai ya nemi taɓa masa kuɗi ba.
“Kenan za ka kori ma’aikata dayawa idan ka koma. Dan Allah kar ka kori ɗan uwana. Yakubu shi kaɗai yai degree a gidan Baffa Musa, kaga yayansa Faruƙu mai ƙaton hancin nan, ko sakandari bai gama ba, kasuwanci ya jona kaman na ubansa. Dan Allah ka min alƙawari ba za ka koreshi ba”
Murmushi kawai Najeeb ya yi.
“Sir Najeeb ka ga yadda ka yi kyau kuwa da ka yi murmushin nan. Dan Allah idan an koma office ka dena haɗa ran nan, ba ka kyau”
Juyar da kai yai yana kallon gefe duk da kuwa hankalinsa na ga surutun da Farida ke yi…
……………………
Har za a tashi Dad ya ce ayi addu’a.
Aka ɗaga hannu aka yi addu’a sannan aka shafa.
Anas ya ce Dad ” Insha Allah ko mi zai tafi according to plan”
“Allah ya sa Anas”
Anas ya kalli sauran officers ɗin ya ce “gentlemen, let’s go”…
Emeka yana zaune da Joseph su na jiran Larry da ya tafi ɗauko kuɗi. Tun ɗazu aka ce an ajiye kuɗi a inda su ka buƙata.
Sun gargaɗi Larry akan ya tabbatar ba wanda ke binsa lokacin da ya ɗau kuɗin, shi ya sa ma su ka ce yana tabbatar da kuɗin na cikin jakar to ya sa jakar a ƙatuwar jakar Ghana-must-go da su ka bashi.
Minti biyu sai ga kiran Larry. Emeka ya sa ihu lokacin da Larry ya ce ya ɗauka kuɗin. Ya kalli Joseph ya ce “Bros we are rich”
Plan ɗin da su ka shirya shine, dama suna da mota, a daren za su bar Kano shi kuma Joseph saboda Najeeb ya ganeshi suna barin Kano daga Kaduna zai wuce ƙasar Ghana. Anan zai zauna har komai ya lafa kafin ya dawo.
Suna cikin tattauna plan ɗin su Larry ya shigo da jakar kuɗi.
Da sauri Emeka ya buɗe jakar ya ce su duba kuɗi sannan su duba ko akwai tracker aciki dan a matsayinsa na wanda ya kwana biyu yana aikin yasan ana iya samun wannan idan aka aiko da kuɗin ransom. Ganin babu tracker ya sa su ka fara jera kuɗin a wata jakar daban.
Abinda ba su sani ba shine sai da aka buɗe jakar aka sa ƙaramar tracker chip aciki sannan aka ɗinke kamar ba a sa komai ba.
Su Emeka na duba kuɗi sauran na shan giya suna ihu su ka ji kamar ana buɗe ɗaya daga cikin ƙofofin gidan.
Emeka ya ce su je su duba ko su Najeeb ne ke son guduwa.
“Larry, you sure say nobody follow you”
Larry ya gyaɗa ma sa kai.
Fitar sauran ke da wuya su ka ji ƙaran bindiga…
“Shi kenan, Sir Najeeb kashe mu za su yi. Ga shi sun fara harbin junan su” Farida ta faɗi kamar za ta yi kuka ta kuma matsowa kusa da Najeeb ɗin.
Shi Najeeb ya gane abinda ke faruwa dan ƙaran bindigan ba iri ɗaya bane.
Jin ana shirin buɗe ƙofa. Najeeb ya kalli Farida ya sa yatsunsa biyu a baki alaman ta yi shiru…
Joseph ne ya buɗe ƙofar ɗauke da bindiga,yana shigowa bai gansu ba zai juya kenan aka kwaɗe kan sa daga baya, sai bindigar ta faɗi, yai taga-taga zai faɗi shima Najeeb ya kuma jawoshi ya gwara shi da gini. Ƙiɓar Joseph ya ke kamar wanda aka aiko shi.
Wani police ne da Anas su ka shigo ɗakin lokacin da Farida ta ga Anas ta ce “Alhamdulillah ashe ku ne”
Najeeb kam yana kan Joseph yana ƙiɓar sa sai da Anas da police su ka zo su ka ɗaga shi, dan tuni Joseph ya suma jini na fita ta hanci da baki…
Da ɗingishi ta ke takawa lokacin da su ka fito, komai ya lafa, Anas ya ce mu su an kashe ɗaya daga ciki sauran kuma duk an kamasu. Emeka da yake ogansu ma an halbeshi a cinya.