SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Ke matsa chan jahila mai kama da….”
Farida ba ta bari ta ƙarisa ba ta amsa da cewa ” ke ce jahilar ai. Kwartuwa mai bin gindin maza, Allah ya wadai da halin ki. Tir da ke Aneesa mai ƙaton baki. Hooooo ashewo….Hoooo ashewo” (ashewo- karuwa)
Aneesa ta yi saurin kashe wayar saboda zuciyarta da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Wannan wace irin yarinya ce haka, lallai kuwa Maijiddah za ta ci ubanta idan ta shigo ma ta gida. Sai da ta gama banbamin bala’i sannan ta dubi screen ɗin wayarta ta sa hannu ta shafa lips ɗin ta.
“Ko wa yace ma ta ina da babban baki? Ba dai AbdulWahab ba”…
Farida na jin an kashe wayar ta sa dariya ta ce ” ƙaramar ‘yar iska, da ki tsaya ma na”
Ta kalli Maijiddah da ta yi zuru-zuru da ido
“Ke kuma ki cigaba da yin shiru-shiru har wannan matar ta sa mi ki ciwon zuciya. Gara ki ɗaure ɗamara dan wannan matar da alama ‘yar tasha ce”
“Sannu Malama Farida, expert a ɓangaren rashin mutunci”
“Kai Yakubu ba na son iskanci fa”
“Ki fito Anas na jiran ki a waje”
Gyale kawai ta yafa ta fita bayan ta gayawa Ummi. Gaishe shi ta yi lokacin da ta shiga motar na shi.
” ‘yar uwa ya jiki”
“Da sauƙi yaya na”
” ashe ba ƙaramin jin jiki ku ka yi ba. ‘Yar uwa ya abin ya faru ne? Najeeb ya ƙi ya bani labari”
Dama abinda ta ke jira kenan ta fara karanto ma sa yadda abin ya faru. Labarin da tun safe ta ke faɗawa ‘yan gidan su da maƙota da ke zuwa gaisuwa.
Abu ɗaya ta ƙi faɗa wanda ita kanta duk yawar maganarta ta rasa dalilin ƙin faɗar da ta yi. Ta ƙi faɗin cewa Joseph ya tofa wa Najeeb miyau.
Sai da ta gama ba da labarin Anas ya ba ta wani envelope ya ce “wannan daga Najeeb constructions ne. Kuɗin magani”
ya miƙa ma ta wani envelop ɗin ya ce ” wannan kuma Dad ne ya baki, kuma ya ce na gaishe ki da jiki”
“Kai na gode sosai, ka miƙa godiyata wajen Daddy dan Allah. Najeeb constructions kuma sai mun zo mu ku sallama”
“A’a, ‘yar uwa sallama kuma. Ba dai aikin za ki bari ba”
“Eh yayana, zan ajiye aiki da ku”
“Gaskiya ban yarda ba. Ai hutu kawai za ki yi na sati zuwa kwana goma ki dawo bakin aikin ki”
“Ya Anas Ummi na ba ta so, ta ce na ajiye aikin”
“No Farida, Najeeb needs you. Ki ba wa Ummi haƙuri ta barki ki dawo dan Allah”
” to bari mu ga ni dai. Na gode Yaya”
Sai da za ta fita daga motar ta ce ” Ya Anas ya jikin Sir Najeeb?”
” da sauƙi ƙanwata” ya faɗi yana murmushi…
Ita ɗin ma da ta shiga gida sai ta ji kamar ba za ta iya haƙura da aikin ba. Musamman idan ta tuna bikinta da Rayyan zai iya kaiwa wata shida ma su zuwa…
Washe gari su ka wuce Jos ita da Ummi bayan ta yi welcome back ɗin layinta.
…………………
Yana zaune a kujerar sa yana duba wasu files amma hankalin sa na kan wayar sa, jira ya ke ya ga ko an turo ma sa saƙo. Sai yanzu yai da na sanin ƙin bin Anas da yai ranan. Ko ba komai da ya ganta ya tabbatar lafiyar ta ƙalau.
Duk da ya san ba ta da numbar da ya tura saƙon. Ya ja dogon tsaki ganin har awa ɗaya kenan da tura saƙon na shi amma ba amsa, saboda ka da ta gano shi ma ya sa ya ke rubuta saƙonnin da Hausa. Da ya gama duba files da takardun da ke gaban sa ya tashi ya fita a office ɗin. Ganin kujerarta wayam ba kowa ya sa shi jin wani abu a zuciyar sa, ba dai da gaske barin aiki za ta yi ba. Kai tsaye office ɗin Anas ya wuce wanda ba nisa da na shi office ɗin.
Waya ya samu Anas na yi lokacin da ya shigo, ya samu waje ya zauna yana kallon sa.
“Miss Salihu ta bar aiki ne?” Ya faɗa da harshen ko in kula lokacin da Anas ya gama wayar.
“Ka fara kewar ta ne?” Anas ya amsa ma sa
“Oh please, ka amsa min tambayata ba na son shirme”
Dariya Anas yai sannan ya ce ” well, ta ce za ta dawo amma sai Monday”
“Monday is too far”
“Mutumina da alama ka ƙagu ka ganta ko?”
Tashi Najeeb yai ya ce ” idan ba ta dawo Monday ɗin ba, ka nemo min wata sakatariyar”
Anas ya ɗan yi dariya ya ce ” kamar da gaske”……
………..
Ghana-must-go manya guda biyu ne a gabanta tana faman jera kayan gwanjo da ta saro da za ta kai Kano.
Adiyya wata jikar Nanna ta miƙo ma ta waya wai ana ta kiranta tun ɗazu.
Amsa wayar ta yi ta ranƙwashi kan yarinyar wadda ba za ta wuce shekara takwas zuwa tara ba. “Na hana ki ɗaukan wayata ba kya ji ko. Yanzu jiba yadda kuka cinye min chaji”
“Allah Anty ba ni kaɗai bane har da Mubashshir, shi ne ya ke game, ni kallon hotuna kawai na ke yi” yarinyar ta faɗa tana shafa wajen da Farida ta ranƙwasa.
Duba wayar ta yi ta ga missed call ɗin Maijiddah ne da na sister Munibat sai saƙo guda ɗaya wanda wani number ya turo. Numbar na yawan damunta da saƙo tun lokacin da ta yi welcome back ɗin layinta. Ta buɗe saƙon ta karanta kamar haka.
fatan ki na lafiya Aysherh? Ina so ki yadda da ƙaddarar da ta same ki, ki ɗauke shi a matsayin jarrabawar Ubangiji. Zai fi ki koma al’amuran rayuwar ki kamar da, ba tareda wani tsoro ba. N J
Tsaki ta yi ta ce ” shi wannan N J ɗin sai shegen naci, ka kira ba za ka kira ba, sai gatan tura saƙo kamar kamfanin Airtel.”
Ta tura masa reply kamar haka ” Malam NJ ko Mr NJ, koma wa ka ke dai, ina ma ka gargaɗi da ka dena turomin saƙo, saboda ni matar aure ce. Idan ka cigaba kuwa duk inda ka ke, mijina zai nemoka kuma ba za ku wanye lafiya ba”
Sai da ta tura saƙon ta ke ƙara alhinin wannan NJ ɗin wanda take tunanin ƙila cikin abokan Yakubu ne da su ke aiki tare a Najeeb constructions. Idan ba haka ba ta ya NJ zai san an kidnapping ɗin ta har ma ya san ta ji ciwo a ƙafa. Ƙafarta ya fara tambaya ranan da ya fara turo saƙonsa wanda kuma ta san idan ba Yakubu da Anas ba ba wanda ya san ta ji ciwo a wajen aikin su. Ta kawar da tunanin ta hanyar kiran Maijiddah dan ta ji mi ye labari…
Yana zaune ya ji ƙarar shigowar saƙo. Ya ɗauki waya ya duba, sai da ya karanta sannan yai murmushi dan ya san yanzu kam ta samu lafiya tunda har ta iya ma sa reply.
…………………….
Yau sammako yai a office dan ko mai shara ba ta yi aikinta ba lokacin da ya shigo. Fakewa yai da cewa wasu ayyuka zai ƙarasa a office ɗin lokacin da Najdah ta tambayi dalilin fitarsa da wurwuri haka. Duk da kuwa dama shi ɗin mai fitar wuri ne amma na yau daban ne…
Har ƙarfe takwas da rabi ba ita ba alamarta. Haka dai ya ke aikin na shi ba tareda samun kwanciyar hankali ba…
Tun takwas saura ta zo, ta fara biyawa tana tallen gwanjon da ta saro a office-office da ke hawa na farko da na biyu. Sannan ga uwa uba labarin kidnapping ɗin su da ta ke bayarwa ga duk wanda ya ma ta jaje. Ba ta ankara ba tana office ɗin sister Munibat ta ga ƙarfe tara har da kwata.
“Kai ashe haka lokacin ya tafi barin je na kama aiki kafin Sir Najeeb yai ƙuli-ƙulin Kubra da ni”…
“Najeeb na samo ma ka wani secretary, he’s a good guy idan ka amince zai fara aiki gobe”
Ya kalli Khalidah kallon ki na da hankali kuwa.
“Ban sa ki wannan aikin ba. Idan ina buƙatar secretary na san inda zan nema”
“Najeeb, sati ɗaya kenan wancar shashashar ba ta zuwa. Na san abinda ya faru ne ya sa ta ƙi dawowa, ni wallahi da da su….”
“Out”
“Najeeb..”
” i said get out”
Khalidah ta kai maƙura wajen ɓacin rai amma ba yadda ta iya dole ta kwantar da kai idan tana son samun Najeeb.
“Shi kenan zan fita amma ka yi tunani”
Tsaki ya ja sannan ya cigaba da aikin da ya ke akan system ɗin sa.
Shigowar Farida kenan Khalidah ta fito daga office ɗin Najeeb.
“Ina kwana Anty” Farida ta faɗa dan abinda ta ke kiran Khalidar da shi kenan idan tana son tunzurata. Khalidah irin matan nan ne da Allah yai wa baiwar jiki da tsayi.