SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ta amsa wayar ta kunna recording ɗin ta fara ji.
Muryar mace ce ke magana tana faɗin
“kinga Oga Najeeb ɗin nan, babban ɗan luwaɗi ne. Kin san a ƙasar waje ya taso, so ya jima da zama gay, shi ya sa ma ya ƙi aure har yanzu. Ance fa ya kusa kaiwa 40yrs amma ba aure. Hmmm wani abin al’ajabi da na gano shi ne…. Amma kar ki faɗawa kowa fa, Halima. Oga Najeeb da Anas su na neman junan su, a yadda na jiyo ma, wai sun yi aure a sirrance. A office su ke haɗuwa su ci amarcin su. Ni Farida da ki ke ganin nan na taɓa kallon su sunayi da ido na. Bakiga yadda Anas ke zama boyi-boyi ba a gaban Najeeb , ai saboda shi ne matar Najeeb kuma mijin. Shi Anas fa ba wai son shi ya ke ba kawai kuɗinsa ya sa ya amince. Kin san Anas ɗan maigadin gidan su Najeeb ne”
“Innalillahi. Yakubu ba muryata ba ne wannan. Wallahi ba murya ta ba ce”
Farida ta faɗa kaman za ta yi kuka.
“Ki ji ƙarya. Lokacin da ki ke hiran da Halima Baballe duk ta yi recording komai dan ma kar ace ƙarya ta mi ki. Kuma kin ji da kunnen ki”
Farida ba ta ce komai ba ta fita daga office ɗin da sauri.
………
Lokacin da Anas ya shiga office ɗin Najeeb kuwa samun shi yai tsaye jikin window.
“Abokina ka yi haƙuri dan Allah, ban taɓa sanin Farida za ta iya faɗin maganganu haka ba. I’m so dissappointed in her. Kar ka damu, dana koma office ɗina zan typing takardar korarta”
“No need” Najeeb ya faɗi a hankali
“Ban gane ba? Kana nufin ba za a koreta ba kenan?”
Najeeb ya juyo ya kalleshi ya ce ” ba muryarta ba ne. Its a trick”
“How?”
” ba muryarta ba ne, ba kuma yadda ta ke magana ba kenan.”
Anas yai shiru saboda kansa ya ɗaure. Najeeb ya sake playing ma sa recording ɗin wanda Khalidah ta tura ma sa da sassafiyar yau tun ma kafin ya zo office.
Sai da ya gama ji Najeeb ya ce “barin ba ka satar amsa. Miss Salihu ba ta kirana da Oga Najeeb“
“Shit. Kuma fa haka ne” Anas ya faɗi ya na buga goshin sa da taffin hannun sa.
“Kafin Miss Salihu ta fara aiki anan, i know her voice”
“Wallahi na tafka shirme Najeeb. Barin je na bata haƙuri”
…………..
Farida na isa office ɗin su Halima ta samu tana tsaye da wasu tana mu su bayani kan recording ɗin da su ka ji. Farida na zuwa ta yaficota ta wanke ta da mari, kafin ta ankara ta ƙara ma ta na biyu. Kafin ka ce me sun kaure da kokawa…
Ruwan cikin Halima Farida ta zauna tana kirɓanta. Halima na ihu. Da ƙyar mazan da ke wajen su ka janye Farida da ga kan Haliman.
“Ku sake ni na ci uban shegiya annamimiya. Ku sake ni na watsar ma ta da haƙora shegiya Munafuka”
Halima ta samu ta tashi tana rufe hancinta wanda ke fidda jini jikinta na rawa.
Kici-kici ta ke tana ƙoƙarin ƙwacewa. Ana ba ta haƙuri amma ina sai masifa ta ke.
“Ku bar ni na nuna ma ta banbancin da ke tsakanin mu”
Tana ƙwacewa ta yi kan Halima da gudu. Ta ɗaga hannu za ta kai ma ta duka aka riƙe hannun. Ta fara ƙoƙarin yakice hannunta amma ta kasa saboda riƙon da aka ma ta. Ta yi ta yi still ta ka sa dan haka ta juyo
“Ka sake ni na dak……” ta tsaya lokacin da ta ga Sir Najeeb ne riƙe da hannunta. Sake hannun yai ya ce ” Miss Salihu to my office”
Ta juyo ta kalli Halima ta ce ” wallahi ba ta tsaya anan ba. Sai na je har gida na ci ubanki, shegiya dama halin munafurcin da ya hanaki zaman gidan miji kenan”
Yakubu ya ɗauko ma ta gyelen ta da ke yashe a ƙasa ya miƙa ma ta. Wafcewa ta yi da ƙarfi tace ” kai kuma zamu haɗu a gida”
Wucewa ta yi ta bar wajen tana cigaba da zage-zage….
Kai tsaye office ɗin Sir Najeeb ta wuce ranta cike da masifa. Ta san ba makawa takardar kora zai ba ta sai dai wannan karan za ta karɓa za ta bar Najeeb constructions amma sai ta wanke sunan ta.
Kaman ba abinda ya faru haka ta ganshi yana zaune yana duba wa su takardu.
“Sir Najeeb, na san ka ji abinda aka ce na faɗa amma ka sani ba muryata ba ce wallahi, ba ni ba ne”
Ɗagowa yai ya kalleta ya ce ” Miss Salihu, let it be the last time da za ki maida Kamfanina wajen faɗa”
“Sir Najeeb, wallahi a liƙa min sharri kam ba zan zauna haka ba. Kowaye sai na ci kutumar uban sa, hakan ma sai hukuma ta shiga tsakani. Haka kawai dan an sanni da yawar surutu sai a kwaikwayi muryata a faɗi abin da ban faɗa ba”
Kafe ta da ido yai yana gani tana banbami kaman za ta ci babu.
Miƙa ma ta file yai ya ce ” take this file to Anas, kuma ki sanar da Admin na HR inada zama da su anjima”
Mamaki ya kamata. Ta haɗiye miyau ta ce ” ba korata za ka yi ba?”
“Ki na so na kore ki ne?”
Ta yi saurin girgiza kai ta ce ” ba ka ji recording ɗin nan ba ne”
” muryan ki ne?”
” wallahi ba ni bane” ta faɗa da sauri
“Good. Then get back to work”
Ta ɗau file ɗin ta ce ” wani lokaci idan ka yi abu kaman Salihin mutum, Sir Najeeb”
“Miss Salihu!”
Ai da sauri ta bar gaban shi tana dariya.
………..
Zuwa ta yi ta ajiye file ɗin a table ɗin Anas ta juya za ta tafi saboda ba ta son ko haɗa ido da shi.
“Aisha dan Allah ki tsaya”
Ai dama jira ta ke yai magana ta fara masifa ” Ya Anas dama zumuncin kenan, idan na yi laifi a tureni gefe kamar wata kayan wanki balle ma banyi laifi ba. Iya zama na da ku yau wata ɗaya da sati uku amma har ka ji a zuciyarka zan iya maka ƙazafi, ai ba zama mai kyau ake ba kenan…”
“Dan Allah ƙanwata ki yi haƙuri. I was blind by anger, maganganun sun girgizani sosai to the extend na ka sa ma tsayawa na lura cewa ba muryan ki bane. Im really sorry ƙanwata”
“Ba wani, kai dai tabarmar kunya kawai ka ke son naɗewa da hauka. Ni ka ma barni na faɗi abinda ke raina dan abinda zai sa na huce kenan”
“To faɗa ina jin ki”
Yadda yai maganar sai ta ɗan ji kunyar sa.
“Shikenan Ya Anas na haƙura amma tsakani da Allah na ji haushin abinda ka yi min”
“Dan Allah ki yi haƙuri my ƙanwa”…
Farida na komawa office ɗin ta ta ji saƙo ya shigo wayarta tana buɗewa ta ga numbar NJ, ta yi tsaki sannan ta buɗe saƙon
bai kamata ki watsar da kan ki ta hanyar yin dambe da wacce ba ta kai ki daraja ba Aysherh, kin fi ƙarfin haka. Ko kin manta ke matar aure ce ….. N J
“Mtsww, wannan NJ ɗin ma wallahi sai na binciko shi a wannan kamfani, mutum sai shegen na ci, kai ba za ka kira ba idan kuma an kira ba zai shiga ba” … ta ajiye wayar ta cigaba da aikin da ta ke.
…………..
Turo ƙofar aka yi da ƙarfi. Najeeb ya ɗago ido da sauri don ganin wannan mai karambanin. Farida ma da ke jera wasu files a shelf ɗin Najeeb ta juyo da sauri.
“Najeeb wanni walaƙancin ne wannan? Ga wacce ta ma ka sharri amma ba ka ɗau mataki a kanta ba sai Halima. Ka manta Wannan Jakar har dukan Halima ta yi. You’re supposed to sack her”
” ina ganin ba ki shiga office ɗin ki ba har yanzu. Go back to your office akwai saƙo da na sa aka ajiye mi ki”
“Najeeb i’m serious bai kamata ka kori Halima ba she didnt deserve it”
Ko kallonta bai yi ba ya ce ” ki je office ɗin ki ki duba saƙona”
Ta juya a fusace ta bar office ɗin.
Farida ta fara dariya dan ta san saƙon, tunda ita ya ce ta typing suspension later ɗin Khalidan.
Ganin dariyan na ta ya ƙi ƙarewa ya sa ya daka ma ta tsawa.
“Miss Salihu!”
“Sorry Sir” ta faɗi tana ƙoƙarin gimtse dariyan…
Ta gama abinda ta ke amma ta fake dan tana son ganin reaction ɗin Khalidah idan ta dawo.
Ai kuwa sai ga Khalidan ta zo a rikice.
Ta cilla wa Najeeb takardar hannunta tana faɗin ” Najeeb explain this”
” ba ki iya karatu ba ne ko me?”
“Najeeb one month suspension a kan me?”