SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Shiru yai bai kulata ba.

“Najeeb a wani dalilin za ka min haka”

Still Najeeb bai yi magana

“Najeeb magana fa na ke. I’m calling my Dad right now”

Tana ƙoƙarin kiran mahaifin na ta ta ji Najeeb yana magana.

“Alhaji Tukur na bawa ‘yar ka Khalidah Siraj Tukur suspension na wata ɗaya, ko kana da ja akai?”

Saboda wayar a handsfree ta ke sai kawai Khalidah ta ji Babanta yana cewa “ba ni da ja My Engineer. Komai ka yi dai-dai ne”
Najeeb ya sa hannu ya katse kiran ko ɗagowa bai yi ba balle ya ga yadda Khalidah ta taƙune fiska.

“Shikechar inji wani almajirin mu. Asha hutun wata ɗaya lafiya ko, dama ance idan za ka gina ramin mugunta ka gina dai-dai kai” ta ƙarasa maganar tana dariya

Khalidah ta zo gaban Farida ta nunata da yatsa ta ce ” sai na ga ƙarshen ki Farida, you’ll see”

“Allah raka taki gona Anty Big”

Tsaki Khalidah ta ja sannan ta fice a office ɗin.

Tana cikin dariya Najeeb ya daka ma ta tsawa.

“Get out”
Simi-simi ta fita a office ɗin sa.

…………..

An kawo lefen Maijiddah kuma ba ƙarya AbdulWahab ya kashe kuɗi wajen haɗa kayan nan. A wajen ƙarɓan kaya ma Farida ta ka sa ta tsare dan ganin komai ya tafi dai-dai.

Anty Hanne ƙiri-ƙiri ta nuna kishinta a fili saboda kayan da akaiwa Maijiddah ko rabinsa ba aiwa ‘ya’yanta da aka aurar ba.
Baaba Sabuwa kam farin ciki fal ranta.

Ranan sunday da dare AbdulWahab ya zo yiwa Maijiddah sallama da ke ya zo weekend.
Farida ce ta tsarawa Maijiddan kwalliya ta kuma zaɓa ma ta kayan da za ta sa.

Falon Baffa Musa aka saukeshi. Wannan zuwan sa gidan kenan na biyu tun haɗuwar su.

Tareda Farida su ka zo bayan sun gaisa da shi sannan ta fita ta basu waje.

“Ina yini” ta faɗa a hankali dan ita har yanzu ta kasa sake jiki da shi.

“Lafiya gimbiya ta”…

Hiran na su yawanci shi ya ke maganar dan Maijiddah kam kunya ta hanata sakewa.

Ya ɗan taɓa abinda aka kawo ma sa sannan ya tashi akan zai tafi.

“Allah ya tsare hanya, ya kai ka gida lafiya. Ka gaida su Baby da Alizah”

“Amin tawan. Shikenan gimbiya ba wani ɗan abu da za ki bani”

“Abban Alizah mi ka ke so”

Ɗan matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya yana ɗan murzawa. Ya sa hannu ya saukar da gyalen da ta yane kan ta da shi sannan ya tufke ɗankwalin,
warware gashin da ta tufke yai sannan ya fara shafa gashin wanda ya zubo har tsakiyar bayanta ƙanshin man da ta shafa wanda ke fitar da ƙanshin mint leaf kaman kuma lemon grass. Ya kai hancinsa yana shaƙar ƙanshin.
Hannunta da ke trembling cikin na sa da kuma yadda bugun ƙirjinta ya ƙaro saboda closeness na su ya sa ya saita kan sa yai gyaran murya bayan ya miƙe tsaye sannan ya ce ” Allah ya kaimu kwana ashirin da tara gimbiyata”….

………………..

Yakubu ta sa ya ciro ma ta kuɗi bayan ta ga cikakken alert ɗin ta wannan karan Sir Najeeb bai cire komai ba.
Karfe goma saura kwata ta shiga falon Baffa dan bai jima da dawowa ba, sai da ta ba shi lokaci kafin nan ya ci abinci.
Ɗan gefe da shi ta zauna suna gaisawa.

“Baffana na kai na. Allah ya ja zamaninka ya ƙara ma ka lafiya amin”

“Amin ‘yar Baffa”

Hannu biyu ta sa ta miƙa ma sa kuɗi. “Baffa a sa mana albarka”

” wannan bai yi yawa ba Farida”

“Baffa na so ya fi haka ma sai dai ka san mu mata sai a hankali, kuɗin na wa na sayo gwanjo da su kuma ban gama haɗa kan kuɗin ba”

“Allah ya miki albarka Farida” ta amsa da amin.

“Dubu hamsin yai yawa Farida, ba dai duka albashin na ki ki ka kawo ba?” Baffa ya faɗa lokacin da ya gama irga kuɗin.

“A’a Baffa”

Shiru ne ya biyo baya na minti biyu kafin ta ce ” Baffa dama na ce tunda wannan shekaran ka yi bikin su Salima ga na Jiddah nan da wata ɗaya mi zai hana nawan a barshi wata shekaran kaga kafin nan ka tara wani abu”

” A’a Farida, idan na yi haka na ci amanar mahaifin ki. Duk cikin ‘ya’ya na ba wadda ta wuce shekara ashirin na aurar da ita, Maijiddah ce ma har ta kai ishirin ɗin. Idan ba ƙaddara da ta faɗa miki ba ai da tun shekaru uku da su ka wuce anyi bikin ki”

“Baffa Allah ba matsala ka bari irin watan uku na wata shekara sai ayi kafin nan komai ya dawo normal”

“A’a Farida ko da duka gonakaina zan sayar dan na samu kuɗin yi miki aure zan sayar. Ai idan na bari wata shekara sai duniya ta zageni. Idan ba su iyayen yaron sun ce bai gama shiryawa ba ai da tareda Maijiddan zan haɗaki”

“Baffa dai” ta faɗa kaman za ta yi kuka.

“Tashi ki je ki kwanta. Allah ya kaimu watan December”

“Baffa nikam…”

“Tashi na ce” ya faɗa da ɗan ƙarfi.

Ta tashi tana guna-guni ta bar falon.

Sai da ta fita Baffa ya ƙara godewa Allah domin halin Salihu na kyauta kam Farida ta ɗauko, dan lokacin yana raye bashida rowa ko kaɗan, zai iya bayar da abu shi ya rasa kuma hakan bai dame shi ba…

…………….

Lagos

Ranan Monday da safe ya isa Lagos, kai tsaye office ya wuce kasancewa dama shi ɗaya ya je ya bar su Alizah a gidan maƙocin sa kuma abokin aikin sa Mr AbdulRazaƙ.
Bai ɗauka Aneesa za ta zo ba tunda ya gaya ma ta zai je Kano kuma zai bar yaran a wajen maƙota.
Ƙarfe takwas da rabi na dare ya isa gidan Mr AbdulRazaƙ dan ɗauko yaranshi. Sai dai da ya je ake ce ma sa Aneesa ta zo ta ɗauke su.
A take a wajen ya kira Aneesa amma ba ta ɗauka ba. Hankalinsa bai tashi ba sai da ya je gida mai’ aikin su ta ce Aneesa ta wuce da yaran Abuja. Yai ta kiran numbar Aneesan amma ba a ɗauka. Ƙarshe dole ya kira numbar ƙaninta Nazir ya ce ya kaiwa Aneesa.

Minti biyar sai ga kiran Aneesa a wayarsa.

“Wannan wanni irin iskanci ne Aneesa za ki ɗauke min yara ba tareda kin sanar da ni ba”

“Iskanci kuma AbdulWahab, Ni da ‘ya’ya na. For your information, kai da su Baby sai ka janye maganar auren ka. Ko kuma su zauna tare da ni anan amaryarka ta haifa ma ka wasu”

“Anny kin san yaran nan suna Makaranta fa”

“And so, zan sa su a wani anan”

“Look Aneesa, ki maido min da yarana gobe-goben nan ko kuma…”
Ƙiiit ta kashe kiran.

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Free page

0️⃣1️⃣3️⃣

Kwana biyu Aneesa ba ta turo ma sa yaran ba dan haka dole ya kira Alhaji, mijin Maman Aneesan kenan, ya ma sa bayanin komai shi baya ma gari dan haka bai san su Alizah na gidan sa ba. Ya jima yana yiwa Aneesa faɗa akan ta ajiye aiki ta je ta zauna da yaranta amma ta ƙi. Kasancewa Maman ta ba ta bashi goyon baya ba shi ya sa yai shiru ya zuba mu su ido. Ya auri Hajiya Salma ne lokacin Aneesa na da shekara goma shabiyu ƙaninta kuma na shekara tara. Bai taɓa banbanta su da ‘ya’yan sa na cikin sa ba, makaranta mai tsada su ka yi da ta gama sakandare ya turata karatu ƙasar waje.

Aneesa ta haɗu da AbdulWahab ne a cikin jirgi, daga Lagos za ta wuce Abuja. Sun kusan shekara biyu su na soyayya kafin su ka yi aure saboda dagewa da Aneesan ta yi akan za ta yi masters kafin ta yi aure. Bayan sun yi aure ta fara aiki da wani Kamfani a Lagos. Shekaru biyu da su ka wuce Kamfanin su ka buɗe wani branch a Abuja kuma su ka nemi Aneesa ta koma wajen. Ƙarin matsayi da albashi su suka ruɗi Aneesa ta tsallake mijinta da ‘ya’yanta ta wuce Abuja. Abdulwahab ya yi faɗan ya yi fishin amma duk a banza. Haka ya kira Maman Aneesan ya mata bayani akan ba da yawunsa Aneesa ta koma Abuja ba. Buɗan bakin Maman sai ta ce “AbdulWahab idan ta ajiye aikin za ka iya ba ta dubu ɗari shida da hamsin a wata ne (650,000)?” Wannan maganar shi ya sa AbdulWahab ya sauke makaman yaƙin sa ya haƙura ba dan ya so ba, sai dan inda ya ke ganin za a mata faɗan ma goyon bayanta ake. Bai faɗawa iyayen sa ba sai da ƙannensa su ka je ma sa hutu bagtatan su ka tarar Aneesa ba ta nan da farko ce mu su yai ta je gida ne kawai daga baya su ka gano komai, nan Hajiya Yelwa ta ce ba ta san zance ba ta ya za’ayi yana Lagos matar sa na Abuja wai sai ƙarshen wata za ta zo…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button