SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Gidan ya cika saboda gobe ne walima jibi Asabat kuma a ɗaura aure. Farida tun da su ka dawo daga wajen jere ba ta samu zama ba, shiga ta yi cikin ma su haɗa kayan waliman gobe ana aiki da ita.
Cikin ma su aikin cupcake ta ke ana yi ana hira. Chan wata ‘yar uwar su wanda ita kan ta Faridan ba ta san takamaimai ta ina su ka haɗu ba ta ce ” Ikon Allah, kaman ba yau aka yi hidiman bikin Farida ba, na tuna cake ɗin da aka yi ranan mai daɗi, su Talatun Haruna ne su ka yi cake ɗin nan ko?”

Farida ta fusata da wannan zance. Ta miƙe tsaye ” Inna Tabawa ki ke ko wane. Wallahi ki riƙe girman ki, na ga take-taken ki tun awajen jere. Ba zan miki da daɗi ba”

“Daga magana. Ni na ce kiyi sosayya da ɗan shege” Taas Farida ta wanke ta da mari ai kuwa matan kowa ya tashi wasu su ka ja Farida gefe wasu kuma su ka tsaya da Inna Tabawa da ta ke ta zage-zage…

Kai tsaye falon Baffa Ummi ta shige da ita bayan an kawota wajen Ummin.

“Mi ye haka Aishah?, zafin kan ki har ya kai ki mari mace kamar Tabawa”

“Ummi so ta ke ta ci mutuncina cikin jama’a. Tun a wajen jere ta ke ta min habaici ina shareta. So ta ke wanda ma ba su san abinda ya faru ba su sani”

” shikenan?” Ummi ta faɗi ranta a ɓace

Farida ta kalli mahaifiyarta da mamaki ta ce “Ummi maganan Lukman fa”

” da ta yi maganan akwai abinda ya ragu ko ya ƙaru a jikin ki ne?”

Farida ta girgiza kai.

“To ni banga abin ɗaga hankali ba anan. Ƙaddarar ki ce ta zo da haka. Kuma Alhamdulillah Allah ya chanja mi ki da mafi alkhairi sai ki yi ta gode ma sa, ki share ‘yan gulma da gulmar su”

“Amma Ummi…”

“Kul. Ba na son jin wani magana, ki je ki nemi abinci ki ci ki samu ki huta”…

Ɗakin su Yakubu ta shiga ta ke cin abincin, ba wai daɗin abincin ta ke ji ba sai dai saboda Ummi ce ta takura sai ta ci. Gaba ɗaya zuciyarta na ma ta ɗaci. Duk yadda ta so ta basar da abin ta ka sa, kawai sai hawaye. Ta ya za ta manta da wannan rana a rayuwarta, ranan da ya kamata ace ya zamo ranan farin ciki amma kuma komai ya zo ya dagule, ya zamo ranan shine rana mafi baƙin ciki a tarihin rayuwarta. Sai da ta yi kuka mai isarta kafin ta share hawaye ta tattara kwanukan ta fita…

……………….

Anyi Walima lafiya, sai dai duk yadda Farida ta ci burin ganin anyi komai da ita abinda ya faru daren jiya ya kashe ma ta jiki. Da farko ma shiri ta yi kawai za ta wuce office amma amarya Jiddah ta hanata.
“Dan Allah Anty Farida kar ki tafi, ki taimakeni ki tsaya ayi komai da ke. Ke ce support ɗina Anty”

“Na san kin ji abinda ya faru jiya, ba na son tsayawa anan wata ta gayamin maganan banza mu kwashi ‘yan kallo. I dont want to ruin your day”

“Anty dan Allah ki mance da komai, Allah ina buƙatar ki kusa da ni fiye da kowane lokaci”

Da ƙyar Farida ta haƙura ta tsaya. An ci kuma an sha sannan an kira Malami ya yi wa’azi.

Washe gari Asabat ƙarfe shaɗaya aka ɗaura auren Hauwa Maijiddah Musa Wase da AbdulWahab Bello Hassan Kachako

Ɗaurin auren da ya samu halarcin manya-manya mutane, ta ɓangaren Alhaji Bello Kachako da shi kan sa AbdulWahab ɗin.
Da dare aka kai amarya gidan ta wanda kwana biyu kawai za ta yi su wuce Lagos…

Gidan Amarya Maijiddah kam bayan kowa ya tafi aka bar amarya da halayenta.
Tun safiyar yau ta ke gudawa saboda tsoro da fargaba.
Akwai mafiya yawancin mutane da idan su na cikin damuwa ko tashin hankali ko tsananin farin ciki ko baƙin ciki za ka ga yanzu-yanzu cikin su zai hautsine su fara ziryan banɗaki.
Maijiddah was nervous tun wayewar garin yau, abu ne da ta jima tana roƙo sai gashi ya tabbata, wai ga ta amarya. Ta sha Flagyl kam har ba adadi duk dan ta samu sauƙin wannan abun amma kaman tunda Maghriba ta do so abin ya fara ƙaruwa. Yanzu haka kafin Farida ta tafi sai da ta tabbatar ta sha magani amma yanzu da ta ke ita kaɗai sai ta ke jin cikin ta na ƙugi yana kuma murɗawa.

Tana cikin wannan yanayi wanda ta kira da ƙarshen kunya aka shigo ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin yai daidai da kukan da cikinta yai “ƙululululu”

A hankali ya tako wajen da ta ke ya ajiye ledar hannun sa akan drawer sannan ya tsugunna gaban ta ya sa hannu ya ɗaga gyalenta sama yana mai yin Bismillah.
Jikinta rawa ya ke, sai zufa ta ke haɗawa. Na farko saboda tsoro na biyu kuma saboda yanayin da ta ke ciki.

“Alhamdulillah, finally Gimbiya Allah ya nuna ma na wannan rana”

Duk maganan da ya ke yi sama-sama ta ke jin sa. Kamar ta saki ihu ta ke ji saboda kunya da haushin kan ta. Ta ya za ayi daren farkon su ace ta ɓarke da gudawa, wannan abin kunyan har ina.

Hannunta ya kamo yana wasa da yatsunta bayan ya zauna kusa da ita.
“Bari mu yi sallah sai mu ci abinci, na san baki ci wani abin kirki ba yau”

A karo na ba adadi cikinta ya sake yin ƙugi, wannan karan kam AbdulWahab ya ji.

“Sorry princess yunwa ko?”

Idan ta cigaba da shiru za ta cutu haka nan da kunya ace ta gaya ma sa matsalarta sai dai ya za ta yi.

“Ki shiga ki yi alwala ni inada alwalata” ya katse tunanin ta

Ai da sauri ta miƙe ta shige banɗakin. Duk yadda ta so ta daure ta yi alwala amma hakan bai yiwuba dole dai sai da ta je ta zauna a toilet. Ƙarshen kunya sai ga shi ƙaran gudawan na fitowa da ƙarfi wanda tabbas ta san AbdulWahab da ke ɗakin ya ji.
Ta gama amma kunya ya sa ta kasa tashi ta yi flushing, ta jima tana zaune daga baya ta yi ta maza ta tashi ta flushing na shi sannan ta yi alwala. Sai dai ka sa fitowa ta yi daga banɗakin dan ba ta san da wanni ido za ta kalli AbdulWahab ba.

Jin shiru kuma ta ƙi fitowa ya ce ” gimbiya ko na zo na fitar da ke ne?”

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito. Daga bakin ƙofa ta tsaya kanta a ƙasa ta ce a hankali ” I’m sorry, cikina ne ya ruɗe Yaya”

Tasowa yai har wajen da ta ke tsaye ya kamo hannunta ya ce ” There’s nothing to be sorry about my dear, mun riga mun zama ɗaya ai”

Sai da ya zaunar da ita sannan ya ce “kinsha magani?” Ta ɗaga ma sa kai.

“Barin haɗo mi ki tea sai ki fara sha”
Fita yai daga ɗakin wanda cikin minti shabiyar da ya ɗauka sai da Maijiddah ta sake zagayawa banɗaki.

Lokacin da ya dawo ya sameta a ɗan kwance gefen gado. He know she’s nervous shiyasa ta ke experiencing wannan abun. Ya tuna akwai wani abokinsa mai irin wannan, ko exam za su yi sai ya ɓarke da gudawa, a ranan da za su fara exam na Waec shekaru da dama da su ka wuce sai da Hussaini ya makara saboda ruɗewa da cikinsa yai.

A yadda ya ganta she’s already weak, idan yai yunƙurin yi ma ta wani abu that will label him a cruel man.
Taimaka ta yai ta tashi ta sha tea ya haɗa ma ta da kaza.
“Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki, ki ci ki samu ƙarfin jikin ki”

Shi da kan shi ya fara ba ta naman a baki har ta ƙoshi. Ya ce ta shiga ta yi wanka ta ce na yi.

“Kinga yanzu jikinki ya tsatstsafo da gumi saboda tea da ki ka sha. Ki je ki watsa ruwa”

Gaba ɗaya kunya sai ya sake rufeta. Ta tashi ta shiga ta sake wanka da ta fito ba ta same shi ba ya tattara wajen. Ta yi saurin buɗe closet ta nemo kayan bacci riga da wando ta sa, sannan ta ɗaura hijab akai.

Da ya dawo a zaune a bakin gado ya sameta.
“Hauwerh cire hijabin nan akwai zafi”

Ba mu su ta cire hijabin ta sunkuyar da kai tana wasa da bakin pyjamas ɗin ta.

“Ya cikin na ki?”

“Da sauƙi”

“Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru kin ji”

Ta gyaɗa kai.

“Now breath in and breath out”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button