SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ba ta gane ba har sai da ya nuna ma ta yadda za ta yi da kan sa sannan ta yi yadda ya ce. Sai da ta yi kusan sau goma kafin ya ce ta kwanta.

Kafin ya shimfiɗa sallaya yai sallar nafila tuni bacci ya sace amaryar sa. Da ya idar sai ya gyara ma ta kwanciya sannan ya kwanta bayanta ya musu addu’a ya kashe wutan ɗakin…

Washe gari da kunyar sa ta tashi tunowa da tai da abinda ya faru jiya. Sai dai shi kam ko ajikinsa, nuna ma ta yai wannan shine amfanin auren domin sun riga sun zama ɗaya. Duk wani matsalarta na shi ne, haka nan duk matsalarsa na ta ne.

Da dare su ka je gidan su sallama, daga nan su ka wuce gidan su Maijiddan. A wannan lokacin Farida ta tambayeta ko gudawar ta tsaya kafin ango ya shigo. Maijiddah ta ce “inaa, Anty ni kam ai na sha kunya” a taƙaice ta gaya ma ta abinda ya faru Faridan ta yi ta ma ta dariya.
Ba su jima ba su ka wuce saboda da sassafe jirgin su zai tashi.

Daren ranan ya gaya ma ta basic abubuwan da ya kamata ta sani gameda airport da jirgi. Sannan ya jaddada ma ta ba abinda zai faru yana tareda ita.
Ko breakfast ba ta iya yi ba saboda kar ta ci wani abu ya dameta. Ƙarfe tara jirginsu ya wuce Lagos. Kuma Alhamdulillah Maijiddah ba ta yi gudawa ba, sai dai ta tsorata kam lokacin da jirgin zai tashi, ba dan AbdulWahab na riƙe da hannunta yana kwantar ma ta da hankali ba ƙila da ta yi kuka. Sai da jirgi ya lula sama sannan ta ɗan samu nitsuwa kaɗan…

Asha amarci lafiya Maijiddah (banda gudawa plz????)

…………………….

Safiyar Monday Farida ta fito aiki duk da kuwa gajiya bai saketa ba, sai dai kamar yadda ta yiwa Maijiddah dariya sai gashi itama tana tsaka da aiki cikinta ya hautsina. Da farko sharewa ta yi tana mita ” mutum ya yi ta ciye-ciyen mai kwana biyu ba dole ciki yai ta kuka ba”

Sai dai fa lokaci guda ta kasa yin komai ta tashi ta nufi office ɗin Najeeb da gudu dan nan ne kusa da ita sannan ta ɗauka baya office ɗin dan ya fita ɗazu ya je meeting. Abinda Farida ta manta shine ya riga ya dawo tuntuni.
Da gudu ta zo ta wuceshi yana zaune yana aiki, kafin ta ƙarasa ma ta saki tusa a hanya.
Yana shirin buɗe baki yai magana kan shigo ma sa office da ta yi da gudu ya ji ƙaran tusan da ta yi…

Hankali kwance Farida ta zauna ta zazzage kayan cikinta, dama tun ran asabat rabon da ta yi, ga shi ba ƙaramin abinci ta ci ba a bikin nan. Ta jima a ciki kafin ta wanke ta yi flushing, kasancewa banɗakin yai gum sai ta ɗau air freshner ta feffesa ta ƙara buɗe windown banɗakin da kyau saboda iska ya ratsa.

Ta fito tana ɗan daddanna ciki tana faɗin “kai abubuwan da na ci a bikin nan ai sai barka. Kashi rahama ne Allah, ka ji yadda na ji wani saƙayau lokaci guda”

Cak ta tsaya da tafiya lokacin da muryan da ba ta taɓa tunanin ji ba a wannan lokacin ya doki kunnenta

“Miss Salihu”

Kaman ta nitse cikin office ɗin haka ta ji sai dai ita Aisha Farida ce dole ta nuna dakewarta. Tukunna ma dama yana office lokacin da ta shigo? ko dai bayan ta shiga banɗakin ne ya shigo office ɗin.

“Miss Salihu whats the meaning of this?”

Da ƙarfinta ta waiwayo bayan ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya. Ita ɗin expert ce wajen waskewa, ta ce

“Daɗin abin ma kowa yana yi, abinda na yi ba farau ba ne akai na. Ni’ima ce da ubangiji ya baiwa bayinsa dan ya nuna ma na mu ɗin ba komai ba ne. Da Sarki da shugaban ƙasa da maikuɗi da talaka, malami da jahili, mai kyau da mummuna, mace ko namiji, fari ko baƙi. Dukkan mu muna da buƙatar wannan ni’ima. Abu ne ba babba ba yaro”

Ta ɗan haɗe rai ta ce ” yanzu haka Sir Najeeb kai ma wannan ni’imar sai da ka yi ta kafin ka zo office yau, ko tun jiya rabon da ka yi?”

The girl is really crazy, taya za ta yi abin kunya and pretend kaman ba komai. Masifa ya ke so ya ma ta amma maganganunta sai su ka kusa sa shi dariya. Ya daure ya ce ” Miss Salihu a wani dalilin ya sa ki ka yi min amfani da banɗaki?”

“Saboda ya fi kusa da ni mana”

“This should be the last time da za ki yi haka”

“Ok Sir”

Har za ta wuce sai ta juyo ta ɗan yi gyaran murya ta ce ” Sir ina da magana”

Ido ya ɗaga ma ta alamar miye.

“Sir, tsakani da Allah tusar da na yi ɗazu ka ji ta?”

Kallon-kallo su ka tsaya yi. Har ga Allah tana son sani dan bayan ƙarar da tusar ta yi ba ƙaramin wari ne ya biyo bayan tusar ba.

“Get out of my offfice”…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Last Free page

0️⃣1️⃣5️⃣

“Mama har yanzu bai kirani ba, ina ga bai san ma na yi yaji ba fa” Aneesa ta faɗa cike da damuwa a ran ta.

“Ya ki ke so na miki? Na kira AbdulWahab na ce ka zo ka bada haƙuri matar ka ta yi yaji ko ya?”

“Mama do something please, ba zan iya sharing mijina ba”

“An riga an ɗaura auren Aneesa live with it. Ke ne za ki san yadda za ki riƙe gidan ki ta yadda yarinyar ba za ta samu kan shi ba”

Aneesa ta ɗan ɓata fuska ta ce “Mama ta ya zan yi hakan bayan bana zama a Lagos”

“Za ki ajiye aikin ki kenan?”

“Hell no. Ta ya zan bar career ɗi na when i’m at its peak. Ko kaɗan”

Mama ba ta ce komai ba, to mi za ta ce. Itama mace ce da mijinta ba ya gabanta. Ta taso da aƙidar ‘yan cin kai, yau tana Dubai gobe tana China wajen saro kaya, kasuwancin ta shine a gaban ta. Auren fari ta haifi Aneesa da Nazir, da ta auri Alhaji Abdullahi ma ɗa ɗaya ta haifa ta rufe haihuwa. Kuɗi kuɗi su kawai ta sa a gaba ba ta da lokacin kula da iyalin ta balle tarbiyyan yaran ta, shi ya sa ko kishiyoyin ta ba sa gaban ta, dama kuma kowa gidan ta daban…

…………………

Farida na zaune wani saurayi ya shigo neman Najeeb.
“Wa za a ce?” Ta tambaya lokacin da ta ɗau wayar.

“Ki ce ƙanin shi”

“Sir wai ƙanin ka na neman ka”

Ajiye wayar ta yi ta ce ” ya ce ka shiga”

Ba a jima da shigar wannan baƙon ba Anas ya zo shima ya shiga.

Dukkan su uku zama su ka yi ana taɗin bayan rabuwa.

“Big B tunda ka ƙi auruwa mu zamu shige gaban ka fa, dan na gaji da zama tuzuru”

“Shege yaushe ka dawo da za ka fara maganar aure. Anas see this small boy fa”

Anas dai murmushin ya ƙe yai dan ya san inda maganar za ta tsaya ba za ta ma sa daɗi ba.

Farida ta shigo ta samesu a haka, bayan Anas ba ta taɓa ganin Najeeb ya sake yana taɗi da wani ba. Sai dai kamar yadda wannan saurayin ya ce shi ƙanin sa ne ƙila su na da alaƙa tunda dai a yadda Anas ya gaya ma ta ƙanwar Najeeb ɗaya ce wato Najdah. Wata ‘yar girman kan kaman yayan na ta.
Kai tsaye wajen Najeeb ta nufa a wajen kujerun da su ke zaune wanda anan ya ke saukan baƙin sa.

“Sir ga wannan ana buƙatar signature ɗin ka anan” ta faɗi lokacin da ta miƙa ma sa wasu takardu.

Ya amshi takardun ya fara dubawa.

“Kai Big B wannan hottie as a secretary ai za ta ɗauke hankalin ma su zuwa wajen ka”

Najeeb ya ɗago ido ya ma sa wani kallo wanda ya sa yai saurin chanja magana da cewa.

“Ba wanda ta kai sweety na kyau ai. Najdah is the epitome of beauty ba ƙarya”

Gyaran murya Anas yai sannan ya ce “Musty zan wuce office, sannu da zuwa”
Musty ya miƙa ma sa hannu su ka gaisa. Idon Farida na kan Anas wanda ta ga ya chanja lokacin da Musty yai maganar Najdah. Tun farko-farkon fara aikinta ta san Anas ya na son Najdah, duk da kuwa Anas ɗin bai iya buɗan baki ya faɗawa Najdan ba har yau.

“Ya Anas dan Allah ka ɗan jirani minti biyu” ta faɗa tana murmushi.

Sauke idon da za ta yi domin ƙarɓan takardun da Najeeb ya gama signing sai ta ga idon shi chul akan ta. Ba ta san ma’anan wannan kallon ba amma ta fassara shi da cewa kallo ne da ke nuni da zan gamu da ke.
Da ta amsa takardun ta ce “Allah na gani ni ban ci bashin kowa ba, kurwata kur”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button