SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Auren Alhaji KB Amina ta samu kwanciyar hankalin aure wanda rabonta da shi tun aurenta da Salihu. Bayan da result na Waec ɗin ta ya fito Alhaji KB ya nema ma ta admission a UJ ba ta samu ba dan haka kawai ya nema ma ta ADR CLIS (AD Rufa’i College for Legal and Islamic studies) da ke Misau inda ta fara karantar Law. Da ta gama diploma lokacin ɗan su ɗaya Hamza, ta fara koyarwa a makarantar sa kafin ta cigaba da karatu. Sai dai samun wani cikin ya sa ta ajiye batun karatu a gefe tukunna. Ta cigaba da renon cikin ta.
Zaman Amina da Alhaji KB zamane na amana yana son Farida tamkar shi ya haifeta har lokacin da ta haifi Hamza bai taɓa nuna wa Farida banbanci ba. Alhaji KB ɗan asalin Jahar zamfara ne yanada ‘yan uba amma a wajen mahaifiyar sa su biyu ne shi da ƙanwar sa Hannatu. Mahaifiyarsa ta rasu tun yana shekara shida. Uƙuba na matan uba ya sa ya koma wajen ƙanwar Mamansa da ke aure a Jos lokacin yana shekara sha ɗaya. Anan yai karatu ya zauna har ya kai matsayin da ya ke yanzu. Hannatu ta jima da rasuwa. Ta rasu jim kaɗan da barinsa Zamfara. Raliya ɗiyar Hajiya Aina’u mariƙiyar sa ya aura. Sai dai har Allah ya ma ta rasuwa ba su taɓa haihuwa ba. Haka nan bai ƙara aureba sai akan Amina. Sau biyu tak ya kai Amina Zamfara inda anan ta gane ‘yan uwan Alhaji KB ba sa ƙaunar ta, shi ɗin ma abin hannunsa ya sa su ke ɗan girmamashi.
Abdul na da shekara biyu Alhaji KB ya rasu. Mutuwar da ta gigita Amina da Hajiya Aina’u. Lafiya-lafiya ya tafi Zamfara kawai sai yayan sa Ubaidu ya kira wai Kabiru ya rasu zazzaɓi ya sashi a gaba da dare kafin safiya ya cika.
Amina ba ta shiga tashin hankali ba sai da kwana ishirin kacal da rasuwan Alhaji KB ‘yan uwan sa su ka zo su ka koreta a gidan sa. Ƙarshe a gidan su ta ƙare takaba. Kafin wata uku da rasuwar sa su ka saida makarantar sa da gidan sa da mafi yawancin kadarorin sa. Hajiya Aina’u da Amina sun yi ƙoƙarin shigar da ƙara Kotu sai dai tun farko da su ka yi yunkurin hakan aka rufe bakin su. Haka nan Amina wadda ‘ya’yanta ke kira da Ummi ta koma gidan jiya sai dai wannan karan tana da ilimi daidai gwargwado da kuma wayewa. Wata makarantar ta nema aiki kuma ta samu da wannan ta ke yin hidimar yaranta da shi. Tsohon mijinta Ibrahim ya nemi ta yi kome saboda yanzu ya rabu da Kubura kuma Alhamdullillah matar sa Hafsatu tanada kirki. Ummi ta ƙi tace ita da aure har abada. Ba yadda Babanta bai yi ba amma ta ƙi ta ce aure huɗu da tayi a baya sun isheta. Yaranta uku na gabanta Farida, Hamza da AbdulMalik. Shi ma Faruƙ ya kan zo hutu wajen Ummin sa lokaci zuwa lokaci har lokacin a Kaduna ya ke. Hajiya Aina’u na ƙoƙarin taimakawa Amina da ɗawainiyar yara daidai gwargwado sai dai fa har yau ‘yan uwan KB ba su waiwayeta ba balle su nemi taimakawa yaran marigayi. Gado da ya bari kuma babu batunsa dan tuni sunyi wasan kura da dukiyar sa.
Aisha Farida Salihu yarinya da ta taso da ƙiriniya ga surutu. Ba dai ka faɗa ta yi shiru ba. Kwata-kwata ba ta da tsoro, tana son umminta sosai gashi ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba, idan ka ga suna hira tamkar wa su ƙawaye. Sau tari ma akan ɗauka ya da ƙanwa ne su. Tunda su ka koma gidan su Ummi, Farida ta dena zaman banza ganin dai yanzu ba da bane. Ta koyi kitso da lalle tana yi, ga saida kayan ƙwalama da ta ke yi a school. A haka har ta ƙare secondary school ɗin ta. Jamb ɗin ta na farko ba ta ci ba dan haka ta fara zuwa koyon computer a shagon ƙanin Umminta Ahmad. Ta koyi abubuwa da dama dan Alhamdulillah Allah ya bata ƙwaƙwalwa. Da ta sake Jamb ta tafi Federal polytechnic da ke Bauchi saboda UJ da ba ta samu ba. Business Administration ta karanta a ND da ta zo HND ta koma Marketing. Aisha Farida ‘yar kasuwa ce tuƙuru. Dan tana makaranta ba ta zauna haka ba ita ce saida turare, takalma da jakukkuna. Ga shi duk hutu idan ta je Jos za ta saro gwanjuna ma su kyau ta zo tana sayarwa students. Wannan ya sa ‘yan ajin su ke kiranta Aisha mai gwanjo.
Yanzu shekarar ta ashirin da uku, tana service a Yola. Tun a camp su ka haɗu da Yasir Sa’ad ɗa ga senator Sa’ad Babagana. A UK Yasir yai karatu. Da farko su na fita daga camp zai relocating zuwa Abuja Inda iyayen sa su ke sai dai soyayyar Farida da ya shigeshi farat ɗaya ya sa ya fasa. Hakan ya sa a Inda aka turata primary assignment ɗin ta shi ma ya je. Duk iya watannin da su ka yi tare Farida ba ta bashi dama ba. Tausayin sa ta ke ji ta girme shi da shekara ɗaya ita kuma tana ganin tsayawa soyayya da shi ɓata lokaci ne. Ga uwa uba kiran da Hajiyar sa ta mata akan ko da wasa kar ta amince da soyayyar Yasir saboda karatu zai yi hakanan akwai alƙawarin aure tsakanin sa da wata. Ita dai Farida ba dan tsoro ta ke baya-baya da shi ba ko kuma ta ƙi son sa ba sai dai bazata bawa kanta ciwon kai a kan Yasir ba. “Yaushe ma ka girma?” Abinda ta ke yawan gaya ma sa kenan.
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Free page
0️⃣0️⃣2️⃣
Da dare baƙuwar number ya kirata, da ta ɗauka sai ga muryan Rayyan.
“Ɗankwassi! a ina ka samu number ta?”
“My Farida kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu”
“Chan ta matse ma ka” ta faɗi tareda kashe wayar.
Ya sake kira ba ta ɗauka ba. A hankali a hankali Rayyan ya cigaba da kiran Farida, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya ke. Cikin sati uku sai da ya san yadda ya ja hankalin Farida har tana ɗan kulashi ta dena ma sa faɗa idan ya kira.
Ranan da su ka yi passing out ɗin su sai ga shi a Yola. Ta ji mamaki hakanan kuma ya ɗan samu matsayi a zuciyarta. Saboda Yasir ya haƙura da ita ya sa ta introducing Rayyan a matsayin saurayin ta. Yasir kamar ya haɗiyi ran sa saboda baƙin ciki haka su ka rabu da shi baran- baran. Ko sallama babu.
Rayyan Abdullahi ɗan Kano ne kuma ma’aikaci a Zenith bank. Ya je Bauchi ta’aziyar ‘yar yayarsa da ta rasu su ka haɗu da Farida. Sosai ya ke jin Farida a ransa, tsiwarta da masifarta yana burgeshi matuƙa. Ya ɗau ɗamaran koyawa Farida son sa musamman da ya gane ba ta da wani tsayayyen saurayi. To ina za ta yi saurayi bayan masifarta kaɗai ya isa ya sa samarin su dinga gudun ta.
…………………………….
Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye ɗakin sa ya wuce dan ya san Daddy ba ya nan balle ya je ya gaida shi. Ya na shiga ya danna SHS zuwa Main kitchen “lemon tea in 10minutes” ya faɗi tareda zama ya fara cire socks na shi daga nan ya cire gaba ɗaya kayan jikin sa sannan ya shiga toilet.
Adama ta zo haurawa ɗauke da tea ɗin Najeeb ta haɗu da Afrah da ke shirin haurawa saman. Ta duƙar da kai ta gaisheta, Afrah ta amsa a gatsine.
“A Ya Najeeb za ki kai wa?”
Adama ta amsa da “eh”
“Kawo zan kai masa” ta ƙarɓi tray ɗin daga hannun Adaman.
Ta cigaba da hawa stairs ɗin tana tafiya ƙarar takalminta na ba da sautin ƙas- ƙas- ƙas…
Tana jin ƙaran ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido.
“What the fuck! Mi ki ke yi a ɗaki na” Ya daka ma ta tsawa