SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Har ta fita daga office ɗin bai daina kallon ta ba.
Musty cikin fake American accent ɗin sa ya ce ” Your secretary is funny and cute”
“Ba ka daina halin na ka ba ko?”
“Sorry Babban yaya”
Tana fita ta tadda Anas na tsaye yana jiran ta. Gaba ɗaya fiskar sa ta chanja bisa yadda ta san shi da, shi ba kaman Najeeb bane kullum fiskar sa a sake ta ke gashi da son barkwanci.
“Yaya na ban gane wannan ɗan adawar ba fa, shi waye?”
Murmushin ya ƙe yai ya ce “ɗan ma su gida ne. Mustafah Sulayman Jibo kenan”
Kalmar da ya faɗa ta ‘ɗan ma su gida’ ya sa ta tuna da audion da aka ce ta yi kwanakin baya inda ake cewa shi ɗin ɗan Maigadin gidan su Najeeb ne, kenan da gaske ne.
“Ya Anas kar ka damu mu akai za mu dangwalawa. Idan da so ai ya share komai”
“Ki na ga Najdah za ta tsallake ɗan uwanta ta zaɓe ni ko kuma Daddy ne zai watsar da zumunci ya zaɓe ni?”
“Ya Anas da wannan ma amma tun farko kai ka yi sake. Da ka gina soyayyar ka a zuciyar ta da tuni an wuce wajen”
Girgiza kai yai ya ce ” Farida ba za ki gane ba”
Wucewa yai ya bar office ɗin ran sa ba daɗi…
Najeeb na zaune da Musty ne amma hankalin sa na kan tunanin mai Farida za ta faɗawa Anas. The girl is mischievous, yanzu haka wani gulma ta ke yi.
A wajen cin abinci Farida ta samu Anas shi kaɗai, bai ordering abinci ba, ruwa ne kawai a gaban sa, yana zauna amma hankalin sa yai nisa cikin tunani.
“Ya Anas yau da garau-garau na zo, za ka ci” Farida ta ajiye kular tana ƙoƙarin buɗewa.
” ‘yar uwa yau ba na jin yunwa” ya faɗi ba tareda ya kalli abincin ba.
“Allah sai ka ci, nan nan na hana Yakubu abincin nan na ce a yaya na zan kaiwa amma ka gwaleni ba ka isa ba”
Ta fara zuba abincin a plate tana faɗin “Ya Anas yajin ya ji maggi fa, ga man ma sai ƙanshin albasa ya ke”
Sai da ta gama haɗawa ta tura gefen sa ta ce ” dan Allah ka ci”
Ba yadda zai yi dole ya ɗau spoon ya fara ci. Ita ma ta haɗa na ta ta fara ci. So ta ke ta ma sa maganar Najdah shi ya sa ta zo.
“And what is the meaning of this?” Muryan Najeeb ya gauraye ilahirin wajen.
“Anas miye haka?, babu respect tsakanin Oga da mere secretary. Ta ya za ka bari ta zauna a inda na ke zama na ci abinci. Are you trying to disrespect me kamar yadda ta ke disrespecting ɗi na”
“Najeeb is not…”
“Shut up” Najeeb ya katse Anas da tsawa. Wannan ya ja hankalin kowa ya koma kan su.
Ta shi Anas yai zai bar wajen. Farida ta ce “Yaya dan Allah ka tsaya ka ci abincin ka, ni barin bar ma sa wajen”
“Bar shi na gode Farida” ya faɗi sannan ya bar wajen.
“Girma ya faɗi, kuma wallahi an ji kunya”
Hannu Najeeb ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama ” I’m warning you Miss Salihu, ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki”
Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Najeeb shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama sadakarwa Najeeb marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta.
Ranan dai ita ɗin ma ka sa cin abincin ta yi. Mi ya ke damun Najeeb da har zai yiwa Anas haka, hakan ma agaban jama’a wanda duk a ƙasan Anas ɗin su ke…
Kai tsaye office ɗin Anas ta wuce da ga canteen. Yana zaune yana ta kan zane a takarda wanda da ka gani ka san yana zanen ne saboda huce haushi.
“Yaya na kar ka ce na cika gulma amma anya Sir Najeeb yana da lafiya kuwa. Gaskiya a binciki ƙwaƙwalwar sa”
“Lafiyar sa ƙalau Farida, kawai dai he has a rough life ne. Mahaifiyar sa then Sabreen, su suka maida shi haka”
“Sabreen?” Farida ta faɗa da alamar tambaya.
“Macen da Najeeb ya fara so ba”
“Dama duk girman kan Sir Najeeb ya taɓa soyayya? Abun mamaki”
“Kar ki damu da abinda ki ka ga ya yi ɗazu, anjima kaɗan za ki ga ya zo ba da haƙuri”
“Duk da haka Ya Anas, abinda yai bai ma ka adalci ba wallahi”
“Kar ki damu, abinda yai bai kai zuciyar sa ba”
“Wannan sirikin na ka Allah kaɗai ya san yanayin sa. Yau ka gan shi shiru anjima ya fara faɗa gobe idan ya fara banbamin bala’i har wani spark bakin sa ya ke yi”
Ai Anas bai san sanda ya fara dariya ba “kai Farida kinada abin dariya ba kaɗan ba”
“Allah Ya Anas wani lokacin kaman majnuni ya ke, ka san lokacin da aka kidnapping ɗin mu haka mu ka kwana mu ka wuni bai min magana ba daga baya kuma bini-bini sai ya ɗaukeni”
“To waya sani ko ke ce ke sa shi haukan”
“Ni Aisha Farida! Rufa min asiri kafin yanzu na ga query letter”
Ta ɗan gyara zama ta ce ” yawwa, da ma maganar Najdah zan ma ka”
Ya ɗago ya kalleta
“Mi zai hana ka faɗa ma ta kana son ta, you never know, sai ka ga an dace. Balle ni ina ganin tana son ka ma”
“Baba na gadi yai a gidan su har ya rasu, karamci na Daddy ne ya sa ya sponsoring karatuna tun daga primary har masters da na yi shi ya sa na zama abinda na zama a yau. Daddy is like my father amma kuma na san indai akan maganar Mustafah ne to zai zaɓeshi ya bar ni, domin Mustafah jinin sa ne”
” tsoro shi zai sa ka rasa masoyiyar ka wallahi. Ba ka taɓa ce ma ta kana son ta ba, ba ka gayawa Najeeb ba balle kuma Daddy, to dan Allah ta ya za su san kana yi balle har a dubi wanne ya fi dacewa da ita tsakanin kai da Mustafah”
“Ki bari kawai Farida. Gara na zauna a matsayina”
“Dan Allah kar ka bani kunya ma na”…
………..
Lokacin da aka dawo daga break ta koma office ɗin ta. Ko da aka zo neman Najeeb ta kira office ɗin sa amma bai ansa ba, ta shiga office ɗin amma baya nan. Har banɗaki sai ta leƙa amma shiru. Numbar sa ta fara kira amma ba ta shiga.
Daga ƙarshe dai ranan har aka tashi ba ta ga Najeeb ba. Haka nan ba ta san inda ya je ba dan da ta fita ƙasa ta tambayi security aka ce ma ta Najeeb ya fita da mota tuntuni.
A zuciyarta ta ce “ai dole ka gudu tunda ka yi abin kunya”…
Tunda ya bar canteen kai tsaye motar sa ya je ya ɗauka ya bar kamfanin, ya na shiga gida ɗakin sa direct ya wuce ya samu gefen gado ya zauna tare da dafa goshin sa. He cant believe wai shi ne yai wa Anas tsawa. Anas fa, Anas da duk faɗin duniyan nan ba shi da aboki kamar sa. Saboda me?
Shi kan sa bai san dalili ba, ya san ba laifin Anas a zaman da Farida ta yi a wajensa. Sai dai ya rasa dalilin da ya sa maimakon ma ya ji haushin Farida sai ya kasance ya fi jin haushin Anas akan ta. Bai san ya za’a yi ya dena jin haushi ba duk lokacin da Farida ta ke tareda Anas.
Ya jima yana tunani a ran sa kafin ya tashi ya fara cire kaya dan ya watsa ruwa.
……………
Samun Anas ta yi akan dan Allah ya kaita gidan su Najeeb ta bashi wa su takardu sannan ta bashi saƙonnin wanda su ka zo ba su sameshi ba tunda wayar sa a kashe ya ke. Yana sauketa a compound ɗin su ya juya ya tafi dan shima bai shirya fuskantar Najeeb ɗin ba, ko da kaɗan ne to ya ji haushin abinda Najeeb yai.
Ranan da su ka zo gidan da dare ba ta lura da gidan ba, saboda dare da kuma hali na gajiya da rashin lafiya. Amma yanzu kam ta ga yadda gidan ya ke da girma da kyau, sai da ta gama yabon kyaun gidan a zuciyar ta kafin ta wuce ciki. Doorbell ta danna tana jira a buɗe.
Najdah da Afrah ke cin abinci a dining saboda har yanzu Mom ba ta dawo daga Bahrain ba.
“Adama…. Adama ki zo ki buɗe ƙofa”
Adama ta fito da sauri ta nufi ƙofan.
“Sannu, wa ki ke nema?” Adama ta tambayi Farida da ke tsaye a bakin ƙofa.
“Ni sakatariyar Najeeb ne, na kawo ma sa saƙo yana nan?”
” ki shigo”
Ta matsa ma ta ta shiga.