SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ƙarfe tara saura minti shabiyar ya gama bitar abin ya kira Farida. Ta san dole zai kirata domin ta ɗauka ma sa laptop da wasu files dama.
Ƙoƙarin tashi yai a kujeran ya ji ya ka sa tashi. Da ya tashi sai kujeran ta biyoshi.
“What’s this” ya faɗi lokacin da ya ke ƙoƙarin raba takashinsa da kujeran amma hakan bai yiwu ba.
“Sir Najeeb ya dai?”
Farida ta faɗa kamar ba ta san mi ya ke faruwa ba.
Tsaki yai ya cigaba da ƙoƙarin raba jikinsa da kujeran.
“Sir idan ka ja da ƙarfi zai yaga ma ka wando ka ga anyi ba ayi ba kenan. Tsuliyar CEO Najeeb constructions a waje” ta sa hannu ta ɗau flash ɗin da ke kan table ta ce ” tunda takashin Oga ya maƙale a kujera sai na kaiwa Ya Anas kawai yai presentation ɗin tunda dama shi ya kamata yai tun farko”
Sai da ta fara tafiya ya ƙwalla ihun sunan ta da ƙarfi “MISS SALIHUUU”
Ta waigo tana fari da ido ta ce ” SIR NAJEEB YA DAI”
difdifdifdif….. anan na kawo ƙarshen free pages. Na yi ƙoƙari ai har page 15. Well, za ka samu cigaban labarin idan ka biya 200 kacal. Stay safe and Allah ya mana albarka ya rufa mana asiri duniya da lahira ta ku AZIZAT
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣1️⃣6️⃣
Tana fita daga office ɗin Sir Najeeb office ɗin Anas ta wuce. Ta sameshi ya yi wani jugum da shi. Tabbas abinda Najeeb ya ma sa ya mugun kashe ma sa jiki.
Ajiye flash ɗin ta yi a gaban sa ta ce “Yaya na ga shi ka je ka yi presentation ɗin”
“Roƙonsa ki ka yi? Ko kawai ɗaukowa ki ka yi?”
“Ko ɗaya, Yaya na shi da kan sa ya bani ya ce na kawo ma”
“Ban yarda ba, Najeeb ba ya chanja magana da wuri. Kar ki damu ƙanwata, Najeeb shi ke da kamfani yana da ikon hana ni ko ya sa na yi abu”
“Ya Anas da gaske na ke fa, idan ba ka yarda ba ka zo muje ka tambayeshi”
Da farko dai Anas bai amince ba daga baya da ta takura sai ya tashi su ka fita, har lokacin dariyan Najeeb na cinta.
A ɓangaren Najeeb kuwa yayi nasarar raba jikin sa da kujeran amma kamar yadda Farida ta faɗi sai da wandon shi ta farke, wasu daga cikin pattern na wandon suna manne da gum ɗin a jikin kujera, wandon ya koma har ana ɗan ganin boxers na shi.
Najdah ya kira akan ta kawo ma sa kaya daga gida, ta ce ma sa tana school ai kuwa ya fara babbaleta da masifa abinda bai saba yi ma ta ba, idan ba masifa akan Mom ba, normally ba ya taɓa ɗaga ma ta muryarsa. Ganin yadda ya ke faɗa ya sa ta san lallai akwai matsala, dole haka ta bar class ta wuce gida.
Yana ajiye wayar sai ga Anas da Farida sun shigo, yai saurin komawa ya zauna akan kujeran dan kar Farida ko Anas ɗin su ga yadda bayan wandon sa ya koma a rarike.
“Sir Najeeb ina kai ka ce Ya Anas ya je yai presentation ko?”
Sai da ya ma ta kallon banza sannan ya kalli Anas ya ce ” ka je ka yi pitch ɗin nan, its already time”
Anas da mamaki ya ce ” miyasa ka chanja ra’ayin ka?”
“Oh please, just go”
“Ya Anas, Sir Najeeb ba shi da ja fa, kai ɗin ne dai za ka yi presentation ɗin”
Anas yai shiru yana nazarin Najeeb, akwai ɓacin rai mai tsanani a tattare da shi amma yanzu bai da halin tambaya saboda chanjawar da abokin sa yai. Ya karɓi flash ɗin daga hannun Farida ya juya. Farida ta bi bayan sa tana gwada irin tafiyar Najeeb. Sai da su ka kai bakin ƙofa ta juyo ta ce ” Sir Najeeb asha zaman kujera lafiya” sannan ta sa dariya.
Bayan fitan su da kusan minti arba’in Najdah ta zo mi shi da wasu kaya daga gida.
” Big B mi ya faru ka ke ta min tsawa ɗazu?”
“I’m sorry baby, i was just pissed off ne”
“Barin koma school muna da class”
Ok kawai ya ce ya jira sai da ta fita daga office ɗin sannan ya wuce banɗaki ya chanja kaya.
Lokacin da ya ga wandon wani haushin Farida ne ya zo ma sa har wuya. He’s 100% sure ita ta sa wannan abun a wajen, kuma ta yi ne domin ta hanashi presentation ɗin nan.
“All because of Anas” ya furta a fili.
Ya kalli kan sa a madubin banɗakin ya ce ” Did she really love him?”
Wanni ɓangare na zuciyar sa yana cewa miya shafeka idan tana son Anas, wani ɓangare kuma na cewa bai dace su yi soyayya ba, Anas is a good person amma wannan Ayshern, bai san ma ya zai kwatantata ba.
Shi dai abinda ya barwa ran sa shine dole ne ya hukuntata. Ya rasa miyasa ya ke kasa aiwatar da komai a kanta despite the fact cewa ta raina shi kuma tana karya dokokin sa son ran ta….
Najdah daga office ɗin Najeeb sai ta wuce office ɗin Anas. So ta ke ta sake tambayarsa ko da gaske ne yana son Farida, domin ranan ba ta barshi yai magana ba ta kashe wayar.
Ganin baya office ya sa ta yi yunƙurin tafiya idan ya so sa haɗu daga baya, sai hankalinta ya je kan wani hoton sa da ke kan table. Ta ɗauka hoton ta ƙura ma sa ido. A cikin tarihin rayuwarta tana son baƙin namiji, ita baƙin mutum na burgeta. Farar fata gareta amma many a times tana envying skin ɗin baƙaƙen mutane. Tun tana ƙarama ta san Anas, lokacin idan sun zo hutu Nigeria, su na tare koyaushe saboda tafi kowa kusa da Najeeb shi kuma shine kaɗai abokin Najeeb. Wani lokacin ko da Najeeb bai zo hutu ba to kullum tana tareda Anas, wannan ya sa ta shaƙu da shi tun a yarintar ta, shekaru uku da su ka wuce kuma ta fara jin wasu baƙin lamura game da shi wanda ita kan ta ba za ta iya fassara su ba. Ta ɗan shafa hoton sannan ta ajiyeshi.
Tana fitowa ta yi kiciɓus da Anas da Farida, da alama office ɗin na sa za su shiga amma maganar da su ke yi ya sa su ka tsaya a wajen. Dariya Anas ke yi sosai harda riƙe ciki. “Farida you are too much wallahi, abinda ki ka yiwa Najeeb kenan”
Doguwar tsaki Najdah ta ja wanda ya ja hankalin su.
“Najdah” Anas ya faɗa lokacin da ya juyo ya kalleta.
“An dai ji kunya” ta faɗa sannan ta bar wajen. Da sauri Anas ya bi bayanta yana kiran sunan ta.
Ta shiga lifter amma kafin ƙofar ta rufe Anas yai saurin sa hannu ya tare sannan ya shiga lifter ɗin shi ma.
“Najdah wai miya faru ne?”
“Dont pretend kamar ba ka san abinda ya faru ba. Sakatariyar Big B fa ka ke so. Sakatariyar sa”
A wannan dama da Allah ya bashi yau, dole ya cire tsoro kamar yadda Farida ta ce.
A hankali ya furta ” to miye a ciki? Ita sakatariyar Najeeb ba mutum ba ce?”
Wannan karan kaman za ta yi kuka ta ce “Yaya yanzu duk faɗin garin nan ka rasa wanda za ka so sai ita, that cheap girl”
Ƙwarai ya gane kishi ta ke amma bashida 100% assurance cewa kishin sa ta ke, sai dai dole ne ya tabbatar wa kan sa domin shi ta ke kishin.
“Najdah wa ki ke so na so? Wa ki ke ga zai so ɗan Maigadi”
“Yaya you know we love you, ka riga ka zama ɗan uwan mu yanzu”
Matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya ya ce “so idan ɗan Maigadi ya nemi ‘yar masu gida za ta amince?”
Jikinta yai sanyi haka nan kuma kusancin su da hannunta da ya riƙe ya sa ta fara jin wani baƙon yanayi ajikinta, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri.
Zuciyar sa ce ta ce ‘Anas is now or never’
A hankali ya kai bakin sa dai-dai kunnenta ya ce “i love you Najdah, only you”
Maganar yai dai-dai da tsayuwar lifter dan haka ta wafce hannunta ta fita da gudu. Bai bita ba, sai ma murmushi da ya fara yi saboda jarumta da yai yau, finally he said it…
Farida na zuwa office ɗin Najeeb ta tadda ya chanja kaya.
“Manyan mutane kenan, Allah ya ja zamanin ka CEO”
Fiskar nan ba fara’a ko kaɗan ya ɗago ya kalleta ya ce “your two weeks suspension starts now, Miss Salihu”