SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Suspension”

Sai kuma ta yi shiru.

“Two weeks suspension is not all, bayan kin dawo za ki serving punishment na ki”

“Hutarere wallahi. Hutun sati biyu ai gaba ta kaini, ka ga zan fara azumi a gida kenan dan Jos zan wuce. Na gode Sir Najeeb Allah ya ƙara daraja”

“Leave” ya faɗi da ƙarfi

“Sir Najeeb ina da magana” ba ta jira ya ce komai ba ta ce “tsakani da Allah abinda ka yiwa Ya Anas bai dace ba, ka san yadda mutumin nan ke ganin girma da darajarka amma ka walaƙantashi. Irin walaƙancin kun nan na ma su kuɗi ya sa ya kasa furtawa ƙanwar ka kalmar so, kaima kuma da ke ba ka damu da shi ba, sai ba ka gano son da ya ke yiwa ƙanwar ka ba”

Ɗago ido yai yana mamakin maganganun ta.

“A rage girman kai Sir Najeeb. Shi girman kai rawanin tsiya ne”…

Bai san lokacin da ta fita daga office ɗin ba saboda ƙwaƙwalwarsa da ta tafi duniyar tunani.

Anas na son Najdah, how when,why?. Kenan ba Aysherh ya ke so ba?

Da sauri ya miƙe ya bar office ɗin…

Wasu takardu Anas ke dubawa lokacin da Najeeb ya shigo, da ka gan shi ka san yana cikin farin ciki.

“You love my sister?” Ya tambayeshi lokacin da ya shigo.

“Najeeb…”

“Idan har kana son Najdah, why Miss Salihu again”

Dariya yai ya ce “tsaya Najeeb, waya gaya ma ka akwai abu tsakanina da Farida? I love your sister, ita kaɗai na ke so”

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja sannan ya bar office ɗin.

Nan zuciyar Anas ta ɗauko kan zan cen.

“Najeeb kishi ya ke da ni. Haba, dole biri yai kama da mutum ai. I suspected this tuntuni, Najeeb is inlove”

Murmushi ya biyo bayan maganar da yai wa kan sa, duk wani abinda Najeeb ɗin ya ma sa sai ya ga ya washe ko kaɗan baya jin haushin sa. The fact that Najeeb has feelings for someone else bayan Sabreen ai abun farin ciki ne. After 8yrs of loneliness.

Cikin kwana biyun nan abubuwa sun chanja. Najeeb ya koma yana jin kunyar Anas saboda abinda ya ma sa duk da kuwa Anas ɗin ya nuna komai ya wuce. Shi kan sa Najeeb ba zai iya faɗan dalili ɗaya da ya sa yai ma sa haka ba domin haushinsa ya ke for no reason amma kuma yanzu ya washe.

“Yau zan fara zuwa hira officially, sirikina ka gaya min tips wanni irin kaya Najdah ta fiso namiji ya sa”
Najeeb ya dundeshi ya ce “ɗan iska, ta fi son gwanjo”
Kalmar gwanjo da ya faɗi ya sa sunan Aysherh ya zo ma sa, kwana uku kenan da ba ta nan.

” abokina dan Allah kar ka manta a shigemin gaba wajen Daddy”

“Fuck you, Daddyn ne sai ni ne zan ma sa magana, kai ma ai ɗan sa ne you can talk to him about it”

“Ni ba marar kunya bane irinka ai”…

Anas na fita daga office ɗin sa ya tura wa Farida text akan an janye suspension ɗin ta resuming aiki gobe. Lokacin da text ɗin ya shigo Farida na bacci so ba ta gani ba.

Shigowar Khalidah office ɗin ne ya sa shi deleting ɗin text ɗin da ya ke shirin tura wa Farida ta ɗaya layinsa.

“Kwana na biyu da dawowa banga sakatariyar ka ‘yar gold ba. Ko ka koreta ne?”

” get out”

“Maida wuƙar Najeeb. Na zo maganar project da ake yi a Kaduna ne”

Ya nuna ma ta kujera akan ta zauna…

Farida na ganin text ɗin Najeeb ta yi tsaki ta tura ma sa reply kamar haka

Sir Najeeb ni ba zan dawo ba sai sati biyu sun cika, kana gani za a fara azumi nanda kwana biyu ka ce na dawo, gaskiya sorry

Lokacin da ya gama karanta text ɗin yai ƙaramar tsaki.

……………….

Sati biyun dai ba ta yi shi ba, sati ɗaya ta yi ta dawo saboda yadda Anas da Yakubu su ka takura akan ta dawo.
Duk da an rage awa ɗaya cikin lokacin aiki, hakan bai sa ta jin haushin aikin ba yanzu saboda watan azumi da aka shiga.
8-3pm ba wasa ba ne a wajen Farida ga ɗan karen zafi da ake yi a garin na Kano, ga ruwan sama ma dai har lokacin da azumi ya kai goma ba wani alamunsa sosai dan sau ɗaya aka yi ruwa. Daga ƙarfe shabiyu za ka ga Farida ta yi laushi. Da ƙyar ta ke kaiwa lokacin tashi.

Yau ma wani aikin da za ta yi Najeeb ke ma ta bayani.
Burping ta fara yi akai akai har sai da Najeeb ya fusata ya ce ” Miss Salihu will stop sounding like a frog”

(Burping kaman ƙwanafi kenan, ban san Hausa word na shi ba. Irin dai abinda ma su ulcer su ke yi ɗin nan ko kuma idan mutum ya cika cikinsa da abinci dayawa za ka ga daga maƙoƙoron ka kana fitar da sautin irgh irgh irgh )

“Sir Najeeb ba fa da gangan na ke ba, ulcer na ne ya tashi…” ba ta ƙare maganan ba ta kuma yi ya ce “Gosh! Miss Salihu get out”

Ba ta musa ba ta fita dan dama a gajiye ta ke…

Ya dawo daga sallar Azahar ya shiga office ɗin sa sai ya ji ƙanshin abinci. Abinci in his office a watan Ramadan? Ya juya inda ya ke jin ƙaran sokali and there he sees her. Ta barraje a ƙasa tana cin jollof ɗin taliya da macaroni.

“Since when did my office become your dining room?”

Ɗago ido ta yi ta kalleshi hannunta ɗauke da sokali totse da abinci.

“Ni ban ɗauka za ka dawo yanzu ba”

“Miss Salihu”

“Dan Allah Sir Najeeb ka barni, ka ga office ɗina kowa na shigowa ƙarangatsau, na ka office ɗin akwai privacy”

Zuwa yai ya zauna bai ƙara cewa komai ba. Lokaci zuwa lokaci yana ɗaga ido ya kalleta. Shi mamakin yadda ta ke cin uban abincin nan ya ke. Ko za a matse shi ba zai iya cinye abincin nan ba amma ita ya san zuwa anjima kaɗan za ta take shi.

Wata rana ana azumi goman ƙarshe, ranan anyi tsananin rana. Ƙarfe biyun rana sun je wani site Farida tana tsaye tana jin maganganun su har ta koma ba ta jin komai sai yijib ta faɗi ta suma. Najeeb da mutanen da ke wajen su ka yi kan ta.
Wanni Emmanuel na shirin kai hannu zai taɓa ta Najeeb ya daka mi shi tsawa “dont touch her”….

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣1️⃣7️⃣

Bayan ta farfaɗo ya sa aka kawo ma ta ruwa, maltina da madara akan ta karya azumi.

“Kai za ka biyamin ai idan na karya” abinda ta faɗa kenan lokacin da ya miƙa ma ta maltinan.

Ranan daga wajen ma ya maida ita gida ba tareda sun koma kamfani ba.

Haka dai a dararance ta cigaba da azumi har aka ƙare. Ana gobe Sallah aka ba su hutun kwana uku akan rana ta ukun sallah za a dawo. Farida kam cewa ta yi ba ta san zance ba sati ɗaya za ta yi. Ta wuce Jos ta yi sallan ta achan, duk da Kano za ta ga hawan sallah amma wannan baya gaban ta ta fiso ta ji ta jikin Umminta. Ƙila ma daga wannan sallah ita da sallah a Jos sai ta Allah.

……………..

Lagos

Sati uku Maijiddah da angonta su na kwasan amarci, ba ta da matsala dan yaransa ba ma su hayaniya sosai bane.

Iya Bose ke mu su girki, amma tana kwana uku da zuwa ta fara shiga kitchen tana taya Iya Bose sarrafa abinci duk da kuwa Iya Bosen ba ƙarya ta iya girki sosai. A wajen ta ta san favourite na mijinta ta kuma koyi yadda ake sarrafa su. Shi ba bayarabe ba amma yana son cin amala da sakwara, dan haka ta dage tana koyon su a wajen Iya Bose. Miya kam ta ga ikon Allah, domin ita dai a gidan su idan ba kuka, kuɓewa, ko alayyaho ba to ba wani special miya da ake yi. Akan yi miyar egusi wani lokacin saboda Baffa na so amma a wajen Iya Bose sai ta ga miyar egusin ma ba kala ɗaya ba ce. Haka ta dinga ɗaukan darasin girki a wajen ‘yar tsohuwar matar nan.

Daren Jumma’a da ya cika sati uku da auren su sai ga Aneesa ta zo.

Suna zaune su na kallo da yara a falo ta shigo, yaran suna ganinta su ka fara ihun mommy mommy.
A hankali Maijiddah ta fara satan kallon Aneesan duk da kuwa ta taɓa ganin hoton ta, amma ganinta a fili sai ta ga ta ƙara zama ma ta wata Madam. A ƙalla Aneesa za ta kai 36yrs ko 37yrs, amma jin daɗi da kuma samun mayuka ma su tsada sai ya ɓoye shekarun ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button