SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Nonye ta zo ta tafi da yaran bayan sun karya saboda makaranta da za su je. Su ma su Aneesan sun gama karyawan amma ta ƙi tashi saboda AbdulWahab ya ƙi ya ƙare cin abincin.
“Sweetheart time fa ya tafi”
Ya ɗan yi gyaran murya ya ce “yanzu zan gama. Yau na tashi da muguwar yunwa ne”
“Namiji munafiki” Aneesa ta faɗi a zuciyarta. Ta san dalilin Maijiddah ya sa shi ka sa ƙarasa abincin akan lokaci.
Ala dole ya tashi saboda Aneesa da ta tsaya a kan sa. Tare su ka fita daga gidan amma minti shabiyar kacal sai ga AbdulWahab ya dawo. Maijiddah na kan tattare dining ɗin ta ji an rungumeta ta baya. “Princess yau ba kya so na je office ko?”
” Yaya ni a su wa, ka je Allah ya kiyaye hanya”
“Wasa ki ke yarinya, wani office kuma bayan ban gaisa da gimbiya ta ba” ya ɗauko wayansa ya ma ta hoto kafin nan ya ɗauketa cak su ka shige ɗakin ta wanda shine mafi kusa.
…………
Wannan weekend ɗin ta je Jos kuma ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba domin weekend ɗin ƙarshen wata ne, kaso mai tsoka ta ware cikin kuɗin ta ta tafi nemo sexy gwanjuna a kasuwa, tanaɗin biki takeyi tun kafin abin ya matso daf ta rasa lokacin zuwa Jos.
“Kin gaya ma sa kin taɓa aure?” Maganar da ta sa Farida ta ka sa kai lomar tuwon da ta yanko kenan.
“Ba na so a samu matsala kin san ‘yan gulma, gara ki gaya ma sa tun kafin ya ji a waje”
“Ummi na ga ban tareba ai”
“Duk da haka, Farida ba na son a samu matsala a bikin ki irin na wancan karan. Gara duk wa ta ƙofa da zai kawo fitina a toshe ta tun kafin lokacin.
Da wannan zance ta koma Kano, zuciyar ta na tsoron abinda Rayyan zai ce idan ya ji wannan ba tu.
Sai da ta kwana biyu tana tunanin yadda za ta faɗa ma sa kafin daga baya ta yanke shawaran komai ta fanjama fanjam.
Tun kafin ya zo dama ta gaya ma sa tana da magana da shi. Dan haka da ya zo hira yau sama-sama su ka gaisa ya ce yana sauraron maganar ta.
“My Ray akwai abinda ya kamata ka sani gameda ni. It will come to you as a shock amma ka yi haƙuri”
“Ina jin ki”
“Na taɓa aure”
Ya zaro ido yana jiran ƙarin bayani.
“Yes, shekaru uku da su ka wuce an ɗaura aurena da Lukman, sai dai ko tarewa ban yi ba aka raba auren saboda matsalar da ta taso”…
Lokacin da ta gama bashi labarin Lukman yai shiru yana nazari daga ba ya ya ce ” kin ga ke rabona ne, shi ya sa komai ya wargaje a lokacin”
Ta yi mamakin maganar sa dan ta ɗauka zai yi fushi saboda rashin gaya ma sa da ba ta yi ba da wuri.
waye Lukman?….
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣1️⃣9️⃣
Khairat Ilyas Magaji ta taso cikin gata da jin daɗi a gaban iyayen ta. Iyayen ta ita kaɗai su ka haifa wannan ya sa su ka ɗaura dukkan ƙaunan su a kan ta. Mahaifinta da Mahaifiyar ta dukkan su mutanen Kebbi state ne.
Tana ƙare secondary school mahaifinta ya turata karatu ƙasar South Africa inda anan ta haɗu da Lawrence su ka fara soyayya.
Lawrence Schneider asalinsa Bayahuden ƙasar Germany ne amma a South Africa aka haifeshi.
Rashin isashshiyar ilimi na addini,rashin tarbiya mai kyau da kuma son zuciya su suka sa Khairat ta sakamar Lawrence ragamar rayuwarta har ta koma ko Sallah ba ta yi saboda idan Lawrence ya ganta tanayi yana fushi da ita.
Gidan da iyayen ta su ka kama ma ta, ya koma tamkar gidan ta da na Lawrence, domin kusan koyaushe anan ya ke kwana. A wani hutun dogon zango da ta zo Nigeria, lokacin shekararta na uku kenan a makarantar ta fara rashin lafiya. Aka ma ta treating ɗin shi sai kwana biyu kuma zazzaɓin ya sake dawowa. Wannan karan da su ka je asibiti aka ma ta gwajin ciki, sai ga shi result ya fito tana ɗauke da cikin wata uku.
Alhaji Magaji da matar sa ba su shiga tashin hankali ba sai da Khairat ta ce ai cikin na Lawrence ne.
“A Jew! Khairat ba ma Christian ba Jew. Wanda sun fi kowa tsanar musulmai” Alhaji Magaji ya faɗa cikin masifa.
Sun yi ƙoƙarin zubar da cikin aka ce mu su akwai haɗari saboda Khairat ta jima tana shan maganin hana ɗaukan ciki kuma ya sa mahaifarta yai rauni.
Lokacin komawa makaranta yai Alhaji ya hana Khairat komawa. Shi da kan sa ya je har South Africa neman Lawrence. Abin takaici a gidan da ya kamawa Khairat anan ya samu Lawrence yana hutawa da wata baturiyar karuwar sa.
Ko da ya shaidawa Lawrence Khairat na ɗauke da cikin sa dariya yai ya ce “who wants to have a baby with a moslem whore”
Alhaji dan takaici bai san lokacin da ya mari Lawrence ba. Abu kamar wa sa sai ga shi an kama Alhaji Magaji saboda ya mari Lawrence. Kasancewar sa baƙar fata ya sa abun ya kuma sawa kotu ta ɗau tsauri akan al’amarin. A ƙalla Alhaji Magaji sai da yai wata kusan uku a ɗaure kafin aka fitar da shi nan ma bayan ya biya tara wa Lawrence.
Wannan ya ƙunsawa Alhaji da matarsa baƙin ciki. Itama Khairat ɗin tunda ta ji abinda Lawrence yai sai jikin ta yai sanyi.
Duk min lalacewar ɗa dai na ka ne. Haka Khairat ta raini cikin shegen ta a gidan su har lokacin da ta cika watannin haihuwa. Wata rana da tsakar dare ta tashi da naƙuda iyayen ta su ka kaita asibiti. Ta jima tana labour kafin ta haifi ɗa namiji.
Nurse ɗin da ta sanar da su haihuwar Khairat ita ta cikata maganar da cewa Allah ya yiwa Khairat rasuwa.
Bayan an yi bakwai ɗin Khairat Alhaji ya fara shirye-shiryen barin Kebbi saboda gulmace-gulmace da ake yi akan mutuwar Khairat.
Garin Jos Alhaji ya dawo da iyalin sa, inda su ka cigaba da rainon Lukman tamkar ɗan cikin su. Tarbiyan da ba su bawa Khairat ba, shi su ka duƙufa su na ba wa Lukman.
Lukman Ilyas Magaji ya taso cikin tarbiyya mai kyau, ga shi dama yaron mai biyayya ne. Tun yana shekara shahuɗu yai haddar ƙur’ani, yana da ilimi na boko da addini. Alhaji Magaji da Hajia Zainab su ya sani a matsayin iyayen sa har ya girma ya zama ƙwararren Likita.
Wata rana a asibitin Juth inda ya ke aiki aka kawo wata yarinyar cikin uniform mota ya bigeta. Wasu couples ne Mr and Mrs Owulum su ka kawota saboda su ne su ka bigeta da mota.
Yarinyar tun kan a fara duba ƙafarta ta fara ihu tana kuka tana faɗin Allah ya isa.
Lokacin da aka fara stitching kuwa tana kuka tana lissafta abinda Mr Owulum za su kawo.
“Wallahi Kaji goma za ku kawo, na gida biyar na Agric biyar. Kuma wallahi luƙa-luƙa dan ba na son ramammu”
Dr Lukman bai san lokacin da ya fara dariya ba. Ƙarin dariyan ma, Mr Owulum da matar sa ba sa jin Hausa. Ita kuma ta dage sai lissafo abubuwan da za a kawo ta ke yi.
Sai da a ka gama ya kalleta ya ce ” Aisha duk lissafin nan fa ba su gane ko ɗaya ba, ba sa jin Hausa.”
“Kan Uban chan! To wallahi chicken, 10 big chicken Mr Igbo man”
Lukman mi zai yi ban da dariya. Kafin su tafi da ita sai da Lukman ya kusa fitsari a jiki saboda dariya. Ko da ya je gida sai da ya bawa Mom da Dad labarin Aisha mai Kaji goma.
Washegari ma Mr Owulum ne ya kawota amma wannan karan har da Ummi da Nanna. Anan ya ke tambayar ta ko an kawo ma ta Kajin.
Ummi ta ce “ashe a gaban ka aka yi ko?”
Dr Lukman ya ce “na ga alama Aisha na son kaza”
Da za su tafi ya ce “Aisha Kaji nawa su ka kawo”
“Dan uban su shabiyu, shabiyu su ka kawo”
Dr Lukman yai murmushi.
Duk zuwan da za su yi sai Dr Lukman ya tabbatar shi ya duba ciwon Aisha. Bayan sati biyu da haɗuwar su wata ranan Jummu’a sai ga Dr Lukman a gidan su ya zo gaisheta. A wajen Mr Owulum ya samu
address ɗin ta.
Har cikin gida ya shigo ya gaida Baba da su Nanna da zai tafi Farida ta rakashi har wajen motar sa.
Ya shiga mota ya miƙo ma ta ledoji guda biyu.