SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Dr green eyes har da wahala haka to an gode”

Dr green eyes ta ke ce mishi tun ranan da ta fara ganin shi, kasancewa ƙwayar idon sa green ne, wanda ya samo asali daga mahaifinsa Lawrenc.

A hankali Farida da Dr Lukman su ka shaƙu har soyayya ta shiga tsakani. Ko da ta zana WAEC da NECO Lukman ne ya ƙara ma ta ƙarfin gwiwa akan ta ci gaba da karatu. Da ba ta samu university ba ya ƙarfafa ma ta gwiwa akan kar ta zauna haka.

Lokacin da Farida ta ke aji biyu na diploma aka bayar da ita wa Lukman da zimmar tana ƙarewa za su yi aure.

Kowa ya san Alhaji Ilyas Magaji dattijon arziƙi ne, haka nan ɗan sa Lukman shima saurayi ne da aka ma sa shaida mai kyau a ko ina.

Rana ba ta ƙarya Farida ta gama diploma, aka fara shirye-shiryen bikin ta da Lukman.

A Wase za’ayi auren dan haka sati ɗaya kafin ɗaurin aure Farida ta koma chan. Mutanen Kano da Dukku duk sun hallara a wannan biki. Ba wanda ya fi jin daɗi ma kamar Baffa Musa saboda shi bai so har ta kai harka ba tareda an aurar da ita ba. Shi Mutum ne da bai yarda da karatun mace a gidan su ba.

Anyi kamu, anyi walima komai ya tafi lafiya. Ranan Asabat aka ɗaura auren Lukman Ilyas Magaji da Aisha Farida Salihu. Bayan an ɗaura aure ana ɗan gaggaisawa cikin ‘yan uwan Alhaji Magaji da su ka zo daga Kebbi, wani ya fara magana da Alhaji Magaji bayan ya tabbatar a kusa da Baffa Musa su ke kuma maganar ta su ba a hankali su ke ba.
“Allah ya jiƙan Khairat, yau da kun ma ta tarbiya kaman yadda ku ka yiwa Lukman da Lukman bai zama ɗan shege ba”

Alhaji Magaji ya haɗe rai yana hararan ɗan uwan na sa wanda su ke ‘yan uba.

Cikin rashin fahimta Baffa Musa ya ce ” ban gane ba Alhaji Magaji. Wani irin ɗan shege?”

“au ba ku san Lukman ɗan shege ba ne? Lallai! Ai Lukman jikan Alhaji Ilyas ne, wadda ‘yar sa ta haifa ma sa shi shege. Ance ma saurayin na ta ma wani bayahuden bature ne” Alhaji Kamalu yai wa Baffa Musa bayani.

Lokaci guda Baffa Musa ya hau faɗa yana masifa, kafin ka ce me wajen ɗaurin aure ya hautsine. Alhaji Magaji ba abin da ya ke sai hawaye.

Lukman na wajen masallaci su na hotuna da abokan sa aka zo ma sa da wannan mummunan labarin. Da farko bai yarda ba sai da ya shiga masallacin ya ga Alhaji Magaji yana hawaye. Shi kuma Alhaji Kamalu yana ƙara zuba bayani kan yadda Alhaji Magaji ya sakalta ‘yar sa Khairat har ya kaita ga karuwanci a ƙasar waje.
Lukman dai a take a wajen ya suma.

Amarya Farida tana cikin ƙawayen ta ana hira ana ma ta kwalliya. Sai tsokanarta su ke wai yanzu kam an ɗaura aure ta zama Mrs Lukman Ilyas Magaji.

Wajen ƙarfe sha biyu ta gota kaɗan labarin abinda ke faruwa ya iso mu su gida.

Wassu cikin ‘yan uwan su mata su ka fashe da kuka ana ta kururuwa ciki har da Inna Tabawa.
Wannan hayaniya ya sa Farida da ƙawayen ta su ka fito daga ɗaki su na tambayar abin da ke faruwa.

“Wai ashe Lukman ɗan shege ne” wata ta faɗa da ƙarfi.

“Ɗan shege kuma?” Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.

“Wallahi, ance uban sa ma kafiri ne. Yanzu haka su Baffa Musa sun ce sai ya sake ki dan ba za ki auri ɗan sheg…” ta tsaya da maganan lokacin da Farida ta yafuto ta tana dukan ta ta ko’ina.
Da ƙyar aka raba Farida da matar nan. Farida sai zage-zage ta ke tana faɗin ita ko Lukman ɗan Alade ne za ta aure shi.

Gidan biki fa sai ya zama tamkar gidan makoki. Zuwa ƙarfe tara na dare kafin su Baffa Musa su ka dawo kowa so ya ke ya ji mi ake ciki amma Bai yi magana ba cewa yai kawai a fara haɗa kayan lefen da aka kawo da duk wani abu da aka san daga gidan su Lukman aka kawo.

Farida ta yi kuka kamar idon ta zai zazzago. Zuwa tsakar dare zazzaɓi ya rufeta a inda ta ke zaune ta fara kakkarwa, ƙarshe ta faɗi ta suma…

A ɓangaren Lukman ma ko da ya farfaɗo sai da ya sake suma sau uku. Zuwa yamma da jikin sa ya ɗan warware su Baffa Musa su ka zo gadon sa da buƙatar ya rubutawa Farida takardar saki, tareda cewa sun mayar ma sa da sadakin sa yana wajen Alhaji Kamalu tunda Alhaji Magaji ya ƙi ƙarɓa.
Lukman bai ce mu su ƙala ba sai hawaye kawai da ya ke ta yi.

Washe garin da wannan al’amari ya faru Baffa ya karɓo takardar sakin Farida wanda har lokacin tana kwance a asibiti.

Duk da ‘yan uwan Lukman ba su buƙaci kayan da aka kaiwa Farida ba amma Baffa Musa sai da ya sa aka mayar mu su.

Wasa-wasa sai da Farida ta yi sati biyu a kwance a asibiti kafin aka sallamota. Tun daga nan ta koma kamar ba ita ba, ba ta surutu balle hayaniya. Kano Baffa Musa ya so ta bishi a lokacin amma ta ƙi, ta koma wajen Ummin ta a Jos.

Bayan wata ɗaya da dawowanta Jos, Lukman ya zo ya ma ta sallama akan zai tafi Egypt ƙaro karatu. Ya ma ta fatan alkhairi tareda cewa har abada ba zai dena son ta ba. Duk yawan surutun Farida ranan ka sa cewa komai ta yi sai kuka.

“Aisha ina miki fatan alkhairi, ina kuma mi ki kwaɗayin ki cigaba da karatu, and above all” ya goge hawayen da ke shirin zubo ma sa.
“I want you to open your heart for someone else. I want you to always be happy no matter what”

Ta fi jin tausayin shi fiye da kan ta. Shekaru talatin da ɗaya ace rana tsaka kawai a sanar da kai kai ɗin ba ka da asali, kai ɗin ɗan shege ne.

“Greeneyes, yanzu duk alƙawurran mu, duk burikan mu sun tafi a banza kenan?. Yanzu duk yadda mu ke son junan mu ba za mu kasance tare ba?”

Ajiyar zuciya yai ya ce ” za ki samu wanda ya fini Aisha. Kyau, ilimi, dukiya da wayewa za ki samu wanda ya fini su. Za ki samu wanda zai so ki fiye da yadda na ke son ki Aisha. You never know, sai ki ga idon sa ma yafi nawa kyau”

Farida ta ɗan yi dariya ta ce ” green eyes babu mai irin wannan siffan fa”

(Ni kam na ce ba ki je Kano ba ne????)

Wannan ne ƙarshen Farida da Lukman. Tun daga ranan ba ta sake ganin sa ba har yau.
(Amma ta ga mai siffofin da Lukman ya bayyana????)

Lokacin da aka fara saida form ɗin HND ta siya ta koma makaranta.

Wannan kenan.

……………………

Satin su ɗaya da dawowa daga Lagos aka aiko cewa sun winning bidding ɗin da su ka je, kuma an ba su dama su yi samfurin (modelling) wannan gine-gine da za a yi.

Wannan karon kam ta ga seriousness sosai a kamfanin, domin ko yaushe ana kan meeting yadda komai zai tafi dai-dai domin aiki ne da za su yi wa federal government kuma ba ƙaramin miliyoyi za su samu ba idan su ka yi aikin.

Wani lokacin Sir Najeeb a office ya ke kwana. Cikin kwana biyar har ramewa Farida ta ga Sir Najeeb ya yi. Yadda ta ga kowa na kaffa-kaffa da shi haka ya sa itama ta ke taka tsan-tsan da shi.

Yau monday aka shirya meeting a conference room na su, duk wani babban Engineer ko Architect da ke aiki a Najeeb constructions sai da ya hallara.

Bayan an playing mu su power point da ke ƙunshe da zannen da aka yi. Sannan Najeeb ya zo gaban wani table mai faɗi ya ce “Ladies and Gentlemen. Ga biggest project na mu na wannan shekara, project Alpha”

Lokacin da ya buɗe mayafin da aka rufe teburin da shi sai ga modelling ɗin ginin da za su yi. Har ta Farida da ba ta san komai akan aikin zane-zane da ƙere-ƙere ba sai da wannan modelling ya matuƙar burgeta.

Maganar Farida ta ranan ya tuno lokacin da ya ga Farida ta buɗe ido da baki tana ganin model ɗin.

Jawabin godiya ya fara bayan an gama kallo.

“Ina godiya wa team Alpha da su ka taimaka da bani ideas, wanda da su na yi amfani na fito da wannan zanen. Special thanks to Architect Anas, Architect Ifeanyi, Engineer Ɗayyabu, Engineer Mathew…” haka ya kira mutane goma da su ka yi aiki tare ya mu su godiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button