SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Sir Najeeb ni ma a gode min, na yi ta aikin zirga-zirgan kai saƙo da ƙarɓo saƙo ai” muryan Farida ya ƙaraɗe hall ɗin. Nan aka fara dariya. Najeeb kam kallon ” are you for real” yai wa Farida…
……..
Tana shirin fita daga gida ta ji shigowar alert a wayan ta. Ta ɗauko wayan ta duba dan ta san ba ƙarshen wata ba ne. Dubawan da za ta yi sai ga alert ɗin miliyan biyu da ga VESTAC.Inc……
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣2️⃣0️⃣
Tana zuwa office ta samu ana ta shirye-shiryen baƙin da za su zo. Ba ta yi maganar kuɗi da kowa ba dan dama Yakubu ta ke son tambaya ko ya san kamfanin VESTAC. Kafin ta tafi Bank ta bi bahasin wannan uban kuɗi da ba ta san ko ɓatan kai yai ya shigo account ɗin ta ba.
Ba ta ga Sir Najeeb ba, ta san shima yana chan yana ta shirye-shirye.
Sai ƙarfe tara da rabi Najeeb ya zo office. Wankan yau ma daban ta ke, ta san yana da kyau kuma ya iya wanka ba ƙarya sai dai yau wani extraordinary kyau ya ma ta na daban.
Minti goma da shigan sa office Anas ya zo ya wuce a bircike, ko amsa gaisuwan Farida bai yi ba.
Maganar da yaiwa Najeeb ne ya sa Najeeb ya tashi a hargitse yana faɗin What!
“Najeeb takardun zanen ba sa nan and the model is…”
Najeeb bai saurari ƙarshen ba ya fita da gudu.
Farida na zaune tana cin aya ɗanya da ta siya jiya ta ga Najeeb ya fito da gudu. Kasancewar ance Aya na sa ƙarin ni’ima ya sa ta lazimci cinsa ko kuma ta yi kunun aya ta sha tunda ta kusa shiga daga ciki.
Shima Anas bin bayan sa yai da gudun.
Yana tsaye gaban table ɗin yana kallon yadda aka faffasa model ɗin da ya sha wahala wajen haɗawa, and box ɗin da aka ajiye takardun zanen, shi ma empty ba komai a ciki.
Yana tsaye yana huci idon sa ya kaɗa yai ja hannun sa ya fara kakkarwa. Leɓensa na ƙasa ya ciza da ƙarfi amma still bakinsa bai bar rawa ba.
“Na sa an duba camera footage ɗin amma kuma tun jiya da rana baya aiki. It seems kamar an tampering na shi ne”
“Who is the last person to enter this place?” Ya faɗa cikin muryarsa mai fidda amo.
Anas yai shiru dan bai san ta yadda zai fara ma sa bayani ba.
“Who?” Ya sake faɗa da ƙarfi.
“Ba na tunanin za ta yi haka, CCTV footage ya nuna ta shiga ta duba model ɗin har ta ɗau hoton su sai ta fita daga nan kuma bai sake aiki ba”
“Who?” Ya faɗa wannan karan a hankali.
“Farida, your secretary”
Juyowa yai a hankali yana huci, yadda Anas ya ganshi sai da ya tsorata.
“Najeeb i’m sure ba ita ta faffasa abun nan ba, there’s explanation to this”
“Sir Najeeb baƙin sun iso” wani staff ya shigo ya faɗa.
Kawai sai Najeeb ya fashe da dariya, dariya sosai har da ƙyaƙyatawa.
“Najeeb fa za mu yi?”
Cikin dariya ya ce ” ya za mu yi? Hhhhhhhh. Dude she won, she succeeded. Abinda ta ke so kenan dama, to make me look stupid. Ka san mi ta yi ranan? Na san ta gaya ma ka ma, but let me tell you again. This crazy bitch puts superglue on my seat, and …and do you know what she said?”
Ya sake fashewa da dariya ” she said Tsuliyar CEO Najeeb Constructions a waje the bitch dare say that to my face. Yanzu na san mi ta ke nufi, she wants me to be humiliated, to look stupid”
“Najeeb plz calm down” Anas ya faɗa yana ƙoƙarin dafa abokin na sa.
“Calm down?”
“Za mu nuna mu su 3-D powerpoint ɗin sannan mu ba su haƙuri akan modelling ɗin sai gobe, then kafin goben….”
“If you are stupid i’m not Anas, we’ve lost this contract”
Ya mangaje Anas ya fita a wajen. Wajen baƙin ya je aka gaggaisa sama-sama. Anas na wajen yana tunanin mi Najeeb zai yi.
Kawai sai ya ce baƙin su biyoshi. Su na zuwa ya nuna mu su modelling ɗin da aka ɓata.
“I’m sorry but a bitch secretary i hired did this”
Nan su ka fara masifa ” this is unprofessional, Mr Jibo taya za ka bari mu zo tundaga Abuja only to see a destroyed work”
Anas ya shiga ba su haƙuri yana ƙoƙarin nuna mu su hoton zanen a Tab ɗin sa amma ba su saurare shi ba. “We are highly dissappointed in you Mr Jibo” babban cikin su ya faɗa sannan ya juya su ka tafi. Najeeb bai ce komai ba shi kuwa Anas bin bayan su yai yana ƙara ba su haƙuri amma ba su saurare shi ba…
Najeeb ya jima a ɗakin kafin ya fito, yadda ya ke tafiya kaɗai ka san yana cikin tsananin ɓacin rai.
Yana shiga office ɗin ta ya tadda Farida tana waya sai dariya ta ke.
Kallon tsana ya fara ma ta kafin daga baya ya nuna ta da ɗan yatsa ” i will revenge Miss Salihu, bit by bit”
Tunda ta ga yadda ya shigo fiskarsa ba alamun wasa ko kaɗan ta yi saurin kashe waya tana sauraron mi zai ce dan ta ɗan tsorata da yanayin sa.
“Ni kuma mi na yi” ta faɗa lokacin da faɗi kalmar ɗaukan fan sa.
Ba a jima ba Anas ya shigo.
“Najeeb mutanen nan sun tafi, we lost the project”
Najeeb bai kulashi ba ya ma rigingina kansa jikin kujera yana kallon sama ya ɗan juyawa a jikin kujera a hankali.
“Najeeb lets investigate this issue. Ina da yaƙiƙin ba Farida ba ne ta yi wannan aiki”
“She did it” Najeeb ya faɗa a hankali.
Kafin Anas ya fito Yakubu ya zo office ɗin Farida yana ba ta labarin abinda ya faru. Farida ta dafe ƙirji tana faɗin ” wayyo Allah, yanzu wahalan Sir Najeeb duk a banza”
“Farida mi ya sa ki ka shiga wajen nan?”
Ta ɗan rage murya ta ce ” ba dai kana tunanin ni na yi wannan aika-aikan ba”
“Farida camera ya nuna ke ce ki ka shiga wajen nan na ƙarshe and ke yanzu ake zargi”
“Na shiga uku wata sabuwar sharrin da za a min kenan. Ni fa abin ne ya min kyaun na je na ɗau hoton sa. Ga ma hotunan a wayana” ta ƙarisa maganar tana ƙoƙarin buɗo hotunan a wayarta.
Anas ya fito ya same su, the same tambaya ya ma ta akan miya sa za ta shiga ɗakin nan, amsar da ta bawa Yakubu shi ta bawa Anas.
Anas ya girgiza kai ya ce ” Farida akwai matsala fa, Najeeb yana zargin ki, kuma idan ba’a gano wanda yai wannan abin ba i’m sorry but abinda Najeeb zai iya mi ki ba zai tsaya a kora kaɗai ba”
“Wayyo ni Aisha, yanzu ba za a barni na rabu da Sir Najeeb lafiya ba”
Bayan sun bar office ɗin ta ta shiga office ɗin Najeeb, har lokacin yana zaune yana kallon sama.
“Sir Najeeb wallahi wallahi ban ruguza ma ka aikin ka ba, hoton abin kawai na ɗauka saboda ya birgeni” haka ta dinga zancen ta ita ɗaya ba tareda ya tanka ma ta ba, da ta gaji da kan ta ta fita daga office ɗin.
Wannan abu ya sa ta manta da batun miliyan biyu da ta gani a account ɗin ta da safe.
Zuwa rana duk Farida ta shiga damuwa, wannan ya shigo ya ma ta Allah wadai da halin ta wannan ya shigo yana son yi tsaigumi da gulma. Tun tana mu su masifa har ta gaji ta haƙura, idan mutum ya zo har ya tafi ba ta tanka ma sa. Ranan fa gaba ɗaya kamfanin ya rikice. Rashin samun wannan contract zai jawo mu su asara sannan sunan Kamfanin su zai samu mummunan shaida a gari da ƙasar ma gaba ɗaya.
Lokacin da aka tashi Farida da ƙyar ta tashi ta tafi bayan ta leƙa Sir Najeeb wanda har lokacin ke zaune a kujera.
“Sir na san inada rigima amma wallahi ba zan yi abinda na san zai janyo wa kamfanin ka asara ba, tunda na san dukkan mu nan muna ci a ƙarƙashin ka” abin da ta faɗa kenan lokacin da za ta fita.
Ko da ta je gida ka sa taɓuka abin kirki ta yi. Jira kawai ta ke Yakubu ya dawo ta ji mi ke faruwa. Sai dai Yakubu bai dawo ba har chan dare lokacin ita kuma ta yi bacci.
Washe gari da sanyin jiki ta shirya ta tafi wajen aiki.
Ta fara zuwa office ɗin Yakubu amma ba ya nan. Haka ta wuce office ɗin ta tana fargaban mi za ta tarar.