SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Daburcewa ta yi ta fara kame-kame.
“Get out” ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai.

Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani aiki da Joseph sabon sakatarin sa ya turo ma sa. Yana dubawa yana sipping tea ɗin sa a hankali. Ba laifi Joseph yai ƙoƙari, da alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba, sai dai da saura tunda dududu sati biyu da Joseph ɗin ya fara ma sa aiki kenan.

……………………..

A hankali soyayyar Rayyan da Aisha Farida ta fara nisa, domin har ya je Jos ya gaida Ummi…

“Farida ba magana na ke mi ki ba”

“Ummi dan Allah ki haƙura da wannan zancen, zan dai dinga zuwa mu su akai-akai yanzu tunda na gama bautar ƙasa”

“Kin sani sarai har yau Alhaji Musa ni yake ɗaurawa laifi akan na raba ki da dangin Baban ki. Sun fi ni iko da ke Farida”

“Ni kan Ummi ki yi haƙuri, ba zan je ba, albarkacin Inna na ke zuwa mu su dama, kuma ta rasu shikenan”

“Ki yi yadda ki ke so Farida” Ummi ta faɗi tareda barin ɗakin.

Ita ta rasa dalilin da zai sa sai yanzu Baffa Musa zai takura wai ta koma wajen sa da zama. Ita yaushe ma za ta juri zafin Kano balle uwa uba rashin kunyar yaran sa. Dama dalilin Inna ke kaita Kano kuma tunda ba ta nan kowa ya riƙe kan sa. Da wannan tunani ta janyo purse ɗin ta tana irga kuɗin da ke ciki a karo na biyar kenan tun safiyar yau.

Sosai Ummi ta nuna ɓacin ranta akan ƙin zuwa Kano da ta yi, ko gaisuwarta yau da safe ba ta amsa ba.

“Nanna dan Allah ki cewa Ummi ta bar ni na yi zamana anan. Wallahi ba jin daɗin zaman Kano na ke yi ba”

Nanna da ke shan kunu da ƙosai ta ce ” kin dai san da daɗewa Ummin ki tai alƙawarin za ki koma Kano da zaran kin gama makarantar ki. Alhaji Musa da kan shi ya kirata jiya ya ke cewa ya ji shiru. Ke idan ba ke bama ba saurayin ki ɗan Kano bane, idan ki ka je chan sai ku saita kan ku, kinga ba sai an sha wahala ba daga nan sai dai mu je bikin ki chan Kanon”

Ta turo baki tana faɗin “Allah dama kun gaji dani. Ni dai ba zan je Kano ba”

“Ah to, sai ki kira Baffan na ki ki gaya ma sa ai”

Farida ta zumbura ba ki ta fice a ɗakin….

Cikin kwana biyar ta gama shirin ta tsaf, ba wai tana son zuwa Kano bane, sai dai tunda abinda Ummi ke so kenan dole ta yi shi. Ranan asabat ta wuce Kanon tsabar haushi ko kiran Baffa Musan ba ta yi ba balle ta sanar ma sa da zuwan ta.
A ƙofar gida ta haɗu da su Kamal yaran Baffan su na wasa, da gudu su ka zo su ka tareta sannan su ka tayata ɗaukan kayan ta.

Da sallama ta shigo tana ƙarewa cikin gidan kallo wanda ya sha sabon fenti da alama dai saboda bikin Hajara da Salima da za a yi ne.
Baaba Sabuwa ta fara gani wanda ihun yara ya sa ta fito daga kitchen. Duk cikin matan Baffa Musa ita Farida ke ɗan gani da mutunci saboda itace uwargida kuma ba laifi tana da kirki.

“Oyoyo mutanen Jos. Sannu da zuwa”

Gyalenta ta saƙala ajikin igiyar shanya tana faɗin “fatan mun sameku lafiya”
“Lafiya lau, ya su Ummin na ku?”
Daga kitchen ta ke amsa ma ta da lafiya. Sai faman buɗe tukwane ta ke yi tana neman abin da za ta sa a baka.

“Baaba Sabuwa ni kam har yanzu ba ku bar baƙar al’adar ku ba, ace abincin rana sai ƙarfe uku”

“Lah yanzu na ke son ɗaurawa ai”

Farida ta dubi wayar ta tana faɗin ” a ƙarfe ɗayan!”…

Sai da dare Baffa ya sa aka kirata. A falon shi ta sameshi yana cin abincin dare. Bayan ya ma ta ya hanya sannan ya fara bayani ” Aminah ta ce ba ki fara aiki ba dan haka zan sa Yakubu ya nema mi ki aiki a kamfanin da ya ke aiki ko za a dace kema ki samu. Kafin nan kuma ki cewa yaron da ke neman ki ya turo saboda mu san da gaske ya ke yi. Kin dai ga yanzu shirin auren ƙannen ki a ke yi, zuwa ƙarshen shekara ke ma ayi na ki”

“Ni dama na san dalilin cewa in dawo Kano kenan, ni Baffa ban san mi na tare ma ka ba. Kanata wani ƙannena-ƙannena, na ga su suka ƙi karatu su ka ce aure za su yi. Ni dana zaɓi karatu na yi kuma na gama ai sai a bar ni na ɗan sha iska kafin a fara maganar aure na”

Ya ma ta daƙuwa ya ce “Uban ki Farida, na ce kin ci ƙaniyar ki. Wato har yanzu ba ki bar rashin kunyar ki ba ko” .

“To Baffa ina zaman zamana a Jos, ka takura Ummi wai ta turoni Kano. Duk abinda na yi ai kai ka ji za ka iya…”

Marfin kwanon silver ya wurga ma ta ta kauce ba shiri. ” ki kiyaye ni Farida wallahi zan mummunan saɓa mi ki. Tashi ki bani ware! Ja’ira kawai”

Sum-sum ta tashi ta fice a falon dan ta san ƙarshe zai iya marin ta ko ma ya daketa. Dan Baffa Musa akwai saurin hannu.

……………………..

Ba ƙaramin kyau yai ba cikin shirin sa na riga da wando baƙi sai kuma blazer kalar navy blue. Ɗauke da briefcase ɗin sa ya sauko daga stairs ɗin cikin takunsa na girma da ƙasaita.
Ƙai tsaye wajen dining ya je inda iyalen gidan ke cin abinci. Ya sunkuya yaiwa wata budurwa peck a kumatu yana faɗin ” good morning baby”

“Morning Big B” ta amsa tana ma sa murmushi

Itama Afrah da ke gefe ta ce ” Good morning Yaya”
“Morning” ya faɗa a taƙaice.

Tea ɗin da ke gaban Baby ya ɗan ƙurɓa ya ce ” sai na dawo ko”

Wata haɗaɗɗiyar mata da ke zaune opposite da Baby wanda tun saukowar shi idon ta ke kan sa ta ce “have breakfast with us, please”
A dararance ya kalleta ya ce “na gode Justice Nabilah”
Har ya bar falon ba ta dena kallon sa ba, zuciyar ta na ƙuna. Sai yaushe ne ɗan ta zai kira ta da sunan uwa? Sai yaushe alaƙar su zai dawo dai-dai kamar kowace uwa da ɗan ta? Shekaru sun ja amma har yau babu wata chanji tsakanin su.

Baby ta ce”Sorry Mom”
Justice Nabilah ta girgiza kai ta ce ” kar ki damu Najdah” ta ƙaƙaro murmushin dole dan jaddada maganar da ta yi.
Ita dai Najdah jikin ta ne yai sanyi, har yau ta kasa gano dalilin ƙiyayyar Yaya Najeeb da Mom, wanda tun tasowar ta haka ta same su.
Tambayar duniyar nan ta yiwa Big B da Mom amma duka babu wanda ya bata gamsashshiyar amsa. Harta Daddy bai san dalilin wannan gabar ba. Tun yana faɗa akan wannan ƙiyayyar ta su har ya haƙura ya zuba mu su ido…

Tunda ya fita daga gidan kai tsaye wajen motar sa ya wuce. Wanda tuni aka fito ma sa da ita daga parking lot. Sau ɗari zai ɗau driver sau ɗari zai koresu. Shi ya sa yanzu kusan wata uku kenan rabon da ya sake ɗaukan driver. Shi ya ke tuƙa kan sa, ran da yake son yin aiki a cikin mota kafin ya ƙarasa office to zai sa drivern Daddy ya kai shi office.

Najeeb Adam Jibo

matashin da ya ke ji da kyau,kuɗi,ilimi da kuma gata. Ɗa namiji guda ga tsohon Ambassador kuma Professor Adam Jibo da Justice Nabilah Al-Jabir.

Adam Usman Jibo ɗan asalin ƙaramar hukumar Kumo ne da ke jahar Gombe, sai dai kasancewar tun rasuwan mahaifinshi ya dawo wajen ƙanin Baban sa da ke Kano da zama ya saka zamansa ya koma Kano. Alhaji Mustafah Jibo babban ɗan kasuwa ne da ya ke da arziƙo tun a wancan lokacin.

lokacin da Adam ke da shekara bakwai a duniya mahaifin sa ya rasu, dan haka zaman sa da shi da ƙannen sa mata biyu su ka dawo hannun Alhaji Mustafah , lokacin Mustafah da matar sa shekarar su takwas da aure amma basu taɓa haihuwa ba. Sun riƙe Adam da ƙannen sa Ruƙayya da Fatima tamkar ‘ya’yan da su ka haifa. Sai da su ka shekara goma sha biyar da aure ba haihuwa sannan Hajiya Mama wanda haka su Adam ke kiranta ta dage akan lallai Alhaji Mustafah ya ƙara aure ko za a dace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button