SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Get out, get the hell out of here”

Anas dai ya fita ne amma zuciyar sa ta gama amincewa da Najeeb na son Farida. Its so obvious all this while bai gane ba…

“Wai wani irin magani ki ka yiwa Najeeb ne? Duk abinda ki ka yi sai ya shanye. Gaya min wani malamin ki ka riƙe?”

Takaici ma ya sa Farida ba ta tanka ma ta ba.

“Farida da ke na ke magana”

Wannan karan ba za ta ɗauki cin fuska daga wajen Khalidah ba.

“A wajen uwar ki na ke karɓan magani. Ki fita min a office kafin ki ga rashin mutunci”

“Its not over yet Farida” ta snapping a dai dai fiskarta sannan ta fita.

“Kai ya Allah daga wannan sai wannan. Ni da na san wannan cin fuskan zan fiskan ta a wannan kamfani da tun farko da Sir Najeeb ya koreni na tattara koli na na tafi”

Ba ta idda zancen zuci ba wayar ta ta fara ƙara.

Tana ɗauka ya ce ” to my office”

Saɓanin ɗazu da ta ganshi a wancan hall ɗin yanzu fiskar sa ta sauya akwai ɗan fara’a a tattare da shi.

“Ki fixing meeting da team Alpha anjima”

“Sir Najeeb ba abinda za ka gayamin, ba za ka tambayeni gameda gaskiyar lamari ba”

“Miss Salihu, ba yau na fara gaya mi ki ba. Our relationship is strictly professional, anyi investigation kuma an sameki da laifi, kuma an hukunta ki. What else do you want me to say?”

“Sir Najeeb ko da na cigaba da aiki anan, daraja na ta zube, mutunci na ya zube”

“Wanni daraja ki ke da shi dama? You are just a secretary, my secretary”

“Shikenan tunda abinda ka ce kenan. Amma duk min daren daɗewa gaskiya za ta fito kuma da kai da sauran ma’aikatan na ka duk sai kun ji kunya”

…………….

Wata ɗaya kenan da ya wuce. Aiki a Najeeb constructions ya zamewa Farida sabuwa, zuwa kawai ta ke amma ba ta jin aikin a ranta. Ko da Anas ya ce ma ta Sir Najeeb ya biya ma ta kuɗin ba ta ma sa godiya ba. Ta so ajiye aikin amma sai ta yi tunanin idan ta bari to wanda basu yarda akwai hannunta a abinda ya faru ba ma za su yarda, shiyasa ta cigaba da zuwa. Dama niyyarta da zaran saura wata ɗaya auren ta za ta je ta rubuta takardar barin aiki.
Sir Najeeb bai chanja ma ta ba, yadda ya ke da ɗin haka ya ke, wani lokaci yai ihu yai faɗa wani lokaci kuma yai magana a hankali. Saɓanin da da ta ke maida ma sa magana yanzu kam ko mi zai ce ba ta kulashi.
Ta koma ba ruwan ta da kowa aikinta kawai. Ko sallah a office ɗin ta ta ke, balle wajen cin abinci kam ta dena zuwa…

“Sir ga resignation letter ɗi na” ta faɗi lokacin da ta ajiye ma sa takardar a gaban sa.

“Ok” iya abinda ya faɗa kenan ko ɗagowa bai yi ba balle ya kalli idon ta.
Ta yi mamaki dan Najeeb ɗin da ta sani da ba zai yi shiru ba.

“Allah ya sada mu da alkhairi Sir Najeeb. Na gode da taimako da kulawar ka”

Cikin zuciyar sa ya amsa da amin.

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣2️⃣2️⃣

Waɗanda ta ke mutunci da su kawai ta je ta yiwa sallama. Lokacin tashi yai ta haɗa yanata-yanata ta tattara office ɗin,ta ɗauko office laptop da Najeeb ya ba ta dawo ma sa da shi.

“Sir Najeeb zan tafi, ka yafeni dan Allah, na san a zaman da mu ka yi na yi laifuffuka dayawa amma ka yi haƙuri. Allah ya yafemu gaba ɗaya”

Shiru ne ya ratsa office ɗin na lokaci mai tsawo. Tun tana ganin Sir Najeeb zai buɗe baki yai magana har ta cire rai ta fita daga office ɗin.

Sai da ta fita daga office ɗin sannan ya ɗago idon sa ya ce ” i’m not done with you yet Miss Salihu”….

Office ɗin Anas ta je dan ta ma sa sallamar ƙarshe.

“Yanzu ƙanwata shikenan kin bar aiki da mu?”

“Yaya na ai ana tare ko da bana aiki anan”

“Gaskiya ban ji daɗi ba, yanzu idan ki ka tafi wa za mu samo ya replacing ɗin ki. Ke ce the second longest surviving secretary a wajen Najeeb”

“Ya Anas kenan, ai da ƙyar mu ka sha mu ɗin ma”

” ba wani, da ƙyar dai Najeeb ya sha a wajen ki”

Dariya ta yi sannan ta ce ” ya Amaryar ta mu?”

“Tana nan sai rigima”

“Ta kaini rigima”

Anas ya zaro ido yana dariya “ai Farida idan ta kai ki rigima bulaguro zan yi a garin. Irin ki ai sai su Najeeb”

“Hmm Ya Anas kenan. Nikam ina abokin adawar ka? Ko ya janye ne?”

“Ai tunda Daddy ya sa min stamp na yaƙice shi. Ga shi dama gimbiyar wannan ɗan baƙin kaɗai ta ke gani”

“Allah ya kaimu lokacin biki Yaya na”

“Amin ƙanwata, kar a manta da IV ɗin mu fa”

“Ai kune ƙarɓan fari”…..

……………….

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro saura sati uku aure aka kawo lefen Farida kuma gaskiya Rayyan ya yi ƙoƙari sosai.
Farida ta duƙufa da gyaran jiki da shirye-shiryen yadda biki zai kasance.

Yau ana saura kwana goma sha takwas aure, Baffa Musa ya kirata.

“Wani shirme na ke ji za ki yi ranan Alhamis?”

“Baffa friends day za ayi ranan Alhamis tunda ka hana ayi kamu”

“Enemies day za ki yi ba friends day ba. Yanzu ke Farida ba za ki yiwa kan ki faɗa ba. Ayi miki walima salamun alaikum a kaiki ɗakin ki hankali kwance, sai kin bijiro da wani shirme”

“Baffa a cikin gidan nan fa za’ayi kuma iya mata ne ka san inada jama’a”

“Ungo na ki ke da jama’an na ki”

“Mun gode Baffa”

Taɓe baki yai kawai yana bin ta da kallo. Bakin tan nan yana fata ya zaunar da ita lafiya a gidan ta, ba ya kawo fitina ba.

“Baffa ina ka amince?”

“Ya na iya uwata. Allah ya kaimu lokacin ya kuma kaɗe fitina”

“Baffa thank you” ta faɗa tana tashi da sauri…

…………….

Duk yadda ta ke ji gameda auren sai da auren ya zama saura sati ɗaya sai jikinta yai sanyi. Haka kawai sai tsoro ya shigeta gani ta ke kamar za a kuma wani chakwakiyar kamar yadda aka yi lokacin Lukman. Ummi ta zo amma su Nanna sai Alhamis za su shigo. Ranan talata da safe ta wuce Najeeb constructions. Ta fara biya wa office ɗin Sister Munibat ta ba ta katin gayyata tareda cewa idan ba ta zo ba to sun ɓata.

“Sister Aisha kenan, ai indai ina da rai da lafiya to bikin ki da mu za ayi”

Farida ta ɗan harareta ” kaman da gaske, kin sayi ashobe na kuwa?”

Sister Munibat ta fara sosa kai.

” hmmm ai dama na sani, Dan Allah ki daure ki zo”

“Insha Allah sister Aisha zan zo”

Daga wajen Sister Munibat ta wuce wajen Anas. Ta jima a wajen sa, inda ya ke ba ta labarin sakataren da aka ɗauka bayan ta tafi.

“Farida kwanan sa huɗu ya ajiye aiki, wai ba zai iya ba”

“Ai Sir Najeeb idan ba jan wuya ba ba mai iyawa da shi”

“Jan wuya kamar ki ba”

“I’in ai mun sha fama da shi”……

Lokacin da ta shiga office ɗin sa yana jikin shelf ya na neman wasu files. Ta tsaya tana kallon yadda ya ke ta dibi-dibi a wajen. Da ta na nan yanzu da ita ke wannan aiki.

“Sir Najeeb mai ka ke nema?” Muryan da bai yi zatan jin sa ba ya ji a ta bayan sa. Bai san lokacin da ya sake file ɗin ya faɗo ba. Tsayawa yai yana kallonta, ta wani yi haske tana sheƙi, ga wani ƙanshi mai daɗi da jikinta ke fitarwa.
Tsugunnawa ta yi ta ɗauka file ɗin sannan ta miƙa ma sa. “Ga shi na ma ka aikin ƙarshe”
Bai amsa file ɗin ba sai ma juyawa da yai ya je ya zauna a kujerar sa.

“Iko sai Lillahi, daga ganin Sarkin Fawa sai miya ta yi zaƙi. Sir Najeeb ba fa aiki na zo ba da za ka min jan ajin da ka saba”

“Oh really”

“Gashi, dama IV na kawo ma ka” ta yi saurin ajiye file ɗin tareda ciro IV ta ajiye ma sa.

“Dan Allah a daure a zo. Duk da ma dai i’m just a secretary”

Ta ɗan yi dariya ta ce ” was just a secretary”

“Congratulations Miss Salihu”

“Thank you Sir Najeeb”

Ya ɗan kurɓi coffee da ke gaban sa sannan ya ci gaba da latsa laptop.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button