SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Sir Najeeb ina da magana. Dan Allah ka ɗan rage halin kan nan. Ka ga ba kowa bane zai iya jurewa. Ni ma da ƙyar na sha a wajen ka. Allah, watarana idan na koma gida daga office har ƙaramin zazzaɓi na ke saboda stress da zafin kai. Kai ba a maka gwanin ta sannan…”

“Out”

“Ka ga irin halin na ka ko”

“Miss Salihu get out”

Ta yi shiru tana kallon sa sai da ta ga zai sake ɗaukan mug ɗin coffee ɗin sannan ta yi wuff ta ɗauke.
Ta kai baki da nufin ta kurɓe duka lokaci guda sai ta ji shi da zafi sosai. Ta ɗan kurɓi kaɗan ta sake kurɓa sannan ta ajiye ma sa.
Dariya ta yi saboda yadda ta ga ya zaro ido.

“Sir Najeeb tsokalar ƙarshe ne fa. Na tafi”

Harta juya sai kuma ta juyo ta ce “Sir Najeeb a yafe mu”…
Sai da ta rufe ƙofa ya ce “devil in a dress” ya jawo wani dogon envelop ya buɗe, hotuna ne guda uku a ciki ” happy never marriage Miss Salihu” ya faɗa a fili.

(????Sir Najeeb ya dai?)

…………………..

Farida na komawa gida ta tarar da Maijiddah ta zo.

“Kai-kai Jiddah mi ki ke ci haka? Kin ganki kuwa”

“Kai Anty Farida”

“Zo zo mu shiga ɗaki ki gaya min sirrin”

Sai da su ka zauna ta ce ” Jidddah ciki gareki, wannan ƙiban da walakin”

Maijiddah ta rufe ido tana murmushi.

“Masha Allah, Allah ya raba lafiya. Ina kishiyar ki? Har yanzu tana Abuja?”

“E, amma yanzu sau biyu ta ke zuwa a wata”

” ‘yar kusun’wa, za ta ma ajiye aikin ta dawo gidan ta, ko kuma ta ji ta a silencer dan mune ma su gidan yanzu”

“Na gode Anty. Kayan da ki ka bani sun min rana”

“Zauna a wajen, ai mazan yanzu sai da shigar bariki. Nima na je Jos na kwaso nawa suna nan jingim”….

Biki na matsowa jikin Farida na ƙara sanyi kullun ta yi bacci sai ta yi mafarkin an fasa aurenta. Abin ya dameta ta gayawa Ummi, Ummi ta ce ta dinga addu’a. Itama ɗin Ummin Allah-Allah ta ke ayi bikin lafiya ba tareda wata matsala ba.
Ranan Alhamis aka je aka yiwa Farida jere a gidan Rayyan. Rayyan ya gina 3-bedroom flat mai kyau. Baffa yai ƙoƙari dan ya kashe kuɗi sosai wajen sayen ma ta kaya, ‘yan uwan Ummi ma sun yi ƙoƙari gaskiya…

……….. ……….

Ya na zuwa ƙofar gidan ya sa yaro ya kira ma sa maigidan. Da yaron ya fito ya ce yana zuwa…

Musabaha su ka yi da dattijon sannan su ka gaisa.

“Yi haƙuri ban ganeka ba”

Ya miƙa masa envelop sannan ya ce ” ɗan ka zai yi aure ranan Asabat ɗin nan ko?”

“Insha Allahu”

“Matar da zai aura ba matar aure ba ce”

“Ban gane ba”

“Ka dubi cikin envelop ɗin nan za ka ga zahiri” daga haka ya juya ya tafi.

…………………

Anyi friends day lafiya kuma ba laifi ƙawayen ta na Jos sun zozzo, anci an sha kuma an girgije.

Ƙarfe goma sha ɗaya na dare lokacin ba ta fi ‘yan mituna kaɗan da kwantawa ba kiran Rayyan ya tashe ta. Tana ɗauka ya ce ta fito waje yana ƙofan gidan su.

“My Ray lafiya ka zo da daddaren nan?”

“Ki fito Farida akwai saƙon da zan ba ki ne”

Maganar saƙo da ya ce sai ta ji zuciyar ta ya buga. Ta tashi ta sa hijabi ta fito.
Akwai wa su baƙi da ke kwance a barandar tsakar gidan su na hira, da ke ba su jima da tattara tsakar gidan ba.

“Amarya ina zuwa haka?”

“Ƙofar gida zan je an kawo min saƙo”

“Samarin zamani dai, angon ne ya ka sa hakuri haka”

Ita dai ba ta sauraresu ba ta fita.

Wajen motar sa ta je ya buɗe ta shiga.

“My Ray minene, hankalina ya mugun tashi fa”

Da ke dare ne ba iya kallon fiskarsa ta yi sosai ba balle ta ga yanayin sa.

“Farida ashe za ki iya cin amana ta”

Dum ta ji ƙirjin ta ya yi.

“Wallahi ban ɗauka za ki min haka ba”

“Na shiga uku ni Farida ba dai za a kuma ba. Rayyan mi na yi?”

“Ashe soyayya ku ke da Ogan ki. Ashe duk yadda ki ke zagin sa a gabana iya fatar baki ta tsaya”

“Rayyan dan Allah kar ka sa zuciyata ta buga yanzu. Idan ma wasa ka ke ka dena please “

“Da kan sa ya je gida ya ce wa Baba ke karuwarsa ce”

“Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji’oun, Lahaula wala ƙuwwata illa billah. Sir Najeeb ne ya faɗi hakan?”

Miƙa ma ta wayarsa yai ya ce ga hotunan da ya kawo. Ina tunanin ma waɗannan lokacin da ku ka je Lagos tarene ku ka yi holewarku achan.
Ta amshi wayar ta fara kallon hotunan. Hoton farko tana zaune kan cinyar Najeeb ta sa hannayen ta a kafaɗun sa tana murmushi, ɗaya kuma suna tsaye ya rungumeta ta baya, lips ɗin sa a daidai wuyan ta. Ta swipping na gaba wanda tana kallo hawaye na ɗiga a jikin wayar. Suna rungume da juna bakinsu a haɗe kamar suna kissing.

“Ba ni bane, wallahi ba ni bane. Wannan sharri ne. Rayyan ka yarda da ni”

“Dama na zo na faɗa miki ne da kaina kafin gobe a zo gida a faɗa. Na fasa auren ki Farida, ina son ki amma ba zan iya auren ki ba. Najeeb yana da kyau yana da kuɗi, ko bayan mun yi aure idan ya neme ki za ki amince da shi. Ba zan iya aure da zargi a ciki ba”

Bakin ta ne ya fara rawa, tana so ta yi magana amma ko me ya taho zai fito sai ya maƙale a wuyan ta. “Na fasa auren ki Farida” shine maganar da ke ta maimaituwa a ƙwaƙwalwarta.

“Gobe za su zo su karɓi sadaki da lefe, sauran abubuwan na yafe. Na gode da Allah ya tona asirin ki kafin ma ayi auren, dama Umma ta sha faɗamin ba ta yarda da ke ba dan ‘yan Jos ɗin nan yawancin ku ‘yan iska ne”…

Ba ta san ya akayi ta buɗe ƙofa ba, ba ta san kuma ya akayi ta shiga gida ba. Zuwa ta yi ta zauna a bakin gado hawayen da ta ke yi ma ya tsaya. So take ta gane mafarki ta ke yi ko gaske ne. Bacci kam ranan ba bu shi a idon Farida.

Washe gari da safe aka tashi da shirye-shiryen walima. Farida ta kasa magana ta kasa faɗan abinda ya faru jiya, ita har lokacin gani ta ke mummunan mafarki ta yi jiya da dare.

Zuwa ƙarfe goma sai ga Baffa ya shigo yana faɗace-faɗace. Kiran Ummi da Nanna da Baaba Sabuwa yai zuwa falon sa. The next thing da akaji sai kukan Ummi. ‘Yan gulma su ka yi falon da sauri Baffa musa ya fatattake su.

“Amina ki dena kuka, ni ban yarda da abin da su ka ce ba, kuma koma hakanne dole sai na aurar da ‘ya ta gobe. Ba zai yiwu a fasa aurenta har sau biyu ba, sai duniya ta zageni. Ni nawa ‘ya’yan ina aurar da su lafiya ita kuma da ta ke amana gareni ake samun matsala duk lokacin bikin ta”

Nanna da ita kaɗai ce ba ta fara kuka ba ta ce “yanzu wa za ta aura?”

“Yakubu, Yakubu zai aureta, ku cigaba da shirye-shirye Allah ya kaimu goben”…

Farida na ɗaki har lokacin tana zaune jugum, Maijiddah ta yi tambayar duniyar nan amma ba ta kulata ba.

Ummi ta shigo ɗakin tana hawaye. Zuwa ta yi ta tsugunna gaban Farida ta ce “faɗa min gaskiya Farida, akwai abinda ke tsakanin ki da Ogan ki?”

Farida ta kalli Ummi da rinannun idanuwan ta ta ce “da gaske ne ko? Da gaske Rayyan ya fasa aurena?. Ummi banida sa’a a rayuwa kenan? Ummi ina son na yi aure, ina son na samu gidan kai na, ina so na haihu na tara ‘ya’ya, ina so na samu ladan biyayyar aure, ina so na cika miki burin ki Ummi. Ummi ko dai aure ba ya cikin ƙaddara ta ne?”

Ummi ka sa magana ta yi sai kuka…..

Zuwa ƙarfe shabiyu ‘yan gidan su Rayyan su ka zo karɓan kaya. Daga wajen ma su ke cewa aje a kwashe tarkacen da aka jera a gidan ɗan su. Abubuwa dai su ka rinchaɓe a wajen.

Kowa a gidan da abinda ke ran sa, wassu baƙin na shirin komawa amma da su ka ji Baaba Sabuwa ta ce aure ba fashi za ayi, sai su ka tsaya dan su ga ƙarshen Farida.

Farida tun safe ko sau ɗaya ba ta fito a ɗaki ba, ko wanka ba ta iya yi ba balle abinci kam ba a zancen sa.
Da yamma Yakubu ya dawo daga wajen aiki sai a lokacin ya ke jin labarin abinda ke faruwa. Baaba Sabuwa ce ta ma sa maganar auren Farida da ya koma kan sa. Duk da bai shirya aure yanzu ba sannan bai taɓa kawo auren Farida a ransa ba amma indai dan ya cececi mutuncin ‘yar uwar sa ne to zai aureta da gudu ma. Abinda ya ƙara ɗaure ma sa kai baifi yadda aka ce wai ‘yan gidan su Rayyan sun ce wai FARIDA karuwar Ogan ta ba ne. Ya san Farida kuma ya san Sir Najeeb, ko da dai chan ƙasar zuciyar sa yana zargin Sir Najeeb na son Farida amma bai kai har ace wai suna neman junan su ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button