SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Yana cikin wannan tunanin ya ji wayar sa na ringing. Yana dubawa ya ga Farida ai da sauri ga ɗauki kiran.

“Dan Allah Yakubu ka sameni a ƙofar gida”

Da sauri ya tashi ya fita.
Lokacin da ya ganta wani tausayinta ne ya kuma shigan sa. Lokaci guda Farida ta chanja ta zama wata iri, fiskanta ya kumbura ga idon ta da su ka ƙanƙance saboda kuka. Tunowa yai da shekara uku da su ka wuce exactly haka ta lalace lokacin da aka raba aurenta da Lukman. Gara lokacin da sauƙi tunda matsalar daga Lukman ne to yanzu fa.

Ya ƙarasa wajenta yana faɗin “Farida dan Allah ki yi haƙuri, ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce”

“Ka kaini gidan su Sir Najeeb” abinda ta faɗa kenan cikin muryarta da baya fitowa sosai saboda dashewa da yai…

Adama ce ta buɗe ƙofa lokacin da ta danna doorbell ɗin.
“Daddy na nan?”

“Eh ki shigo”

A tsaye ƙiƙam ta tsaya idon ta na kallon ƙasa, kan ta ke sarawa, duk yadda ta ɗaga kan sai ta ji wani raɗaɗi.

Mom ce ta fara saukowa ganin yadda Farida ta ke ya sa tasan yarinyar na cikin damuwa.

” ‘yan mata ki zauna mana” ta faɗa da Hausanta da bai gama nuna ba.

Farida ba ta ce komai ba sannan ba ta zauna ɗin ba. Kitchen Mom ta wuce ganin Farida ba ta cikin hayyacinta.

Minti huɗu sai ga Daddy ya sauko.

“Ina wuni Daddy” ta faɗa da disashshiyar muryarta.

“A’a Aisha Amarya?”

“Na’am Daddy”

“Lafiya dai ko?, shekaranjiya Baban ki ya kawo min katin biki, ina ce ba wata matsala ba ne ta taso ?”

“Daddy kai uba ne na gari amma ɗan ka bai ɗauko hali na gari ba. Najeeb ya min sharri, ya raba ni da farin ciki na. Ya sa min tabo a rayuwata wanda ban san ranan da wannan tabo zai gogu ba. Ni marainiya ce, ba ni da gatan da ya wuce Allah, kuma na haɗa Najeeb da Allah. A kamfanin sa ban tsira ba, na bar aiki da shi ma ban tsira ba. Allah zai saka min” ta fashe da kuka ta fice daga gidan da gudu. Daddy yana kiran ta amma ba ta tsaya ba. Daddy kan shi ya ɗaure dan bai gane ina maganganun Farida su ka dosa ba.

Tana fitowa ta tsaya ta goge hawaye sannan ta fara tafiya duk da kuwa ba ta da ƙwari a jikinta. Ta kusa isowa wajen Yakubu da ke jiran ta jiri ya ɗebeta ta faɗi ta suma. Yakubu ya yiwo kan ta da gudu…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣2️⃣3️⃣

Maigadi da dreba da su ke zaune a benchi su ka taso da gudu.
Ce ma sa su ka yi ya kai ta mota yayinda Iliya dreba yai sauri ya shiga gidan don ya faɗawa Daddy.
Daddy na falo har lokacin yana waya da Anas.

Ya na ma sa bayani Daddy ya ce muje-muje.

Daddy na gaba Yakubu na baya ɗauke da Farida wanda har lokacin ba ta farfaɗo ba duk da kuwa sun yayyafa ma ta ruwa. Kafin su isa asibitin ta farfaɗo amma ba ta san inda ta ke ba….

Chan gida kuma Baffa ne ya ke ta faɗa kan miyasa za’a bar Farida ta fita a wannan halin. Maijiddah ne ta ce tare su ka fita da Yakubu. Sai a sannan yai shiru ya zaro wayar sa a aljihu ya fara kiran numbar Yakubun amma bai ɗauka ba.

“Shima ɗan gatan’wa, ko ina ya shiga oho”…

Ruwa aka ɗaura ma ta aka ma ta alluran bacci dan sun ce jinin ta ne ya hau. Sai da ta fara bacci tukunna Yakubu ya samu damar kiran gida ya faɗa mu su.

Daddy ya dubi Yakubu ya ce ” mi ya ke faruwa ne? mi Najeeb ya ma ta?”

Da kaman ba zai faɗa ma sa ba,sai dai girman Daddy da kwarjininsa ya fi gaban ya ƙi ma sa magana. Duk abinda ake ciki ya tsirge mi shi tundaga farko har ƙarshe.

Da ya gama bashi labarin Daddy ya ɗauko waya ya kira wata number.

“Anas ka na ina ne?”

Yakubu bai ji mi ake ciki ba ya dai ji ya ce “muna room 18 a sama”

Ba’a jima ba sai ga Anas ya shigo. Ganin Farida a kwance ya sa shi mamakin mi ya faru.

“Yakubu ya jikinta?, mi ya sameta?”

Da sauƙi kawai Yakubu ya iya ce masa.

“Ina ɗan banzan nan ya ke?”

Daddy ya tambayi Anas.

Ya gane Najeeb ya ke nema dan haka yai saurin cewa yana office nima daga office ɗin na ke.

“Har da kai ake rusa rayuwar mutane ko?”

Anas ya zaro ido ya ce “A’a Daddy”

Daddy ya miƙe ya ce “Yakubu Allah ya bata lafiya, ina nan dawowa anjima”

Yana Fita daga ɗakin Anas ga bi bayanshi da sauri.
A motan Anas ɗin su ka wuce Najeeb constructions.

Ya jima yana tunanin ko wani hali ta ke ciki. Wani ɓangare na zuciyar sa na faɗa ma sa bai kyauta ba wani ɓangaren na nuna ma sa ya yi dai-dai.
“She deserve it” ya furta a fili.
Yana ƙoƙarin duba wasu takardu da aka submitting ma sa tun da safe amma ya kasa fahimtar komai. Haka kawai zuciyar sa ke ma sa ƙunci….

A hanya Daddy ke sanar da Anas abinda Najeeb yai, Anas ya kaman salati yana salallami.

“Daddy ban san Najeeb zai iya yin haka ba especially saboda zargin da na ke masa akan yana son Faridan”

“Dan uban sa dan yana son ta sai ya mata sharri”

Anas dai shiru yai yayinda Daddy ke ta surfa ma sa masifa kaman wanda shi yai laifin.

Da ke an riga an tashi wajen shiru ka ke ji. Daddy da Anas su ka haura third floor.

Ya kifa kan sa akan kujera saboda wani zazzaɓi da ya rufeshi lokaci guda, ya rasa mi ya sa shi shiga wannan yanayi. He supposed to be happy ya rama kaɗan daga cikin asaran da Miss Salihu ta sa ya yi. But instead his sad.

Buɗe ƙofar office na shi da aka yi ya sa ya ɗago kan sa da sauri.
Ganin Daddy da Anas sai ya miƙe. “Dad ” kaɗai ya iya faɗa kafin saukan mari ya sa ya haɗiye koma mi ya ke shirin faɗa.
A karo na biyu Daddy ya kuma marin sa, ji ka ke taas. Anas na gefe ya sha jinin jikin sa dan faɗan uba da ɗa sai Allah.

“I’m ashamed to call you my son”

“Dad” Najeeb ya faɗa a hankali

“Ashe tarin shekarun ne kawai akan ka ba hankali. Mahaukacin banza Mahaumacin wofi. Sai ka samu me idan ka hanata auren? Tukunna ma, miye dalilin yi ma ta sharri? Miye dalili? “

“she deserve it Dad, she wanted to ruin me. Na rasa big contract saboda ita saboda haka 2 project da mu ka fara su ka soke contract da mu. She tarnished my image and the repeatition of my company”

Wani marin Daddy ya kai ma sa. ” i didnt know i have a monster son. Asaran kamfaninka yana dai-dai da ruguza mutuncin mutum kenan?. Shin ka yi tunanin halin da yarinyar nan za ta shiga? What if she died of shock, sai ka haɗa party kana murna ko”

Ya nuna shi da ɗan yatsa yace ” Anas, kalli banzan yaron nan fa,8yrs ago da Sabreena ta gudu ta barshi kafin auren su he almost died, he was depressed for months. Ya je theraphy section na watanni huɗu kafin daga baya ya warke ya dawo Nigeria. Do you know that this fool here yana shan antidepressant drugs har yau saboda baƙin cikin yarinyar nan. Amma shi ne ya ke da guts da zai je ya hana auren ‘yar mutane”

“Najeeb” ya ka sa magana ma saboda baƙinciki da ya tokare ma sa wuya.
Daddy juyawa yai ya fita, Anas ya kalli Najeeb, kallon ka bani mamaki sannan ya bi bayan Daddy da sauri.

Gidan su Rayyan Daddy ya ce Anas ya kai shi. Da su ka je su ka sa a yi sallama da Baban Rayyan ɗin, aka ce mu su yana kasuwa. Numbar sa su ka karɓa su ka kirashi jin sunan Alhaji Adam Jibo ne ya sa mahaifin Rayyan ya ce yana nan zuwa. Haka su ka zauna zaman jiran sa, kafin ya dawo ma an fara kiran sallan maghrib su ka yi sallah a masallacin anguwar.
A ƙofar gidan aka shimfiɗa mu su tabarma lokacin da Baban Rayyan ya zo.

Daddy bai ɓata lokaci ba ya ma sa bayanin ko shi waye da kuma abinda ya ke tafe da su.

“Malam Abdullahi, wannan hoto da aka kawo muku ba tare su ka ɗauka ba, editting na shi aka yi, kasan yanzu fasahar zamani ba abinda ba ayi. Wannan yarinya ta na da tarbiya kuma kowa ya shaideta da haka. Duk abinda Najeeb ya zo ya faɗa muku to wallahi ƙarya ne, ya yi hakan ne dan ya cimma wani banzan burinsa. Ku yi haƙuri a maida maganar auren yaron ku da Aisha”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button