SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Wait, Farida za ta dawo nan?”
“She has no choice”
“Ka san mi ka ke faɗa kuwa? Yanzu fa Farida matar ka ce”
“So what?”
“Wallahi ba ka ma ta adalci ba Najeeb. Ita da ya kamata ya zama tana zaune a gida, ana treating na ta kamar queen, sai ka kawota nan, nan ɗin ma a matsayin secretary”
“Ba na buƙatar shawaran ka, hold it to yourself”
“Amma Daddy ya sani?”
“Anas ba ruwan ka da al’amarin rayuwata. Dont meddle with my family affairs”
Anas ya sa dariya ya ce “sannu Mr Family man”
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣2️⃣5️⃣
Bayan fitan Anas da jimawa sai ga Khalidah fuuuu ta shigo office kamar wadda aka korota.
“Najeeb why?, why her?”
“Excuse me”
“Najeeb all this while da na ke zuwa wannan wajen ka ɗauka dan kuɗi na ke zuwa, ko an gaya ma ka ina son aikin wahala ne. Saboda kai na ke aiki a nan. Only for you”
“So?”
” Najeeb ka rasa wadda ta dace da kai sai Farida, miye ta ke da shi”
“Idan kin gaji da aiki za ki iya forwarding resignation letter ɗin ki, zan yi farin ciki da ƙarɓan sa”
“Najeeb dan Allah ka fahimce ni, Ina son ka, ina son ka fiye da yadda ka ke tsammani”
“Get out”
“Najeeb please”
“Out”
…………………..
Bayan ta gama gyara ɗakin ta yi wanka ta shirya cikin atampa riga da skirt, ta sauko ƙasa dan yunwa ta ke ji. Gidan shiru sai ƙaran TV da aka bari a kunne. Zuwa ta yi wajen dining ɗin ta zauna ta zuba abinci ta fara ci.
Adama ta fito daga kitchen za ta haura sama Farida ta kira ta.
Sai da su ka gaisa sannan ta ce ” mutanen gidan sun fita ne?”
“Eh”
“Ayya sannu da aiki”
“Na gode Anty”
“Anty kuma, ai sai ki sa na ji kunya. Ki kira ni Aisha ko Farida”
“Anty Farida dai”
Farida ta sa dariya.
“Dama na ce daga yanzu ba sai kina gyara ɗakin mu ba, zan dinga gyarawa”
“Na gode” Adama ta faɗa tana murmushi.
Da rana tareda Adaman su ka yi girkin rana, su na aikin tana ma ta tambayoyi gameda gidan. Su biyu ne ma su aikin ita da Tasallah. Tasallah kuma ta je gida an mu su rasuwa. Ita Adama matar Iliya dreba ne ita kuma Tasallah bazawara ce wanda aƙalla za ta kai shekaru arba’in zuwa arba’in da biyar.
Da su ka gama ta haura sama ta duba wayar ta ta ga miss call ɗin Maijiddah da text ɗin ta, inda ta ke sanar da ita ta isa gida lafiya. Kiran Maijiddan ta yi amma ba ta ɗauka ba sai ta kira Ummi. Sosai su ka yi hira da Ummin wanda ta ke ta ƙara ma ta nasiha akan haƙuri…
Ƙarfe uku saura Mom ta dawo, bayan ta kimtsa ta ci abinci ta sa Adama ta kira ma ta Farida.
Farida na bacci ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa kamar daga sama, ta tashi da ƙyar ta zo ta buɗe.
“Anty Farida Hajia na kiran ki”
“Ok tana ina? Tana falon sama”
“Ina zuwa”
Sai da ta wanke fiskarta sannan ta fito.
A ɗan kishingiɗe ta sameta kan kujera ta yi nisa cikin tunani.
Farida ta ɗan yi gyaran murya ta ce ” Mom barka da yamma”
Mom ta ɗago kai ta kalleta tareda ƙaƙaro murmushi.
“Sannu da zuwa Aisha”
Sai da Farida ta gyara zama sosai sannan ta ce “you’re lucky Aisha, Kin san, Najeeb yana son sunan Aisha sosai”
“Ayya! Amma bai taɓa kirana da shi ba kuwa”
“He likes you. Na san bai gane hakan ba amma nan gaba zai gane”
Farida dai shiru ta yi tana sauraron wannan mata wadda ta ke uwar miji gareta.
Mom ta ɗauki wanni takarda da ke gefen ta ta miƙawa Farida ta ce ” na rubuta mi ki abubuwan da ya ke so da wanda ba ya so. Zai taimaka mi ki wajen ganin kun fahimci juna da wuri”
“Na gode Mom”
Ta miƙa ma ta wani ƙaramin jewelry box ta ce “wannan kyauta ne da na ke son bawa duk matar da Najeeb ya aura”
Farida ta ƙarɓi box ɗin tana godiya.
“Open it”
Tana buɗewa ta ga sarƙa ce ta dimond sai walwali ya ke.
“Its pure dimond” Mom ta faɗa tana kallon yadda Farida ke kallon sarƙan
“Mom na gode, Allah ya saka da alkhairi. Haƙiƙa banida ma bakin godiya, this is too much Mom”
“Ba komai, just make him happy”
“Insha Allah zan yi ƙoƙari Mom”…
Farida na shiga ɗaki ta ɗau sarƙan nan ta gwada sawa a wuyan ta, tana duba kan ta a madubi. Wannan duk taron da ta je ta sa ka shi sai ta zama topic of the day. Tana cikin dubawa sai kuma ta ji jikinta yai sanyi tunowa da ta yi wanda aka bata sarƙan domin sa ba wai ya damu da ita ba ne.
Ta maida sarƙan inda ya ke sannan ta ɗauko takardan da Mom ta ba ta, ta fara karantawa.
- ya fi son kala baƙi
- ya na son cin fruits (musamman apple, inabi da lemu)
- ya na son coffee
- ya na son ƙanshi
- ba ya son wari
- ba ya son ƙazanta
- ba ya son hayaniya
- ba ya cin doya
- ya fi son kifi akan nama
- ba ya son jan abu….
Wayar ta da ya fara ringing ne ya sa ta tsaya da karantawa. Ta ɗauko wayan sai ta ga Rayyan ke kiran ta. Har wayan ta katse ba ta ɗauka ba.
“Mi kuma zai ce min” ta faɗa a fili yayinda kiran sa ya sake shigowa. Sai a kira na uku ta ɗauka.
“Rayyan lafiya ka ke kirana?”
Daga ɓangaren Rayyan ya ce “My Farida ban san ya zan yi ba, yanzu na ke jin wai hotunan nan haɗa su aka yi, wai Alhaji Jibo ya zo ya samu Baba ya nemi a maida zancen auren mu. I’m sorry dear, ki bani lokaci mu zauna mu yi magana”
“A ina za mu zauna? A saman kwano ko a saman bishiyan mangoro. Look Rayyan, kar ka ƙara kira na, ni matar aure ce”
Ta na kashe wayar ta cillata kan gado ta cigaba da karanta takardar da Mom ta ba ta.
………………………
Kusan ƙarfe biyar wa su baƙi su ka zo Adama ta zo ta kirata ta sauko ƙasa. Su biyu ne, ɗaya ta ganeta domin jiya ta zo, ƙanwar Daddy ce da su ke kira Hajia Fatima. Ɗayar kuma ba ta san ta ba.
Sai da su ka gaisa Hajia Fatima ta gaya ma ta sun zo ƙarɓan sizes ɗin ta ne saboda lefe da za’a haɗa ma ta.
Hajia Salma da su ka zo tare wadda ta ke amaryar Uncle Sulaiman ne ta ɗauko Tab ɗin ta ta na rubuta sizes ɗin, tundaga na inner wears zuwa general measurement na ta.
Bayan sun gama aka buge da taɗi, su na haka sai ga Najeeb ya shigo.
“Yawwa ango dama kai mu ke jira”
“Ni kuma?”
“Yes, mun zo karɓan kuɗin haɗa lefe”
“What’s that?”
“Ɗan iska, dan ka yi ƙwacen mata sai ba za ka ma ta kayan lefe ba. To ba zai yiwu ba”
Hajia Salma ta ce ” Najeeb bar Hajia Faty da tsokala. Check za ka rubuta ma na za mu haɗawa Farida kayan lefe”
Sai da yai kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “how much?”
Hajia Fatima ta ma sa daƙuwa ta ce ” ungo na ka da how much ɗin, blank check za ka bamu”
“Hell no, there’s no way i’m giving you a blank check. Ki samu daman zuba jari a shagunan ki ko?
“Zan ci ƙaniyar ka Najeeb”
Najeeb ya zauna ya ciro check book na shi ya fara cikatawa Hajia Salma da Hajia Faty idon su ƙyam akan abinda ya ke rubutawa.
Hajia Fatima ta ce “Allah ya sawwaƙa Najeeb, mi wannan zai yi? Ka san ina da ina zamuje kuwa? Kai ka na sa kaya designer ba ka so matar ka ta sa designer ne?”
Farida kam dai kallon su ta ke yi dan ba ta ga nawa ya rubuta ba. Ƙarshe dai dole blank check ɗin ya ba su…
Yana shiga ɗaki ya ji wayar Farida da ke kan gado yana ringing haka kawai sai ya tsinci kan sa da ɗaukar wayan wanda kafin ta yanke ya ga sunan nan dai da ke tada ma sa hankali My Ray tsaki yai ya maida wayar ya ajiye.
Ya na cire kaya amma sai tsaki ya ke shi kaɗai.
Lokacin da ta shigo yana kan gado, ya kunna TV da ke ɗakin yana kallon tashar Aljazeera.
“Sannu da dawowa, ya aiki”
” your Ray ya kira ki”
Dam ta ji gaban ta ya buga. Ita wallahi ta manta ba ta goge numbar bane ɗazu.
“Sir Najeeb ba wai abinda ka ke tunani ba ne, Allah mantawa na yi ban goge numbar ba”
Bai ce komai ba sai ma remote da ya ɗauka ya fara chanja tasha.
Ganin yai shiru ta ce ” Sir Najeeb ka yiwa Mom godiya ta min kyautar girma. She gave me a dimond necklace”
“Mrs Jibo” ya faɗa da sigar jan hankali.