SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Kar ki ƙara yi min maganar matar nan”

Farida ta zaro ido “mahaifiyar ta kan”

“Idan ki na so mu zauna lafiya, to ki dena kawo min zancen ta”

” yau na shiga uku, Sir Najeeb….”

“Shhhhhhh”

Haɗiye maganar ta yi dan yadda ta ga ran sa ya ɓaci.

Zama ta yi a gefen gadon ta ce “Sir Najeeb zan yi aikin, amma sai ka amince za ka bani dama na wanke kai na daga zargin da ka ke min”

” good for you”

……………………..

Zuwa yanzu ta gama gane yanayin gidan. Mom ba ta da matsala ko kaɗan hakan ya sa ta rasa gane dalilin da zai sa Najeeb ya dinga ma ta abinda ya ke yi. Najdah kam ƙiri da ƙiri ta ke nuna ba ta son ta. Ita kam ko ajikin ta, dan ba wannan ba ne a gaban ta.
Ranar asabat da ta cika sati ɗaya ‘yan gidan su su ka zo ma ta gaisuwa. Ta ji daɗi sosai kuma ta karrama su, gayya guda su ka zo dan duka matan Baffa Musa ne su ka zo da yaran su kusan su goma. Da za su tafi ta haɗa mu su tsaraba…

Anas tun ranan da Najeeb ya ma sa zancen zai dawo da Farida aikin t, ya kira yana ma ta faɗa akan miya sa za ta amince da haka, ta nuna ma sa ba komai ita ke son komawa aikin…

“Sir Najeeb wai haihuwa ka ke a banɗakin ne? Tun ɗazu fa” ta cigaba da ƙwanƙwasa banɗakin.
Haƙura ta yi ta je ta zauna tana jiran sa, dama fitsari ne ya matseta.

Yana fitowa ta tashi da sauri ta shiga banɗakin.

Tunanin ko lafiyarta lau ya ke. If she’s really pressed mi ya sa ba za ta je guest room ba.

Lokacin da ta fito ɗaure da towel ya riga ya shirya takalmi kawai ya ke sawa.
“Sir Najeeb ka jirani mu tafi tare dan Allah”

” i’m not your driver”

“Sir Najeeb ya ka ke so na yi, anguwar kun nan ba lallai mutum ya samu abin hawa da wuri ba”

“Akwai mota a gidan”

“Motan tuƙa kan ta za ta yi ne. Ni ban iya tuƙi ba”

Ya miƙe tsaye ya ce “good for you”
Har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya juyo ya ce “idan kin je office ki yi aikin ki kamar yadda ki ka saba, cause our relationship is strictly professional”

“Na ji Mr professional”

………..

Ta ci sa’a da ta fito lokacin Mom za ta fita ta ce ta shiga ta kai ta. Da suna tafiya ta ce idan sun dawo ta zo ta karɓi key ɗin mota. Farida ta ce ba ta iya tuƙi ba, mom ta ce za ta sama ma ta dreba.
Lokacin da ta shigo kamfanin kowa kallon mamaki ya ke ma ta tunda dai kowa ya san ita Sir Najeeb ya aura. Kai tsaya office ɗin ta ta je, yana nan yadda ya ke ta ajiye jaka ta shiga office ɗin Sir Najeeb.

Yana waya lokacin da ta shigo dan haka ta samu waje ta zauna maimakon da da take tsayawa a gaban sa. Sai da ya gama wayar ya kalli agogon hannun sa ya ce “8:44am Mrs Jibo”

Ta langwaɓar da kai ta ce “na tsaya na karya ne kuma kai ma ka san…”

“Shhhhhh, kin san ba na son latti. Today should be the last time da za ki zo min office a makare. Sannan ba na son personal excuses na ki a nan. Here, our relationship is…”

“Strictly professional na sani” ta ƙarasa ma sa.

“Good, akwai wassu saƙo da zan tura mi ki ki printing na su ki distributing na su according to their respective specification”

“Ok” ta tashi za ta tafi sai ya ce “ɗauko min wancan green file ɗin” ya nuna ma ta shelf ɗin da ke office ɗin. Ta je wajen sai ta ga file ɗin yana ta ƙasa ne ta tsugunna za ta ɗauka dai-dai idon sa ya kai wajen dan ya tabbatar file ɗin za ta ɗauka. Wandon jeans ta saka baƙi sai shirt mai dogon hannu ash color, ta yi rolling da baƙin gyale. Ɗan tsugunnon da ta yi sai rigan ya ɗan ɗaga. Ya rintse idon sa saboda wani abu da ya ji ya tokare ma sa maƙoƙoro.
Farida ta ɗauko ta ajiye ma sa.
Gyaran murya yai ya ce “Mrs Jibo, akwai dokar da ta ba da dama wa duk wata matar aure da ke son saka hijabi a wannan kamfani da ta sa, ba matsala”

“So?” Ta faɗa tana harɗe hannayen ta a ƙirji.

“It means, za ki iya saka hijabi ko mayafi babba tunda ki na da aure”

“I see, amma ka sani ko nawa mijin bai damu da sa hijabina da rashin sawata ba”

“Still Mrs Jibo, ya kamata…”

“Shhhhhh, Sir Najeeb our relationship is strictly professional” ta kwaikwayi muryan sa.

Ya ɗan ji zafi a ran sa amma ya dake da ce wa “ok get back to work”

Har ta buɗe ƙofa idon sa na kan bayan ta. Irin kayan da ta ke sawa ne tun da, amma ya rasa dalilin da ya sa yanzu bai son ganin ta da wannan kayan…

Tana zaune tana typing Anas ya zo zai shiga office ɗin Najeeb sai kuma ya tsaya su na gaisawa. Labarin marukan da Najeeb ya sha a kan ta ya fara yi ma ta wanda ya sa ta fara dariya. Dai-dai lokacin kuma Najeeb ya fito, ba yau Anas da Farida su ka fara hira su na dariya ba amma yau gani yai dariyar ta yi yawa.

“Ango wajen ka na ke son zuwa amma tunda za ka fita barin jira ka a nan, idan ka dawo sai mu yi maganar”

Najeeb bai ce komai ba ya fita, bai yi nisa ba sai ya dawo, har lokacin magana su ke.
Yai gyaran murya ya ce “Mrs Jibo ki tuna min ina da meeting ƙarfe goma”

Ba tareda ta kalle shi ba ta ce to.
Ya sake fita amma ko taku biyar bai yi ba ya dawo.
“Mrs Jibo follow me”

“Ina zuwa”

“Follow me, now!” ya daka ma ta tsawa. Shi kam Anas ya gane kishi ke ran sa, tun ɗazu da ya fito ya ga irin kallon da ya ke ma sa kaman zai mangareshi.

Farida ta tashi da sauri ta ce ” ina zuwa Yaya na”

Sai da su ka fita Anas yai dariya ya ce “muje zuwa Najeeb, da kan ka za ka hanata aikin nan”

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣2️⃣6️⃣

wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi

Har su ka isa second floor bai ce ma ta komai ba. Bin shi kawai ta ke yi amma har su ka dawo ba abinda ta ma sa. Su na dawo wa ta ce “Sir Najeeb dama ba abinda zan yi shi ne ka hana mazauna na su samu hutu”

“Dama hutu ki ka zo yi ne?”

“Sir Najeeb its not fair, ina zaman-zamana kawai ka zo ka tasheni ,na yi ta bin ka kaman wanda aikin bodyguard ka ɗauke ni”

Kafin ya ba ta amsa wayarta ya fara ringing.

“Your Ray?”

“To ba shi ba ne, Yakubu ne” ta faɗa tana picking call ɗin ta yi waje.

Shi ma ɗin ɗaukan waya yai ya kira Anas. Lokacin da Anas ya zo ya ce “ango-ango, ka gama yawo da amaryar ta kan. Can we discuss business”

Najeeb ya ɗan gyara zama ya ce “wannan Architect Yakubu ɗin whats his surname?”

“Yakubu Musa Wase”

“Ok”

Anas ya kalli reaction ɗin Najeeb ya kwashe da dariya yace ” ba dan ka ma sa ƙwace ba da yanzu shi ne angon Farida”

“Kar ka ƙara cewa na yi ƙwace. You and Dad force me into this marriage”

“Ayya! Ashe abinda ya faru kenan ko. Sorry Najeeb angon Aisha”

“Cut this bullshit, ya ake ciki?”

“Dama maganar hutun ƙarshen shekara ne, ta ya za’ayi a gama duk wasu major project da mu ke da su a ƙasa kafin lokacin?”…

Tana duba wasu takardu sai ga mutum ya shigo ma ta office da sallama. Ɗagowar da za ta yi sai ga Rayyan.

Ta miƙe tsaye da sauri. “Rayyan lafiya?”

“Kin ƙi ɗaukan waya ta Farida kuma na ji labari kin fito aiki”

“Wato stalking ɗina ka ke yi?”

“Farida ki zauna ma na mu yi magana”

“Wanni maganan za mu yi?, ni fa matar aure ce Rayyan”

“Exactly, matar Rayyan ya kamata ki zama ba ta Najeeb ba. Duk abinda yai ya yi ne da sanin kan shi dan ya raba mu. Idan ba rashin sanin darajan mace ba, ta ya zai auri mace kamar ki just one week ya dawo da ke aiki, aikin secretary”

“Rayyan dan Allah ka tafi. Ka ga miji na na nan”

“Miji? My Farida miji fa ki ka ce. Ina ki ka saka alƙawurran da mu ka yiwa junan mu. Tun yanzu har kin fara cin amana ta kenan”

“Yau na ga ta kai na, Rayyan duk alƙawarin da na ma ka ba wanda na saɓa aciki, Na yi alƙawarin mallaka ma ka zuciya ta da duk soyayyata idan mu ka yi aure. Kuma ba mu yi aure ba mi ya kawo maganar cin amana a nan?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button