SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Saboda yana da kuɗi ko?”

” yes, saboda ina da kuɗi”

Su ka jiyo muryan Najeeb a bayan su.

“Daɗin abin ma sai dai mutum ya bi gefe yai zagon ƙasa amma bai isa ya tunkari mace ya nemi soyayyarta ba” Rayyan ya faɗa yana yiwa Najeeb kallon banza.

Najeeb ya ƙaraso kusa da shi ya ɗan buga kafaɗar sa ya ce ” mutumina ka ɗan je ka ɗauki darasi a kan virtual reality ka ji”

Ya miƙawa Farida hannun sa guda ɗaya ya ce ” Mrs Najeeb Jibo shall we”

Farida ta haɗiye miyau saboda kan ta ya ɗaure amma indai dan ta yi abinda zai sa Rayyan ya fita a rayuwar ta ne to za ta yi. Duk da ta so Rayyan a baya, amma yadda ya shure watannin da su ka yi tare ya fasa auren ta ana saura kwana biyu ɗaurin aure ya sa tana jin ko da akwai burbuɗin son shi a tareda ita to za ta kaɗe shi ta huta. Ko da ba ta auri Najeeb ba Rayyan ya dawo, to ba za ta iya auren sa ba bayan ya riga ya watsa ma ta ƙasa a ido.

Ta sa hannun ta cikin na Najeeb tareda matsowa ku sa da shi, maimakon ya tsaya a haka sai ya jawo ta jikin sa sosai. Ya kalli Rayyan da yai mutuwar tsaye a wajen saboda kishi ya ce ” please feel free to visit Najeeb constructions some other time, yanzu Mr and Mrs Jibo za su huta. So get out”

Yadda ka san an sace balon-balon (balloon) haka gwiwar Rayyan ta yi sanyi. Yana son Farida sosai tun ranan da ya fara ganin ta a Keke kuma har yau yana son ta, hotunan da ya gani su suka birkita ma sa tunani ya rasa gane kan sa, musamman da ya kasance dama mahaifiyar sa ba son Faridan ta ke ba, ta dai haƙura ne a lokacin dan ba yadda za ta yi.

Juyawa yai zai fita dan bashida ta cewa a wajen. A yadda ya ke ganin su zai iya shaƙe Najeeb a wajen.

“One more thing, dont ever call Mrs Jibo again”
Rayyan ya ji wani abu ya suke shi a ƙirji. Ya haɗiye miyau da ƙyar sannan ya sa kai ya fita.

Rayyan na fita Najeeb ya ture Farida gefe.

Ta ɗan yi ƙara ouch.

“Sir Najeeb za ka karya min ƙafa”

Fiskar nan ba wasa ko kaɗan ya ce ” kar ki sake kawomin tarkace office”

Ta gyaɗa kai saboda yadda ta ga ya ci serious.

Har aka tashi ranan Najeeb ba shi da walwala. Tana ganin ya fito zai wuce gida ta yi saurin bin bayan sa. Bai ma ta magana ba har su ka isa gida itama ba ta ce komai ba dan yunwa ta ke ji.

Shi ne ya fara shigewa ciki ita kan zuwa ta yi ta ɗebi abinci kafin ta haura sama da tray a hannunta.

Tana shiga ta gan shi tareda Najdah, Najdah na nuna ma sa hoton abu a wayarta wai ya zaɓa ma ta.

Sallama ta mu su amma ba ta ji an amsa ba, ko da kuwa an amsan to aciki su ka yi.

“Amsa sallama yana daga cikin haƙƙin musulmi akan ɗanuwansa musulmi”

Najdah ta ɗaga ido ta kalleta sai kuma ta sauke ido. Shi kam Najeeb bai ce komai ba ya san fitina ta ke nema and he’s not ready for that.

Ta ajiye tray ta shiga banɗaki ta watsa ruwa, lokacin da ta fito Najdah ta fita. Ba ta san mi ya sameshi ba amma ta ga ko kayan jikin sa bai cire ba ya miƙe akan gado yana kallon sama.

“Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?” Shiru

“Sir Najeeb ka tashi mu ci abinci”

Ta gama duk surutun da za ta yi amma bai ce komai ba sai daga baya ya tashi ya shige banɗaki…

…………………

Sati ɗaya kenan da fara zuwa aikin ta, ba za ta ce komai na tafiya dai-dai ba ba za kuma ta ce akwai matsala ba. Yawanci ma Najeeb ba ya zama a office ya kan fita supervising ayyukan da kamfanin sa ke yi kuma ya ke so a ƙarasa kafin hutun ƙarshen shekara.

Safiyar yau da ta shiga kitchen ta samu Mom na decorating wani chocolate cake, sai ƙanshi ya ke yi.
“Mom wa ke birthday?” Ta tambaya.

“Ya kamata a ci taran ki tunda ba ki san birthday ɗin waye gobe ba” Mom ta faɗa tana murmushi.

“Najdah?”

Mom ta girgiza kai, Farida ta leƙa cake ɗin ta ga shekarun da aka rubuta “wai-wai ashe na babban mutum ne”

Mom ta yi murmushi ta ce ” he likes chocolate cake”

Farida ta ce “Ayya, cake ɗin ya yi kyau kuma”

“Akwai surprise family dinner da za ayi gobe da yamma. But dont tell him, idan ya sani ba zai zauna a gida ba”

“Allah ya kaimu gobe Mom”

………………..

Safiyar asabat bayan ya iddar da sallah bacci ya koma. Haka kawai ta tsinci kan ta da kallon kyakykyawar fiskar sa, ta jima tana kallon sa, she cant believe he’s 35yrs. Gaskiya jindaɗi da hutu na ɓoye shekarun mutum…

Da ta ɗan tattare ɗakin sai ta fita dan ta taimakawa su Adama da aiki.

Lokacin da ta dawo ɗakin kusan azahar ya riga ya fita. Ta buɗe akwatin kayan ta tana duba kayan da za ta sa. Mom ta ce iyalen gidan Uncle Sulaiman za su zo ga su Hajia Fatima, dole ta yi shigar da ba za a raina ta ba. Tana cikin duba wannan ta ajiye ta sake dubawa ta ajiye aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin,
Ta je ta buɗe ta ga Mom ne.

“Mom ki shigo”
Mom ta miƙa ma ta wani paper bag ta ce “ki sa wannan and please wear the dimond necklace”

Ta amshi bag ɗin tana ma ta godiya…
Ba ƙaramin kyau gown ɗin ciki ya ma ta ba tareda takalmi da purse wanda su ka shiga da kayan.

Ƙarfe huɗu ta fito bayan ta shirya cikin doguwar riga pink da Mom ta ba ta. Lokacin gidan an fara hayaniya, ta sauko ƙasa tana gaisawa da su Hajia Fatima…

Ya na gidan sa Dad ya kirashi akan maza-maza ya zo gida. Ya san ƙila surprise party su ka shirya ma sa. But he has no choice ba ya iya yiwa Dad mu su. Haka ya rufe gidan ya shiga mota ya dawo. Tundaga motoci da ya fara cin karo da su ya san hasashen sa ya tabbata.
Da sauri ya haura sama yana avoiding wata ƙaramar cousin ɗin sa ‘yar shekara biyar da ke cewa ya ɗauketa.
Zuwa yai ya shirya a gurguje dan text ɗin Najdah da ya gani akan ya zo Garden su na jiran sa a wajen.
Komai sauri-sauri yai tun daga wanka zuwa sa kaya. Yana buɗe ƙofa ya gan ta a bakin ƙofa. Daga sama har ƙasa ya kalleta, she look beautiful, ga dimond necklace da ta sa da ya ƙara fito da ita.

“A ka ce na zo na kira ka”

  • a surprise page gobe for team Najeeb*

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣2️⃣7️⃣

Da farko ya shagala da kallon ta amma tunda ya ƙyalla ido ya ga sarƙan da ke wuyan ta sai ya janye idon sa yana cewa “matsa na wuce”

“Sir Najeeb Happy birthday”

Bai amsa ba kawai wucewa ya yi. Ta bi bayansa tana cewa ” Dan ma ka samu na wishing na ka Happy Birthday ɗin” yana takun sa na ƙasaita ta na bin sa a baya, da ke heel ta sa sai ya zama ba ta iya sauri ba sai ta ɗan sa gudu-gudu sauri.

Sai da su ka kusa isowa wajen sai ya tsaya, tana iso shi sai yafara tafiya a hankali ta yanda za su jera tare.

Su na shiga wajen aka sa tafi. Wani cikin cousins ɗin sa ya ce ” ka ga salon soyayyar manya. Har ta tafiyar su iri ɗaya ce”

Najdah ta zo ta kama hannun Najeeb ta ma sa jagora zuwa inda zai zauna. Yana zama itama Farida ta zauna gefen sa.

“Happy Birthday babban yaya” Uncle Sulaiman ya faɗa yana kallon Najeeb da ke kujeran su na opposite.

Daddy ya ce ” kar ka kumbura ma sa kai, wannan taron domin ‘ya ta aka yi ba shi ba”

Najdah ta ɗauko cake ta kawo gaban sa. Ta kissing goshin sa ta ce ” Happy birthday sweet Bro”

Murmushi yai sannan ya amshi wuƙar yanka cake ɗin ya sa zai yanka.
Aminu babban ɗan Uncle Sulaiman ya ce ” ka yanka tareda amarya ma na mu san yanzu kam ka bar tuzuranci”

Juyowa yai ya kalli Farida wanda itama shi ta ke kallo.
” he’s right, ‘yata help him cut the cake” Daddy ya faɗa yana kallon yadda Najeeb ya haɗa rai.

A hankali Farida ta ɗau hannun ta ta ɗaura akan na Najeeb. Ido ya ƙura ma ta ita ma cikin idon sa ta ke kallo. A haka har wuƙar ya nitse cikin cake ɗin. Sai da aka fara tafi sannan su ka cire ido cikin na junan su.
Da ya yanka ma cewa aka yi Farida ta sa ma sa cake ɗin a baki bayan ta sa aka ce shima ya ba ta, relunctantly dai ya sa ma ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button