SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ba a jima ba aka fara serving abinci ana yi ana taɗi ana dariya. Haɗa kujeru aka yi da table sai ya zama kaman a dogon table ake cin abinci. Sun jeru straight akan kujerun.

Anwar ɗan Hajia Fatima ya tashi ya ce ” aga aga?”

Aka amsa ma sa da aga

“Aga waye yai aure @35yrs?”

Aka nuna Najeeb.

Aminu ya tashi “Aga Aga” aka amsa da aga

“Aga waye yai ƙwacen mata?”

Aka nuna Najeeb, wassu na dariya ƙasa-ƙasa.

Wani kallo ya watsawa Aminun dan ya girmeshi kusan shekara shida amma shi ya yi aure harda yarinyar su ɗaya.

Aminu ya zauna yana dariya.

Anas ya tashi ya ce “aga aga?”

Da aka amsa ma sa ya ce “aga waye yai auren soyayya da sakatariyar sa?”

Wassu su ka nuna Najeeb wassu kuma wanda ba son auren Najeeb da Farida su ke ba, su ka fara hararan Farida, irin su Najdah da Afrah wanda tunda ta dawo daga weekend ta tarar da auren Najeeb ta tattara ta koma gidan Uncle Sulaiman.

“Barin nuna wani short video clip na wannan masoya, there first fight and probably there first love”

Idan da yadda Najeeb zai yi ya je ya make Anas a inda ya ke tsaye da ya je. Dan wani mugun kallo ya ke aika ma sa daga inda ya ke zaune.

Anas ya ɗaga Tab ɗin sa sama ya playing video ɗin. Video compilation ne na wajen da Farida ta fara zuwa aiki har ta hana Najeeb shiga office, da wajen da ya koreta ta ƙi tafiya har ta rungumeshi lokacin da ya kira security. Sai wajen da Najeeb ya zo ya zauna akan superglue. Tun a clip na farko aka fara dariya, Daddy har da tari tsabar dariya. Wassu da ke gefe su ka dawo wajen da za su ga video ɗin da kyau.
Lokacin da video ɗin ya ƙare Anas ya ce ” Thanks to CCTV footage na kamfani mun samu wannan video na masoya mai cike da tarihi”

Najeeb ya rintse ido ya cize leɓen sa na ƙasa. Wannan embarrassment ɗin da me yai kama. A gaban su Daddy da ƙannen sa, dan duk wajen idan ka cire iyayen to ya girme mu su.

A lokacin aka fara cewa ya tashi ya duba kujeran da ya zauna ko akwai superglue a kai. Wa su kuma su na kwaikwayon maganar Farida su na “Sir Najeeb ya dai?”

Farida kam idon ta na ƙasa saboda ta ji kunya. Duk uban mutanen da ke wajen nan sun ga asirin ta.

Uncle Sulaiman yana dariya ya ce ” kai gaskiya Alhaji ka iya matchmaking. Ka haɗa Najeeb da dai-dai da shi”

Aminu ya ce ” ai yanzu da take gidan sa idan yai mata laifi da ruwan borkono zai yi tsarki”

Anwar cikin dariya ya ce ” sai ya zama tsuliyar Big B is on fire kenan”
Gaba ɗaya wajen kowa dariya idan ka cire Najeeb da ya cika yai fam.
Farida ma da ta sunkuyar da kai ɗan dariyan ta yi…

Ana cin abinci ana sake gulman abinda aka gani. ” Hajia Fatima har da cewa immediately Anas ya tura ma ta video za ta forwarding wa Najma da su Uncle Abubakar da ba sa nan…

Daddy ya ce ” kar ku sa ‘ya ta a gaba. Idan ɓera na sata to daddawa ma na wari”

Yadda hannun Najeeb ke shaking, Farida da ke gefen sa sai da ta tsorata. Ta leƙa ta ga hannun sa ɗaya da ya sa akan cinyar sa ya tamke shi kamar mai shirin kai dundu amma still hannun na rawa, ɗaya hannun da ya riƙe tsokali da shi kuwa yai wa sokalin riƙon makami ne.

Ana cin abinci amma Najeeb ba ya ci. Farida ma tunda aka playing video ɗin nan ta ka sa cigaba da cin abincin.

Lokaci guda hayaniyar da ake ta tsaya chak. Wanda su ke opposite da su Najeeb su su ka ga matar da ta doso wajen da ake taron ita da Adama da ke riƙe da tray za ta kawo wani nau’in abincin.

Jin shirun yai yawa kuma su Daddy sun ƙurawa mai zuwan ido ya sa wassu daga cikin wanda ke zaune layi ɗaya da Najeeb su ka juya, cikin su har da Aminu.
Muryan Aminun ne ya fitar da sunan wacce ta doso wajen cikin takun ta na ainihin celebrity, yadda ta ke catwalking kamar a kan redcarpet ta ke za ta je karɓan Oscar award.

“SABREEN” ya faɗa da sigar mamaki

Jin sunan ya sa sauran su ka juya duk da ma ba kowane a wajen ya san Sabreen ba, balle labarinta. Idan ka cire Najeeb da Farida duk sauran sun juya.

Najeeb na zaune, takaicin abinda Anas yai ya cika shi, chan ƙasan ran sa yana tsara irin yadda zai ciwa Anas mutunci idan su ka haɗu, ya ji muryan Aminu ta fitar da sunan da ya tsana a rayuwar sa“Sabreen)

Yadda wajen yai shiru ya sa yai tunanin ko dai Sabreen ɗin ne su ka gani ko kuma su na so su sake playing prank a kan sa da sunan Sabreen.

Sanye ta ke da wani arnen baƙin kaya. Gown ce wanda ta kamata ƙyamƙyam, sannan ya fidda duk wani sura na jikin ta. Hannu ɗaya dogo ne har zuwa wuyan hannun ta(wrist) ɗaya kuma hannun vest gareshi. Jikin rigan yana da adon duwatsu wanda sai kyalli su ke, ta ɗan yafa wani ƙaramin gyale wanda gyalen yadda ka san abin tata haka ya ke, shara-shara da shi, gyalen ma an ɗan yane shi ne kaɗan amma duk rabin gashin na ta na waje. Tana ɗauke da wani designer purse wanda aƙalla kuɗin sa a ƙiyasin kuɗin Naira zai kai miliyan huɗu. Murmushi ta ke har ta ƙaraso wajen.

“Hi everyone” ta faɗi tana ƙarasawa wajen Mom da itama ke daskare akan kujera tana mamakin zuwan Sabreen, dan ba ta da masaniya akan zuwan na tan.
Ta kissing kumatun Mom kamar yadda Larabawa su ka fiyi idan za su gaisa da mutum.

“Masa’ul Khair Ammaty” ta faɗa tana ƙara faɗaɗa murmushin ta tareda sauke idon ta akan Najeeb wanda tun zuwan ta wajen Mom idon sa ke kan ta.

“Happy Birthday Noory” ta faɗa tana gyara gashin ta da ya zubo ya ɗan rufe ma ta rabin fiska.

Najeeb ya miƙe tsaye ba tare da ya ce komai ba ya bar wajen. Yadda ya ke tafiya kawai ka san yana cikin ɓacin rai.

Da ƙyar Mom ta iya haɗa kalmomin bakin ta tambayi dalilin zuwan Sabreen Nigeria. Maimakon ta amsa ma ta sai ta tambayi Mom ɗin da cewa ko ba ta son ganin ta ne. Mom ta girgiza kai.

Hajia Fatima ne kaɗai a wajen ta iya cewa ” ‘yar burauba, kin ji yai aure za ki zo ki ɗaga ma sa hankali ko”

Ba ta ji mai Hajia Fatima ta ce ba amma ta san zagi ta yi.

“Let me talk to Noory” ta faɗa sannan ta kama hanya ta bar wajen still cikin takun ta na ƙasaita.

“Tashin hankali kenan, ana wata ga wata. Ke Aisha ki je ki hanata magana da mijin ki dan wannan yarinyar sheɗaniya ce”

Daddy yai ajiyar zuciya ya ce ” ‘ya ta ci abincin ki, ba komai”

Ala dole Farida ta fara cusa abinci a baki. Lokacin da Sabreen ta zo wajen Mom Farida ta gan ta sosai, lallai dole wannan mata ta girgiza rayuwar Najeeb. Farida ta raina kan ta a gaban wannan mata da Allah yai wa baiwar kyau haka…

………………….

Yana zuwa ɗaki ya fara safa da marwa a ɗakin, miyasa lokaci guda abubuwa guda biyu su ka zo su ka haɗu ma sa. Ga abinda Anas yai ma sa which ya san ‘yan familyn su wannan abun har bayan shekaru sai sun yi ta tsokanar sa da shi. Ga uwa uba Sabreen.
What the hell is she doing here? Ya tambayi kan sa.

8yrs, 2months and 11days da tafiyar ta. May be da ba ta gudu ba da su na rayuwa cikin jin daɗi da ‘ya’yan su biyu ɗan shekara shida da ‘yar shekara biyu, dan shekara huɗu su ka tsara za su bawa yaran na su rata (o’o ni Azizat???? Najeeb da Sabreen sarakunan tsari)
Sai dai komai ya rushe lokacin da ta gudu ta barshi da takaici.
Cikin shekaru takwas ya gina kan sa a matsayin CEO kuma Founder na babban kamfani. Yayinda Sabreen ta samu fitowa a fima-fimai 11 a cikin 8yrs. Ta dating Tom cruise ta dating wani ɗan ƙwallo, ta dating wani hamshaƙin mai kuɗi ɗan ƙasar Italy. Shi gashi bai dating kowa ba amma an kakaɓa ma sa sakatariyar sa.
Cikin shi da Sabreen ba zai iya cewa waya fi wani samun cigaba da kwanciyar hankali ba a shekaru takwas.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button