SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Wata ƙanwar maƙocinsa kuma amininsa ya aura. Budurwace dan a lokacin da aka yi auren su shekararta shashida. Cikin ikon Allah watan Halima goma ta haifi ɗan ta namiji ya ci suna Sulaiman. Murna wajen Alhaji Mustafah ba a magana. Bayan Sulaiman ta haifi Abubakar sai da ta shekara huɗu kafin ta haifi Aisha wanda lokacin haihuwanta ta wahala sosai, tun lokacin haihuwar kuma ta ke jinya bayan sati uku ta rasu. Mutuwar da ta girgiza iyalen Alhaji Mustafah gaba ɗaya.
Hajiya Mama ba ta haifa ba amma ta ɗauki duka yaran tamkar ita ta haifesu, wanda ko kaɗan ba za ka taɓa ganin abu ɗaya da zai nuna ma ka ba ita ɗin ta haife su ba. Ba ma kamar Aisha wanda ita ta shayar da ita. Haka yaran su ka taso ba su da wata uwa da ta wuce Hajiya Mama. Kuma har lokacin da Alhaji da Hajiya Maman ba wanda ya banbanta tsakanin yaran marigayi Usman Jibo da kuma ainihin yaran Alhajin. Sai dai a hankali su ka fahimci Aisha ba ta magana, kurmiya ce. Anyita magani amma shiru, tana ji amma ba ta iya magana. Wannan lalura ta sa da Alhaji da Hajiya Mama su ka maida hankalin su wajen kula da Aisha sosai.
Da Adam ya gama primary school na shi Alhaji Mustafah ya kaishi Lagos karatu. Bayan kammala secondary school na shi a kings college da ke Lagos ya wuce Harvard yai degree ɗin sa a fannin International relation,daga nan ya wuce London Business school yai wani degree ɗin a fannin Business sannan yai masters na shi da Phd a Yale University. Ya fara koyarwa a Yale kafin Nigeria ta tura shi Canada a matsayin Ambassador daga nan aka maida shi USA daga USA sai Belgium daga nan sai South korea wanda daga south korea ɗin ne yai retire ya dawo Nigeria inda yai zaman shekara ɗaya yana hutawa, gomnati ta mi shi chaaa akan ya shigo siyasa a dama da shi sai dai shi ya fi son koyarwa saboda ya amfanar da mutane ilimin da ya tara. An awarding na shi professor kuma yana visitin lecturer a jami’o’i da dama a ƙasar, musamman ABU, BUK, UJ, UI da sauran su.
Adam Jibo ya haɗu da Nabilah Aljabir ne a Yale University lokacin yana masters na shi. ‘Ya ce ga wani hamshaƙin mai kuɗi Aljabir Al Mukhtarr ɗan asalin ƙasar Bahrain. Soyayya ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin su tun haɗuwar su a library. Ba ƙaramin sa’insa aka samu ba kafin aka amince da auren su musamman da ya ke tana balarabiya shi yana bafulatanin Nigeria. Sai dai Nabilah ita kaɗai ce ‘ya mace a wajen mahaifinta kuma mahaifinta na son ta sosai.
Bayan auren su da shekara ɗaya ta haifi Najma wanda sunyi niyyar sawa yaransu sunayen da su ka fara da harafin N da A da J. Harafin N saboda Nabilah, harafin A da J kuma na Adam Jibo. Bayan shekara uku ta haifi Najeeb wanda daga shi sai da shekaru su ka ja kafin Najdah ta zo duniya, kusan shekara sha uku Najeeb ya bata. Dawowar su Nigeria Nabilah ta yi Pre Law school na wata shida kasancewar a ƙasar waje ta yi karatu kafin ta yi regular Law school. Ta yi aiki a kotuna da dama kafin daga bisani ta kai matsayin Justice.
Najma ɓangaren likitanci ta karanta tana aiki a National hospital Abuja a matsayin gyneacologist. Tana auren wani hamshaƙin mai kuɗi ɗan kasuwa kuma likita Dr Mujahid, yanzu haka yaran su uku.
Tun kafin Adam Jibo ya dawo Nigeria dama ya riga ya gina wani ƙaton gida a Kano. Anan iyalen sa ke sauka idan sun zo hutu Nigeria. Ƙannen sa sun yi aure suma da nasu iyalin Fatima na aure a Kano yayinda Ruƙayya ke aure a Katsina. Suma ƙannen sa ‘ya’yan Alhaji Mustafah sun yi aure da iyalen su. Sulaiman yana Kano yayinda Abubakar ke Abuja. Duk wata su kan haɗu ayi meeting a gidan tsohuwa wato Hajiya Mama. Alhaji Mustafah ya jima da rasuwa tun kafin rasuwan Aisha. Hajiya Mama tana nan a gidan Alhajin sai fama da jikoki. A gefen gidan Alhajin duka Sulaiman da Abubakar su ka yi gininsu. Shi Adam ne gidan sa yai nisa da su. Sai dai shima indai yana gari to kullum sai ya je ya gaida Hajiya Mama wannan ya zamo ma sa al’ada. Hajiya Mama ita ya sani a matsayin uwa. Goggon su ta jima da rasuwa bayan rasuwar Mahaifin su ta sake wani auren a Ashaka inda wajen haihuwa ta rasu. Haƙiƙa Hajiya Mama uwa ce ta gari. Ba ta haifi nata ba amma ta riƙe yaran mijinta tsakani da Allah wanda har yau suna darajata. Inda ace ta ha’ince su da tuni sun watsar da kashinta musamman bayan da Alhaji Mustafah ya rasu.
Duka karatun Najeeb a ƙasar waje ya yi su. To dama a ƙasar wajen aka haife shi. Yai degree na shi na farko a MIT (Messacheusettes Institute of Technology ) inda ya karanchi Engineering and Technology daga nan ya sake wani degree ɗin a ɓangaren Architecture. A London yai Masters na shi kafin ya tafi Korea yai Phd na shi.
Ya fara aiki a Korea da wani construction company kafin ya ajiye aikin ya je yai wani course a India, lokacin Mahaifinsa Professor Adam Jibo ya dawo Nigeria da zama. Bayan ya ƙare course ɗin ne ya dawo Nigeria ya buɗe Kamfanin sa mai suna Najeeb constructions shekaru bakwai da su ka wuce kenan.
Ya taso cikin kuɗi kuma ya nemi kuɗi ya samu. A shekarun sa talatin da huɗu, ba abinda ke gaban sa da ya wuce kamfanin sa. Zai iyayin komai saboda samun ɗaukakar kamfanin sa.
Anas shi ne babban aminin sa, jinin su ya haɗu sosai duk da kuwa Najeeb ya girmeshi da shekara uku, amintar su ta sa lokacin da ya buɗe kafanin sa ya jawo shi gefen sa su ka haɗu su ka ɗaukaka kamfanin saboda shima Architect ne. Bayan Daddy da Najdah wanda ya ke kira Baby to Anas shi ne mutum mafi kusa gareshi idan ka ɗauke Hajiya Mama. Sun jima da baran-baran da yayarsa Najma a kan ƙin Mahaifiyar su daya ke yi wanda har yau babu wanda ya san dalili abu kusan shekaru ishirin kenan.
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Free page
0️⃣0️⃣3️⃣
Kamar kowani lokaci idan ta zo Kano ɗakin Inna ta ke kwana, wannan karan ma hakan ce ta faru, sai dai yanzu Maijiddah da Zainab ke kwana a ɗakin bayan rasuwar Inna. Daga zuwan Farida ta kori Zainab a ɗakin tace ba za su kwana su uku ba. Zainab ta fice daga ɗakin tana ƙuƙuni.
Maijiddah ‘yar Baaba Sabuwa ce, kuma duk cikin yaran gidan tafi su hankali, kasancewa anyi auren ƙannenta biyu gashi za’ayi wasu biyun ya sa ake goranta mata rashin miji, kullum a takure take, dududu shekarar ta ishirin amma yadda ake mata gori a gidan ka ɗauka ta shekara talatin ne ba tayi aureba. Wai har ‘yar Zainab da ke shekara shahuɗu tanada samari ita ba ta da kowa. Duk masu zuwa wajenta ba sa jimawa su ke guduwa. Islamiyya kaɗai ta ke zuwa yanzu, sai kuma takan taɓa ɗinki a keken Baabarta sannan tana sana’ar kitso. Dan wani lokaci har gida ake zuwa a kirata ta je ta yi kitso, domin gaskiya Allah ya bata baiwar iya kitso.
Shekarar ta uku da gama secondary, dokar Baffa Musa ce, sai dai mace ta yi karatun gaba da secondary a gidan mijinta amma ba a gidan shi ba, shi ya sa Maijiddah ba ta yi wani hoɓɓasa domin ta cigaba da karatu ba, saidai cikin ran ta tana ƙwaɗayin hakan. Ba wai muni gareta ba tana da kyau dai-dai gwargwado sai dai gaskiya guntuwa ce. Dan harta Zainab da bata gama tsayinta ba, ta fita tsayi.
Maijiddah tafi ganin gajartar da Allah ya mata a dalilan da ya sa ta rasa manema…
Suna sallar Asuba Maijiddah ta gaida Farida sannan ta fara gyara ɗakin su har lokacin Farida na yin azkar. Da ta gama ta fita dan ta fara hidiman cikin gida. Lokacin da Farida ta fito daga ɗaki Maijiddah kaɗai ta samu a tsakar gida tana shara. Cikin isa ta riƙe ƙugu tace ” Jiddah ina batun dokokin dana sa a gidan nan wancan zuwana Kano?”