SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

…………………..

Su Daddy na zuwa aka duba jikin Sabreen wanda har ya feso da ƙuraje abinka da jar mace. Magani aka ba su aka ce ta shafa. Mom ta karɓa ta shafa ma ta. Likitan cewa yai allergy ne ba komai ba.
Mom ta ce da sun koma gida za a chanja ma ta ɗaki tunda ta ce daga kwanciya a gado ta fara jin zafi da ƙaiƙayin.

Lokacin da su ka dawo gida ƙarfe shabiyu na dare ya wuce. Ɗakin Najma da ta ke sauka idan ta zo su ka wuce da ita. Mom ta je ta ɗebo ma ta kaya a wancan ɗakin da ke ƙasa.
Sai da su ka tabbatar ta kwanta a wannan gado lafiya kafin su ka bar ɗakin…

Farida ta yi bacci kafin su dawo amma Najeeb ya ji dawowar su, sai dai ko leƙowa bai yi ba.

Yau da asuba Najeeb ya fito daga wanka yana sa kaya sai ga siririyar tusa ta fito. Farida da ke shirin shiga banɗaki ta leƙo inda ya ke dan sarai ta ji tusan.

“Sir Najeeb ka ji abin da na ji kuwa?”

Yai gyaran murya ya ci gaba da saka belt ɗin da ya ke ba tareda ya kulata ba.

“Sir Najeeb fitar tusa na ji fa, kuma ba ni na yi ba. Ba ma irin warin tusa na bane”

Ɗagowa yai ya kalleta ran sa a haɗe.

“Ke wai bakin ki ba ya iya yin shiru ne?”

Ɓiiiit sai ga tusan ta kuma fitowa.

Ta kama baki tana faɗin “Lahaula! Sir Najeeb ashe kai ne. Ina ga basir ke damunka, ka nemi magani”

Hannu ya kai zai buge bakinta ta ja baya da sauri tana dariya. Sai da ta shiga banɗaki ta leƙo da kan ta ta ce “Sir Najeeb tusan ka irin ta yara. Kasan ance tusa kala uku ne akwai Ɓiiiit na yara, booooot na manya, alanrankiɗibobot na tsofi”
Tana faɗin haka ta banko ƙofar banɗakin…

Ya na tsaye yana naɗa tie amma dariya ya ke ciki-ciki. Cikin zuciyar sa yana maimaita abin da ta ce. “Where on earth did she know all this” ya tambayi kansa.

Kafin ta fito ya riga ya shirya ya fita. Lokacin da ya kai ƙasa ya haɗu da Daddy.
“Morning Dad”

“Morning ya jikin Aisha?”

“Da sauƙi” ya faɗa yana tuno abin da ya faru jiya.

“Allah ya ƙara ma ta lafiya, za ka koya ma ta mota ne ko za ka enrolling na ta a driving school? Ka ga ba daɗi Najdah na hawa mota ita ba ta da shi”

” Ehm Ehm…” ya rasa abin faɗa.

“Shikenan duk abinda ka yanke ya yi dai-dai”…

……………….

Saboda abinda ya faru ranan Sabreen ba ta fita ba. Lokacin da Najdah ta dawo ne ta ke jin abinda ya faru a bakin Sabreen ɗin, saboda ba ta kwana a gida jiya ba, gidan Uncle Sulaiman ta kwana.

Najdah ta tashi ta je ɗakin dan ta tabbatar da zargin ta. Sai dai Adama ta riga ta chanja bedsheet ɗin kuma an gyara ɗakin dan haka ba abin da ta gani.

Da ta dawo ta ce da Sabreen ta san wanda ya sa ma ta abu a gado. Sabreen ta zaro ido tana tambayar waye?…

………..

“Khalidah ban gane mi ya ke faruwa ba? Kin min alƙawarin zan samu wannan sakatariyar Najeeb ɗin amma daga dawowata ki ke min zancen banza wai Najeeb ya aureta. Ya aka yi haka? Ba kin tabbatar min plan ɗin mu zai tafi dai-dai ba. Zai koreta a aiki ni kuma na sameta”

” Alhaji matawalle ban san ya zan ma ka ba. Ba fa kai kaɗai ka ke jin zafin abin nan ba. Kai damuwarka ka kassara Najeeb ni damuwata na samu Najeeb. Kai buƙatar ka ta biya ka sa Najeeb ya rasa babban project wanda hakan ta jawo ma sa asara, ni kuma fa? Mai na samu banda ƙara haɗa Najeeb da sakatariyar sa”

“A’a Khalidah bayan kassara Najeeb kin min alƙawarin samun sakatariyar sa, Farida sunan ta ko?”

” Alhaji Matawalle ka fita a office ɗi na, ka bar ni da takaici da ƙuncin da zuciyata ke fama da shi”

“Kar ki kawomin zancen banza Khalidah, ba na neman abu na rasa”

“Ya zan ma ka ne? Ka je ka ɗauki Farida ma na idan ka isa”

“Haka ki ka ce ko” ya girgiza kai ya fita daga office ɗin.

Yakubu ya koma da baya lokacin da ya ga Alhaji Matawalle na shirin fitowa. Dama ya zo kawo wa Khalidah wa su takardu ne ya ji ƙarshen hiran na su. Jin sunan Farida ya sa ya fasa shiga office ɗin.

…………………..

Wannan weekend ɗin da Aneesa ta zo ne ta lura da cikin jikin Maijiddah. Ba ta san lokacin da ta ce “Sweetheart yaushe wannan yarinyar ta samu ciki?”
AbdulWahab bai kulata ba ya cigaba da cin abincin da ya ke yi.

“Sweetheart magana fa na ke”

“So ki ke na bayyana mi ki abinda mu ka yi ta samu ciki? ko so ki ke ki san sau nawa mu ka yi kafin ta samu ciki?”

“AbdulWahab zai kai 4 months fa”

“Allah ya sauke min ita lafiya amin”

“Abinda ma za ka ce kenan? Bayan ka gama cin amana ta da yarinya ƙarama, wanda a haife ka haife ta har kana da bakin cewa Allah ya sauketa lafiya”

“Ya nuna ina da lafiya kenan, kuma kin ga ina da damar ƙaro irin Hauwerh biyu idan ina so, kin ga in shiga nan in shiga nan”

Aneesa ta cillar da cokalin hannun ta.

“Wallahi ba zai yiwu ba. Ba ka isa ba AbdulWahab”

“Ki cigaba da aiki a Abuja, zan cigaba da aiki a nan kuma da idon ki za ki dinga ganin sakamakon ayyuka na ma su kyau da tarin lada. Alhamdulillah da na kasance musulmi, na ke da damar auren mace fiye da ɗaya. Kin ga musulunci ya min rana”

Juice da ke glass cup a gaban ta ta ɗauka ta watsawa AbdulWahab tana zage-zage. Bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya bar wajen.

“Ka dawo ma na, ka dawo mu ƙarasa maganar, macuci kawai”…

Wannan weekend ɗin gaba ɗaya cikin faɗa su ka yi dan AbdulWahab dena shiga sabgar ta ya yi. Tana komawa Abuja ta sanar da Mama Maijiddah na da ciki, ga mamakin ta sai Mama ta ce “Allah ya raba lafiya”

“Mama kin ji mi na ce kuwa? Su baby da Alizah su na gab da samun step siblings”

“Na ji kuma na gane, idan kina son haihuwan ke ma sai ki dena planning ki koma tara ‘ya’ya rututu kamar Kaza”

Aneesa ta rasa bakin magana, dan inda ta dosa Mama ba ta bi nan ba.

A ranan da ta je office ta nemi a maida ita Lagos ko kuma ta ajiye aiki. Su ka ce za su duba.

…………………..

Da ke tun ƙarfe ɗaya Najeeb ya fita kuma ya riga ya ce ma ta ba zai dawo ba sai yamma shi ya sa ta tattara ta fito dan ta koma gida. Tana fitowa ta hango Sabreen da wassu police biyu su na tahowa. Mamaki ya kamata ta ɗan tsaya dan ta yi gulman me ke faruwa.
Sabreen ta nuna ta tana faɗin “she’s the devil, arrest her”

Farida ta zaro ido ” arrest me for what?”

“Ran ki shi daɗe za ki bimu zuwa station mu mi ki wassu tambayoyi”

“Ƙwal ubanchan, na bi ku station a dalilin me. Kun san ko wacece?”

Ɗaya police ɗin ya kwantar da murya ya ce ” dan Allah ki yi haƙuri mu je, mu ma daga sama aka samu”

Sabreen sai hararanta ta ke.

“Shikenan barin kira miji na” ta fito da wayarta daga jaka ta fara kiran Najeeb sai dai da ke inda su ke ba service sai bai shiga ba. Jikin Farida yai sanyi, ta tura ma sa text kawai ta bi police ɗin nan…

Bai duba wayar sa ba sai ƙarfe biyar da rabi bayan sun dawo kamfani. Yana duba missed call ya ga har da numbar Farida ga kuma text ɗin ta. Ya buɗe text ɗin ya ga ta rubuta Sabreen ta arresting ɗi na

“Arrest?” Yai saurin kiran numbar Faridan ya ji ta a kashe. Da sauri ya fara dialling numbar Anas ya na fita daga office ɗin da gudu…

Shi da Anas su ka isa gida dan numbar Sabreen ɗin da Najdah ta turo mu su an ƙi ɗaga kiran su.

Hankali kwance su ka samu Sabreen tana zaune a falo tana cin apple.

“Where’s she?” Ya daka ma ta tsawa

” who?”

“Dont be stupid Sabreen, where is she?”

Juyar da kai ta yi gefe ba ta amsa ba.
Ƙarasawa yai wajen ya fincikota yai waje da ita Anas ya bi bayan sa…

…………

Tun da su ka shiga mota ya ke faɗa abin mamaki Sabreen ta ce ba za a fitar da Farida ba saboda abin da ta ma ta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button