SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Lokacin da zai tafi bayan ta raka shi wajen motar sa ya ce ” za’a koma aiki monday yaushe za ki dawo?”

“O’o ni Aisha Farida, dan aiki kawai za a neme ni. Ni kam dole idan na koma a chanja min matsayi ya kamata a upgrading ɗi na, na bar matsayin sakatariya”

” ki na son ƙarin matsayi ne?”

“Haba Sir Najeeb wa ya ƙi cigaba a duniya”

Bai san ya ake zuwa gai da sarakai ba shi ya sa bai zo da komai ba. Ya dai bar musu dubu ɗari a gefen ɗrinks ɗin da su ka kawo ma sa wanda ko taɓawa bai yi ba…

Har motar sa ta ƙule Farida ba ta bar wajen ba. Tana ƙissima abubuwa dayawa a ranta. Zuwan Najeeb ya sa Najeeb ya ƙara samun wani matsayi na daban a zuciyar ta…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣3️⃣1️⃣

wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900

Yana hanya ta kirashi lokacin koma fita daga Jos bai yi ba. Ya saƙala bluetooth ya amsa kiran.

“Sir Najeeb shi ne har da ɗawaiyina haka. Mun gode Allah ya ƙara buɗi. Allah ya kai ka lafiya”
Amin kawai ya ce ya kashe kiran.

Da ya isa Kano yana so ya kira ta amma ya ka sa. Sai ya ɗauko wayar zai danna numbar ta sai ya fasa ya ajiye, ana huɗu da yai haka sai ga text ɗin ta ya shigo tana ma sa ya hanna da fatan ya isa lafiya.
“Na isa” kawai ya daure ya rubuta ya ma ta reply da shi. Maimakon ta haƙura a haka sai ta kuma turo da wanni text ɗin.
“Sir N mi zan taho ma ka da shi? ina son zuwa Wase gobe”

Bai san ina ne Wase ba, dan haka ya minimizing wayar ya browsing sunan nan ya gane wata ƙaramar hukuma ne a Jos.

Ya ma ta reply da “ok”

Ta sake turo wani saƙon ” Sir N ba ka faɗi abinda zan kawo ma ka ba”

Ya na so ya ajiye wayar ya shareta amma zuciyar sa ta hanashi

“Kan ki” ya tura ma ta ba tareda ya gama tantance ma’anar faɗin hakan ba.

“Kan kifi? Sir N kan wani irin kifi?”

Ganin reply ɗin ta ya sa shi murmushi. Ya ɗan jima kafin ya tura ma ta “Mrs Jibo sleep”

Good night kawai ta sake turowa daga nan ba ta kuma turo da wani saƙon ba. Shi ma ya ajiye wayar sa gefe ya kwanta.

…………………..

Safiyar Sunday ya aika ma ta da Iliya driver akan ya je ya ɗauko ta. Ita kam tana chan tana kan haɗa kayan tsaraba da za ta zo da shi. Sai da Iliya ya kusa isa cikin Jos sannan ya kira ta ya ce ya kusa isowa.
Wani matsayi ta ke kuma hangowa kan ta idan ta koma Kano. Ya sa an kawota da mota ya kuma turo ma ta driver ya dawo da ita. Wannan karramawar sai Mrs Jibo ai…

Lokacin da su ka isa gida ana kiran sallar maghrib. Iliya ya je ya kira Friday su ka shiga da buhun dankalin turawa da ta zo da shi da kuma wata ƙatuwar jakan ghana-must-go.

Ɗakin Mom ta je dan ta gaidata ta samu ba ta nan, ta wuce ɗaki ta shirya ta yi sallar la’asar da magariba…

Ƙarfe tara ta sauko ƙasa dan ta nemi abinda za ta ci, ba komai a dining ɗin hakan ya sa ta shiga kitchen shi ma wayam. Yunwa ta ke ji dan haka ta tsaya ta girka noodles da soyayyan ƙwai, ta fito ɗauke da plate ɗin shi kuma Najeeb ya shigo.

“Sir Najeeb” ta kira sunan sa. Juyowa yai ya ganta tsaye riƙe da plate da cup

Sai da ya gama kallon ta daga sama har ƙasa sannan ya juya ya tafi. Ta bi bayan sa da baki buɗe.

A dining ta zauna ta ci abincin ta dan idan ta haura sama za ta ji ƙiwuyar saukowa, sai da ta gama ci sannan ta wuce ɗaki.

“Sir Najeeb irin ba ka ji daɗin ganina ɗin nan ba, ko sannu da zuwa babu”
Bai kulata ba hakan ya sa ta gane akwai abinda ke damun sa dan bayan bai kulatan ba fiskar sa ya nuna yana cikin damuwa.

“Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?”

“Please stop talking” abinda ya iya faɗa kenan ya gyara kwanciya a kan gado.
Tabbas akwai abinda ke damun shi dan Najeeb ba ya bacci da wuri, sannan duk rintsi sai ya yi wanka ya sa kayan bacci kafin ya kwanta.

Kaman yadda ya buƙata ɗin, shirun ta yi tana tunanin ko me ke damun shi.
Har ta kwanta Najeeb bai tashi ba, ba kuma baccin ya ke ba dan idon sa a buɗe lokacin da ta leƙa shi…

Washegari da ta shirya ta fito ne ta haɗu da Tasallah a kitchen wanda ke shaida ma ta Mom ba lafiya an ba t gado.
“Ayya ashe shiya sa jiya da na dawo na ji gidan shiru. Ya jikin ta?”
Tasallah ta ce da sauƙi. Maimakon office da ta yi niyyar zuwa sai ta wuce asibitin lokacin Iliya ya kawo Adama za ta ɗauki wassu kayan buƙatu sai su ka tafi tare.

Ta yi mamakin yadda Mom ta faɗa haka. A wajen Najdah ke cewa ” tunda yanzu ke ki ke juya Big B sai ki sa ya zo ya ga Mom. Kin wani yanko ƙafa kin zo irin son a sani ɗin nan”

Farida ta kalli Najdan sannan ta kalli Mom da ke kwance tana bacci.

“Na san da cewa ba kya son ganina tareda yayan ki, amma ki sani shi ya kawo ni gidan ku ba ni na kawo kai na ba. Tun farko-farkon zuwa na ki ke ta ƙananun magana akai na, ban tanka mi ki ba. Kar ki sa na kalle ki da idon Aisha Farida dan ba za ki ji daɗi ba. Ki bini a hankali mu tafi a yadda mu ke yanzu”

Najdah ta yi tsaki, ta ɗau waya ta fara latsawa.

Farida ta fice daga ɗakin gudun kar ta fara masifa ta tada Mom daga bacci. Amma tabbas za ta ware lokacin Najdah nan ba da daɗewa ba…

Kai tsaye Najeeb constructions ta wuce sai dai da ta je office ɗinta kama baki ta yi saboda chanji da ta gani, office ɗin ta da na Najeeb ya koma kusan guda ɗaya, maimakon gini da ke tsakanin su yanzu wani tinted glass ne ya raba su wanda daga office ɗin sa yana iya hango komai a na ta office ɗin amma ita kuma ba za ta ga na sa ba.

” ba dai wannan Sir Najeeb ya ke nufi da matsayi ba”

Ba ta gama zama ba Najeeb ya shigo ran sa a ɓace. Yanzu ya fito daga board meeting.

“Sir Najeeb ashe Mom ba lafiya shi ne ba ka gaya mun ba”

“Get back to work Mrs Jibo”
Gwiwanta yai sanyi ba dai duk wani zumuɗi da zaƙalewan da ta ke yi a kan sa duk na banza ba ne.

“Noory” muryan Sabreen ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

Murmushi Sabreen ta yi ganin Farida a wajen. Da alama itama daga wajen da Najeeb ɗin ya fito ta fito.

Ganin Sabreen ya sa ta ma tuna da zancen ta, ita harga Allah ta manta da wata Sabreen.

“Noory, you are just taking it personal, i’m here to work”

“Kar ki sake kirana da wannan sunan. Here and anywhere else i am Najeeb to you”

Ta ɗan ji haushi saboda a gaban Farida ya faɗa. Amma ta dake ta ce “fine”

Farida ta fice daga office ɗin ta koma na ta duk da ta san daga inda ta ke su na kallon ta.

Wani yanayi ta tsinci kan ta ciki. Sabreen ta fara aiki anan, mi hakan ya ke nufi? Kenan watarana Sir Najeeb zai aiketa wajen Sabreen ko Sabreen ɗin ta ba ta saƙo dan ta kaiwa Sir Naheeb. Ba zai yiwu ba, dole ta ajiye aikin nan. Ba za ta yi aiki tana ƙarƙashin Sabreen ba, wannan cin fuska ne.

“Congratulations ‘yar uwa. Finally gaskiya ta fito” muryan Anas ya doki kunnen ta.

“Wani gaskiyar?” Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓoye damuwar ta.

Zama yai zai ma ta bayani sai ga Sabreen ta fito.

Tana ganin su ta yi wani murmushi sannan ta juya tana catwalking ta fita.

Anas ya juyo ya kalli Farida wanda itama bin bayan Sabreen ɗin ta yi da kallo.
Ya ce “asirin wanda su ka kitsa mi ki sharri ya tonu. Gaskiyar zance ta fito”

“Haba! Yaya na wani ɗan Alatsinen ne ya ke son ganin baya na”

“Wallahi Khalidah ce”

“Ban yi mamaki ba dan za ta rina”

Nan ga shiga labarta ma ta yadda aka yi gaskiya ta fito.
Da kotu za su shiga amma an settling case ɗin tsakanin Kamfani da su saboda Alhaji Matawalle ba ya so a je kotu domin ya na siyasa kuma ya na son fitowa takaran senator. Na biyu kuma Alhaji Tukur mahaifin Khalidah ba ya son wargaza alaƙar sa da Najeeb, 8% shares na shi a kamfanin shi ya san kuɗin da ya ke samu, shi ya sa shima ya zaɓi teburin sulhu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button