SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Maimakon Daddy ya ce ma sa wani abu ne ya samu Mom sai yai ma sa maganar Najeeb, Najeeb da su ka rabu lafiya ƙalau jiya.
“Daddy ya rasu ko?” Ya faɗa hawayen da su ka cika idon sa su na gangarowa.

Daga ɓangaren Daddy ya ce ” a’a, yanzu likitocin su ka fito amma bai farfaɗo ba har yanzu”

Yai hamdala tareda cewa gashi nan zuwa…

Zuwa ƙarfe bakwai na safe asibitin ya cika da ‘yan uwa. A wannan lokacin ne Uncle Sulaiman ya sa aka maida Daddy gida saboda ya chanja kaya.

…………………

Farida ba ta farka ba sai ƙarfe biyar lokacin da alarm ɗin ta yai ta ruri ba kakkautawa. Da ƙyar ta sa hannu ta jawo wayar ta katse alarm ɗin. Mafarki mai daɗi ta yi, itada Najeeb su na zaune a wani lambu, kanta na kan cinyar sa yana wasa da gashin ta.

” I love you Aysherh” ya faɗa idon sa cikin na ta.

“I love you too Sir Najeeb”

Hannun sa ya sa ya ɗan matse bakin ta ya ce “ba na hana Sir Najeeb ɗin nan ba”

“Sorry my champ”
Ta ɗan ɗago kanta ta kissing goshin sa sannan kumatun sa sannan hanci. Ganin ta tsaya ya sa yatsa ya nuna lips ɗin sa.

Ta girgiza kan ta. Ya ɗan yi ƙanƙan da ido alamar tausayi. Murmushi ta yi tareda haɗe bakin su…

Ta tashi jiki a mace ta shige banɗaki, wannan mafarki da ta yi ya sa ta sassauta jin haushin sa da ta ke ji.

Lokacin da ta zo gaban madubi, kallon kanta ta yi ta fara gwada maganan da za ta yiwa Najeeb ta yadda zai tabbatar ran ta ya ɓaci ya kuma ɗauki maganarta serious.
A hankali tana fari da ido ta ce “Sir Najeeb, gaskiya idan Sabreen za ta yi aiki a kamfanin ka to ni zan ajiye aiki na”
Ta yi tsaki ta ce ba haka bane barin sake. Wannan karan ta haɗa rai ta ce “Sir Najeeb zan ajiye aiki na”

Sai ta kwaikwayi muryan sa ta ce ” good for you”

“Good for you kawai za ka ce min? Ka na tunanin idan na ajiye aikin akwai wanda zai iya yi ne?”

Da muryar sa ta ce “dayawa ma”

” Sir Najeeb, Allah ni kaɗai ce za ka iya jura. Ba wanda zai iya juran faɗan ka. Kai ba mace ba amma sai shegen mita”

“Aysherh” ta ji muryan sa a bayanta. Da sauri ta juya amma ba kowa. Ta rufe ido tana tuno kiss ɗin su na ranan…

Saboda ta tsara ba za ta koma aiki ba shiya sa da ta gama azkar ɗin ta ta sauko dan ta taya Adama aiki.
Tana saukowa ta haɗu da Daddy wanda shigowar sa kenan, ganin sa sanye da kayan bacci ga kuma damuwa shimfiɗe a fiskar sa ta yi tunanin ko wani abu ne ya samu Mom.

“Daddy ya jikin Mom” ta faɗa cike da tararrajin mi zai ce

“Alhamdulillah da sauƙi ‘ya ta”

“Lah ba mu ma gaisa ba” ta faɗa tana tsugunnawa ta na mi shi ina kwana.

Tausayin ta ne ya kama Daddy. A yadda ya ga Najeeb ɗazu zuciyar sa ta karaya. Yanzu idan Najeeb ya rasu wanni hali Aisha za ta shiga? Auren da bai wuce sati shida ba.

“Aisha ki shirya yanzu, idan na fito za mu je asibiti Najeeb ba lafiya”

Dum ƙirjinta ya buga “Najeeb ba lafiya, mi ya same shi?. Allah sarki ashe shi ya sa bai kwana a gida jiya ba.” Tambayar da ke yawo a kanta kenan.
Amma duk yadda aka yi rashin lafiyar Najeeb mai tsanani ce dan kuwa Daddy ba zai damu har haka ba idan minor abu ne.
Komawa ɗaki ta yi dan ta ɗau gyale da jakar ta…

Iliya ne ya ke jan su, cikin motar shiru ka ke ji. Ganin yadda Daddy ke ta yawaita faɗin Lahaula Wala Ƙuwwata Illah Billah lokaci zuwa lokaci sai Farida ta ƙara tsorata da lamarin. Ba dai Najeeb ya rasu ba ne, idan Najeeb ya rasu ina za ta sa kan ta…

Sai da su ka isa asibitin sannan Daddy ya ce ” ‘ya ta ina so ki kwantar da hankalin ki dan Allah. Insha Allah komai zai zo da sauƙi, Najeeb ya yi hatsari jiya da dare”

Dafe ƙirjinta ta yi da sauri lokaci guda kuma numfashin ta ya tafi hucin gadi na ‘yan wasu sakanni.
Hawaye ne su ka fara zirya a idon ta su na gangarowa.

“Ba kuka za ki ma sa ba, addu’a za ki ma sa Aisha”

Tafiya su ke amma ƙafafuwanta ji ta ke kaman ba ajikin ta su ke ba, she’s not feeling them ko kaɗan.
Har su ka isa wajen su Anas hawaye ta ke. Yadda ta ga an cika wajen sai hankalin ta ya ƙara tashi.

Daddy ya tambayi ɗanuwan sa ko likitan ya ce wani abu. Uncle Sulaiman ya ce sun ce ƙarfe tara za a ma sa CT-scan aga mi ya hana shi farfaɗowa dan sun ce su na zargin ƙwaƙwalwar sa ta kumbura ne.

Anas ya raka Farida gallery na theater room ɗin inda ta hango Najeeb kwance ansa ma sa life support system. A lokacin ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Anas ya ɗan dafa ta ya ce ” dan Allah ki dena kuka addu’a za ki ma sa abinda ya ke buƙata kenan”

“Mutuwa zai yi ko?, mutuwa zai yi tun ban nuna ma sa yadda na ke son shi ba ko?, Ya Anas ba zan iya jure rashin sa ba”

Shi ma dai Anas daurewa kawai ya ke amma ya karaya da halin da ya ga abokin na shi….

Zuwa yamma an tabbatar mu su da cewa akwai jini da ya daskare a ƙwaƙwalwar Najeeb wanda idan ba acire ba ƙwaƙwalwar za ta yi ta kumbura ne har kuma ta iya jawo ta dena aiki gaba ɗaya wanda ƙarshen zancen dai mutuwa ce.

Abun ka da ma su dukiya tuni aka kira Dr Sajid Usman Abdallah dan ya zo ya jagoranci aikin da za a ma sa. ( ga wanda ba su san Dr Sajid ba an bar ku a baya ???? ku karanta Mutum mugu ne. Yana nan a wattpad, za ku ga yadda Angon Zaytunah da Naziha ya sha goggonmayar rayuwa. Yai fama da zafin kishin Zayty da kuma rashin kamun kan ta. Sannan ya zo yai dakon soyayyar Ziha yarinyar da shekara ashirin da biyar cur ya ba ta, But aka ce love is blind☺)

Ranan Alhamis aka saka aikin kuma har lokacin Najeeb is in comatose. Kwana biyun nan Farida ta yi su ne akan sallaya. Kaso biyu cikin uku na daren sun tafi a sallah da roƙon Allah ne sauran kaso ɗaya kuma ya tafi a kuka da tunani.
Mom ma da aka sallamota wani tashin hankalin ta shiga dan sai da ta suma lokacin da ta je ta ga ɗan ta kwance a asibiti rai a hannun Allah…

Sun yi aikin awa shaɗaya akan Najeeb kuma Alhamdulillah an cire jinin da ya daskare ba matsala.
Sai dai Dr Sajid ya ce akwai yiwuwar Najeeb zai cigaba da zama cikin coma na tsawon lokaci. Amma, ba abinda ya fi ƙarfin addu’a…

Wata ɗaya kenan da ta wuce, wata ɗaya na kuka da roƙon Allah, wata ɗaya da tun ana cewa zai iya farfaɗowa gobe har aka zubawa sarautar Allah ido.
An tabbatar da case ɗin Najeeb ta shiga PVS (persistent vegetative state) yanzu kam sai randa ya farfaɗo kawai amma ba maganar ana tsammanta zai tashi nan kusa.

Duk wani wanda ya san Najeeb Adam Jibo sai da su ka tausaya ma sa. Shi ba mai bacci ba, shi ba mutuwa ba. Yana nan yana numfashi amma gashi a kwance ba abinda zai iya yi.

Wannan wata ɗayan da a ka yi Farida ta zama certified nurse a wajen kula da Najeeb. Tunda aka dawo da shi ɗaki na musamman da aka gyara saboda shi Farida ta koma kwana da shi. Duk yadda Daddy ya hana ta ƙi. Ita ke goge ma sa jiki safe da kuma yamma, har turaren sa ta je ta kwaso tana fesa ma sa. Ta ce Sir Najeeb ba ya son ƙazanta kuma yana son ƙanshi.

Zuwa yanzu ta rage yawan kuka da ta ke. Tana asibiti yanzu 24/7 duk da kuwa an ce ba sai an zauna da shi ba tunda ba wai tashi zai yi ya buƙaci abu ba kamar normal mai jinya. Idan ka ga ta je gida to ta je ɗauko wassu kaya ne. Kullum da safe da kuma dare sai Daddy da Mom sun zo sun duba ta tareda duba Najeeb da fatan cewa ko da na ɗan ƙaramin lokaci ne zai buɗe idon sa.

Farida ta chanja ta zama silent. Ko Sabreen ne ta zo duba Najeeb ba ta kulata, fita ma ta ke ta ba ta waje har ta gama tsiyarta ta tafi. Wanda iya ka daɗewar ta minti ishirin ne…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button