SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Yau ma ta na kwance gefensa tana ɗan shafa gashin sa da ya fara tohowa saboda lokacin da za a masa aiki aske gashin aka yi yai ƙwaranƙwal.
Taɗi ta ke ma sa kamar yadda ta saba yi.
“Sir Najeeb a ina ma mu ke”
Ta ɗan yi murmushi ta ce “yawwa na tuna, ranan da na fara jin wani abu gameda kai shine ranan da aka zo aka rescueing na mu daga hannun su Joseph. Ban ganewa zuciyata ba tun daga ranan. Ko da na dawo office kullum idan na kalli idon ka sai na ji wani abu ya taso min daga chan ƙasan zuciya ta, shi ya sa ko ina magana da kai na ke avoiding haɗa ido da kai. Ko da yaushe ina ƙoƙarin yaƙi da zuciyata saboda wani sabon al’amari da ya dinga taso min da shi gameda kai ba mai yiwuwa ba ne, na dinga tabbatar wa kaina ka fi ƙarfi na, na dinga nunawa kai na, Najeeb Adam Jibo ya fi ƙarfin Aisha Farida Salihu. Amma ka san me? Bayan ƙaddarar aure ta shiga tsakanin mu sai….”
Sallamar Anas ya katseta daga labarin da ta ke wa Najeeb.
Sai da su ka gaisa ta ke tambayar sa ya aiki?
” ‘yar uwa abubuwa fa ba daɗi. Riƙe kamfani kaman Najeeb constructions sai ma su zafi irin Najeeb ɗin. Kin san Allah daga jin zancen halin da Najeeb ya ke sai kowa ya fara fidda asalin halin sa. Aka dena bawa aiki mahimmanci ana sako-sako da duk wani ayyuka da ake yi. Can you imagine wai anyi board meeting akan wai ba su yarda na jagoranci kamfani ba”
Farida ta zaro ido ” to amma Ya Anas ba kai ke riƙeta ba idan Najeeb ba ya nan?”
“Haka ne amma kin san na ‘yan kwanaki ne wannan. Najeeb bai taɓa tafiyar da ta wuce sati biyu ba. Yanzu kuma wata ɗaya da sati uku kenan ba ya nan. Farida abubuwa sun fara ja baya. Ba ni da zafi kaman Najeeb hakan ya sa kowa ya fara abinda ya ga dama”
“Amma ka gayawa Daddy?” Ta tambaya tana mamakin wannan al’amari, ba mutuwa Najeeb yai ba amma har an fara juya ma sa baya, Mutane kenan
“Mun tattauna da Daddy kuma ya amince da shawarar da na kawo, ya ce mu yi magana da ke ɗin”
Ta ɗan gyara zama dan ta fahimci zancen sosai.
“Farida riƙe Najeeb constructions ba zai tafi dai-dai ba sai iron man kaman Najeeb. Ki na da zafi, za ki iya taka kowa sannan za ki iya shugabanci. Kin zauna da Najeeb kin ga yadda ya ke gudanar da al’amuran sa i’m sure kin tsinci ilimin shugabanci a tareda shi. Farida ki koma aiki, wannan karan ba matsayin sakatariya ba sai matsayin CEO”
“Allah ya kiyaye Ya Anas. Wani zance ne wannan. Saboda ni ce na kawo son shugabanci duniya sai mijina na asibiti ba lafiya sai na tsallakeshi na tafi wajen aiki” ta goge hawaye ta ce ” ina nan da shi anan har ranan da zai farfaɗo”
“Farida na san ki na so ki kasance tareda Najeeb, amma ba kya ganin kina da hakki akan kula da dukiyar sa. Barin gaya mi ki halin da mu ke ciki yanzu. Kamfanin da ta ke da major shares bayan Najeeb tana so ta janye hannun jarinta ko kuma mu mu sake sayar ma ta da kaso arba’in a ciki. Kin san mi hakan ke nufi? Yana nufin su na so su mallaki kamfanin ta ƙarfi, zai zama Najeeb 35% ne kawai na shi a ciki kuma kinga kamfani ta bar hannun Najeeb. Ke ‘yar kasuwa ce kin san yadda za ki yi ki kawo cigaba a wannan kamfani ki kuma ceceta. Ni Architect ne ban da wani ilimi mai zurfi a wannan fanni. Najeeb da ki ke gani bayan karatun Engineering da Architecture da ya yi yana da degree a fannin kasuwanci sannan yana da certificates dayawa a ɓangarori ma su yawa musamman leadership. Hakan ya sa komai ke tafiya ma sa dai-dai”
“Ya Anas ba zai yiwu ba. A nemi wani ko cikin cousins ɗin Najeeb amma ban da ni. Ba zan iya ba”….
“Farida……”
……………………………
Wata baƙar Marcedez benz ce ta shigo Kamfanin Najeeb constructions. Lokacin da motar ta tsaya an kai kusan minti biyu kafin aka buɗe ƙofa. Wata haɗaɗɗiyar mata ce ta fito daga ciki ta owners corner. Tun daga takun ta ka san mace ce mai aji da kuma girma. Kai tsaye ta shige kamfanin security ɗin wajen yana mata good morning ta amsa ma sa ta hanyar ɗaga hannu.
Anas ne ya nufota yana gaisheta lokacin da ta iso top floor ɗin. Tare su ka jera su ka wuce conference hall ɗin inda za ayi board meeting.
Kujeran da ta zauna an rubuta CEO a jiki waje ne da Najeeb ke zama lokacin yana da lafiya. Waje ne da bayanshi ba wanda ya taɓa zama a wajen idan ana taro haka.
Sai da ta ja numfashi ta sauke sannan ta ce “suna na Aisha Farida Salihu, Mrs Najeeb Adam Jibo kuma acting CEO Najeeb constructions har zuwa lokacin da miji na zai samu lafiya ya dawo”
Ta kalli fuskokinsu mai cike da tarin tambayoyi ta ce ko da me ja?….
Tantarantarantaran. Daga secretary sai CEO wannan ƙarin matsayi har haka @team Farida kuna da aiki a gaban ku. @team Najeeb, sorry Najeebullahi ya tafi hutu, sai kun ganshi kawai dan nima ban san ranan dawowar sa ba????
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣3️⃣3️⃣
wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900
“Excuse me, ba za mu amince da wannan ba. Ta ya za ace za ki jagoranci kamfani kamar wannan ki na matsayin sakatariya. I bet wannan kamfani za
ta ruguje kafin nan da wata ɗaya. Duk da ki na matsayin matar Sir Najeeb hakan ba zai sa ki ma ye gurbin sa a wannan kamfani ba. You are incompetent and clueless” wani a ciki ya faɗa yana huhhura hanci.
Ba tareda ta karaya ko nuna damuwa ba ta kalli mutumin ta ce ” mi ye matsayin ka a wannan kamfani?”
Mutumin ya ɗaga kafaɗa ya na faɗin ” I’m Festus Ogonna the F…..”
“Get out!” Farida ta daka ma sa tsawa wanda kowa a wajen sai da ya sha jinin jikin sa, hatta Anas da ke gefe sai da ya ji wani dum. She sounds exactly like Najeeb.
“Mr Ogonna ba za mu iya zama da wawa kuma jahili ba. Tambaya ɗaya na yi ma ka amma ka fara ba da tarihin rayuwar ka. Who cares about your name?, a wannan kamfani matsayin ka shi ne identity ɗin ka and that’s what i asked ba sunan ka ba”
Kallon-kallo aka fara yi, yadda ta ke magana da faɗa-faɗa ka ce kamfanin na ta ne tun fil azal.
“Get out!” Ta sake daka ma sa tsawa tana kallon sa ido cikin ido.
Mr Ogonna aƙalla zai kai 45yrs amma Farida ba ta kalli girman sa ba balle ta ji kunyar idon sa.
Mr Festus ya yi kasaƙe yana kallon ta. Ya buɗe baki amma ya kasa magana.
Phone da ke gabanta ta ɗauka ta danna wassu numbers. Ba su ankara ba sai ji su ka yi tana faɗin security su zo su fita da wani mahaukaci.
“You cant do this, you dont have the right” Mr Ogonna ya faɗa cikin masifa.
Farida na zaune ba ta ce komai ba sai ma duba takardu da ke gaban ta da ta fara yi. Mr Ogonna ya cigaba da kumfar baki yana faɗawa sauran su sa baki, Farida ba ta da matsayin da za ta jagorance su balle har ta koreshi daga wannan meeting ɗin. Sai dai ba wanda yai magana. Sai kallon juna su ke su na magana da ido amma ba wanda ya furta wani abu.
Su na zaune har securities biyu su ka zo su ka fita da Mr Ogonna yana ta zage-zage.
Ta gane Mr Ogonna sarai, sau dayawa idan anzo meeting tun lokacin Najeeb yana ɗaya daga cikin wanda duk abinda aka faɗa sai ya kushe. Ya fi so ayi abinda ya zo da shi.
Najeeb bai cika sauraron sa ba, yana tashi zai yi magana Najeeb zai ce ya zauna. Wassu lokutan kuma sai ya bari ya gama bayanin sa sai Najeeb ya gwaleshi da cewa sun ƙayatu da labarin wasan kwaikwayon da ya gama ba su.
Mr Ogonna irin ma su son cigaban kan su kaɗai ne. Ba su da wani interest akan aiki indai ba zai jawo ya samu wani matsayi ko wani kamashon kuɗi ba.