SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Anty Farida kin san yau Lahdi ne ba a tashi da wuri”
Murya sama-sama ta fara magana. ” Tab! wato dan bana gidan shine aka watsar da dokokina ko. To ku sani Wallahi duk wanda ya san yau ranan aikinsa ne bai fito ba ganinan zuwa har ɗakin uwarsa in dakeshi kuma ba abinda zai faru. Zan irga uku ɗaya….biyu….” sai ga yaran suna fitowa daga ɗakunan su da gudu. Da ke sun manta tsarin da ta musu, kowa sai ya fito dan kar ya zama ranar sa ce kuma bai fito ba ta bishi ɗaki ta zane. Ba yau Farida ta fara zane yaran gidan ba, yanzu haka yadda su ke tsoronta ko su Yaya Yakubu iya kaci.
Maijiddah ta ɗan yi murmushi lokacin da ta ga ƙannen nata na fitowa da gudu.
………………………….
Ba tareda ya ɗago ya kalli Joseph ba ya ce ” three days” Joseph ya haɗiyi yawu moƙot saboda ba shi da ta cewa, amma taya kwana uku zai ishesa ya je Enugu burial na Maman sa ya dawo a kwana uku, bayan Enugun ma chan cikin wani ƙauye mai nisa su ke.
“Anything else?” Muryar Najeeb ta dawo da shi daga tunanin da ya ke. Joseph ya girgiza kai da sauri ya ce “no sir”. Da hannu Najeeb ya ma sa nuni da yai waje. Joseph ya bar office ɗin da sauri…
Tare su ka fita da Anas, sunje sun duba wani site da kamfanin su ke ginawa. A hanyar su ta dawowa Anas ya nuna yunwa ya ke ji dan haka dole su ka tsaya a wani restaurant da ke kusa.
Fiskar san nan tamau ta ke kamar bai taɓa dariya ba a tarihin rayuwar sa. A haka su ka shiga wajen cin abincin, shi idan ba dan Anas ba ba abinda zai sa ya tsaya a irin wannan waje. The restaurant is not even classy.
Sai da su ka zauna waiter ya zo dan ya ƙarɓi order ɗin su. Da sanin Najeeb ya faɗi wani kalar girki wanda baya cikin menu ɗin su. Saurayin ya ɗan tausasa murya ya ce “sorry sir, we dont have that in our menu”
Najeeb ya smirking ya ce ” then, water will be fine”
Har zai tafi Anas ya tsayar da shi ya ce ya kawo wa Najeeb irin abinda ya ordering.
“Seriously!” Najeeb ya faɗi yana ɗan girgiza kai.
“Mutumina kai fa ba engine ba ne, tun safe fa ba abinda ka ci. Gara ni naci ɗumame na ƙoshi kafin na fito, amma kai na san bayan tea ba abinda ka sa a baki”
“Did i complain?”
“Idan kai ba za kula da kan ka ba, i’ll help you do that”
Kafin a kawo abincin wayar Anas ta yi ringing ganin mai kiran ya sa ya ce da Najeeb yana zuwa. Fita yai daga wajen don ya samu daman magana sosai.
Wata budurwa da saurayi su ka shigo wajen cin abincin . Hankalin Najeeb na kan wayar sa dan haka bai lura da su ba, sai dai table ɗin da ke kusa da na su su ka zauna, da ke budurwar ce ta bashi baya dan haka bai ga fiskarta ba sai dai ya ga na saurayin lokacin da ya ɗago zai ɗau ruwan da waiter ya ajiye mishi.
Surutun da budurwar ke yi ya sa ya ƙara tsanar wajen saboda hayaniya da ta cika shi. Tukunnama, ta ya mace za ta dinga surutu haka in a public place kamar wannan. Tun da su ka shigo siririn muryanta ya gauraye wajen. Kafin saurayin da su ka shigo tare yai magana ɗaya budurwar ta yi ɗari. A haka Anas ya shigo ya same shi, su na fara cin abincin Najeeb yai tsaki ya aje fork da sokali sannan ya ɗau tissue ya goge bakin sa.
“Abincin bai ma ka ba ko?” Anas ya tambaya yana kallon sa. Najeeb ya ɗau ruwa ya kora batareda ya bawa Anas amsa ba. Tsakani da Allah ba wai abincinne bai ma sa ba, ba kuma yunwanne ba ya ji ba. Sai dai surutun wannan budurwane ya cika ma sa kunne. A rayuwarsa ya tsani hayaniya balle kuma yawar magana.
Kamar Anas ya gane damuwarsa ya ce a hankali “wannan yarinya ba dai surutu ba. Kamar radio”
Najeeb ya cigaba da danna wayarsa ba tareda ya ce komai ba…
……….
“Ka san Allah, idan na yi wata ɗaya a garinkun nan toyewa zan yi. Irin wannan zafi haka!. Da wayona Ray ban taɓa fin sati uku a Kano ba, ina ma zan iya”
Farida ta faɗi tana kora ruwa amaƙoshinta saboda tunda su ka zauna ta ke ta zuba surutu.
Rayyan ya ce “gashi ɗan Kano za ki aura ba”
“Ai ka ji inda matsalar ta ke, ina ga fa sai dai kai ka dinga zuwa Jos, dan ba zan tare a Kano ba. Tukunna Ray, wai a garin nan ka taso cikin wannan zafin?”
Rayyan ya langwaɓe kai dan wannan tambayar kusan karo na uku kenan da za ta yi shi a ɗan zaman su a wajen nan.
” My Farida mu ci abincin nan, zai yi sanyi fa”
A hankali ta fara tauna jollof rice ɗin wanda ko loma uku ba ta kai ba ta ajiye cokali. Ta yiwa wani waiter hannu akan ya zo.
Rayyan ya ma ta kallon mi ke faruwa amma ta kauda kan ta ta yi kamar ba ta gani ba.
“Waye ya girka abincin nan?” Tambayar da ta yiwa waiter kenan.
“Any problem ma’am?” Ya tambaya with politeness.
Farida ta kalli abincin ta kalle shi sannan ta ce “abincin ku shine problem ɗin ai. Na san wadda ta girka abincin nan ko tantama babu Bayarabiya ce. Idan ba haka ba taya za’a yi jollof rice a restaurant kuma a cika ma sa yaji. An gaya mu ku kowa ne ke son yaji? ko kuma dai so ku ke mutum ya ci ya koma gida yana gudawa. Da a garin da ba zafi ne sai ace ya yi dai-dai amma wannan Kanon na ku da shegen zafi kuma ku dafa abinci mai yaji kuna ba wa mutane. Mi ku ke nufi?”
Waiter ɗin bai gama fahimtar maganar Farida ba, saboda ba wani hausan kirki ya iya ba. Shekaran sa na uku kenan a Kano. Ya dai gane kalmar ‘Yaji’ dan haka ya ce ” ma’am with due respect, i dont think the food is pepperish”
Farida ta hangame baki ” Yo ƙarya na ke yi kenan?”
“Sorry ma’am”
Rayyan ya girgiza kai ransa a ɗan ɓace ya ce ” Farida dan Allah ki barshi haka, bari a kawo mi ki fried rice”
“A’a Ray, sai ya taɓa abincin nan ya ji dan ya tabbatar da magana ta”
Wani matashi wanda tun shigowar su Farida ya ke ankare da yadda ta cika wajen da surutu ya taso ganin dramar da ake yi.
“Haba Madam. Tun ɗazu ki ke damun mutane da surutu fa, kar ki manta nan public place ne”
Kallon sama da ƙasa ta ma sa sannan ta ce ” Malam sa’ido,gulma da munafurci. Kunnen ka bai jiyo surutun da ke fitowa daga TV ba sai nawa. Tsabar ha’inci ka bar matarka da cin garau-garau , ka zo ka tisa tumbinka a gaba kana cin fried rice da chicken, Allah wadai”
Kunyar da Rayyan ya ji ko wanda aka yiwa maganar bai ji ta ba. A ƙalla mutumin nan zai kai shekara Arba’in, amma Farida ba ta ga girman sa ba ta ke yaɓa ma sa magana.
Mutumin ya zuba ido yana kallon ta kawai tsabar mamaki.
“Kalleni da kyau Malam na fi ƙarfin ka, inma kana ƙungiyar mafiya ne to jinina fau-fau ya fi ƙarfin ka”
Mutumin ya kalli Rayyan ya ce “ɗan uwa gaskiya kana ƙoƙari. This girl is fire” sannan ya koma table ɗin sa.
Ta ce “Ba fire ba Volcano. Mtsww”
Ta kalli waiter ta ce “taste this food before i loose my temper”
Da sauri ya ɗau sokali ya ɗeba abincin ya taɓa. Irin masifan da ta yiwa mutumin nan wai ta ce ba ta loosing temper ba to idan ta yi ya za ta zama kenan.
Tabbas abincin ya ɗan fito da taste ɗin yaji amma bai kai har yadda Farida ta kururuta ba.
“Sorry ma’am, i apologise on behalf of our kitchen….”
Lokaci guda Najeeb ya miƙe tsaye hakan ya bashi damar ganin fiskar budurwar wanda alokacin ke yiwa waiter bayanin abinda zai kawo ma ta a madadin jollof rice mai yaji da su ka kawo. A yadda ta ke masifa ya ɗauka zai ganta gabjejiya sai ya ganta ‘yar mitsila bai fi mutum ya mangajeta ba amma sai shegen baki. Kallo ɗaya ya ma ta ya ɗauke idon sa ya fice daga restaurant ɗin.
A mota ya jira Anas wanda shi kam sai da ya ci yai naƙ sannan ya fito.