SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Daddy ku tsaya Sir Najeeb ya motsa yatsun sa yanzu” ta faɗa tana haki.

Daddy da Mom ɗin kowa sauri ya ke ya je ya ga shalelen ɗan na su.

Koda su ka zo ɗakin Najeeb yana nan dai yanda ya ke.
Kallon da Daddy ya ma ta ne ya sa ta san ba su yarda da maganarta ba

“Allah Wallahi Daddy ya motsa yatsun sa, Allah”

Tana maganan tana hawaye. Mom ta kamo hannun ta ta ce ” Farida it’s ok, addu’ar mu kullum shi ne ya tashi ɗin. You’re just hallucinating ki kwantar da hankalin ki, Bi izni kun fa ya kun zai tashi nan ba da daɗewa ba” jin haka Farida ta tubure akan wallahi Najeeb ya motsa yatsar sa. Ƙarshe dole aka kira likita wanda ya zo ya sa aka kunna mu su video footage ɗin wajen. Dama babban amfani na sa cctv cam ɗin kenan saboda a dinga bibiyar shi ko da zai iya motsawa ko ya farfaɗo ba tareda wani na wajen ba.

Lokacin da su Daddy su ka gani su ka gan hakan ne ta faru Najeeb ya motsa yatsun sa, farin ciki su ka ji marar misaltuwa tareda ƙara samun hope akan Najeeb zai tashi.

“Daddy zai tashi, yana so ya tashi Daddy zan ajiye aikin nan kar ya tashi ba na kusa da shi” ta faɗa tana goge hawayen da ke zubo ma ta.

Daddy zaunar da ita yai yana ƙara ma ta nasiha akan tashin Najee. Ko ta na kusa da shi ko ba ta kusa zai tashi Insha Allah, kuma zai fi jin daɗi idan har ya tashi ya ga ta kula ma sa da Kamfanin sa.
Ranan su Daddy ba su bar asibitin ba sai wajen ƙarfe sha biyu na dare.
Farida kam bayan sallah da ta tashi ta yi ba abinda ya sa ta ɗauke idon ta akan Najeeb gaba ɗaya daren ranan ji ta yi kamar zai buɗe ido ya ma ta magana. Ka sa bacci ta yi saboda kar ya buɗe ido tana bacci…

……………………..

Su uku ne su ka zo domin yin wannan yarjejeniya. A ɓangaren team ɗin Najeeb constructions kuwa su biyar ne Madam CEO tana tsakiyar su.

Dogon bayani Mr Smith yai wanda du ka bayanan sa kan yadda su za su fi samun riba ne ba komai ba. Da ya gama Mr Nokovic ya karɓa ya fara magana amma shi maganar da yai akan wai ba su yadda da shugabancin Farida ba ne.

Da su ka gama ta su bayanin Farida ta karɓa ta fara bayani.

” a duk bayanan ku abu biyu na fahimta. Na farko ba ku yadda na zama CEO ba na biyu kuma ku na son cire hannun jarin ku”

Mr Nokovic ya ce ” mu na son ƙara siyan hannun jari ba wai cire hannun jari ba”

“Oh really, ashe har kun tsorata kenan. Ni abinda na gani a rubuce shi ne kuna son ƙara siyan hannun jari ko kuma ku cire hannun jarin ku. So ni na riga na yadda maganan siyan hannun jari yanzu batun hannun jari da za ku cire za mu yi magana akai. So nawa za ku siyar ma na”

Kallon-kallon su ka farayi suna mamakin yadda lokaci guda ta juya abun kan su.

“Ba ni da lokaci da yawa, kaman yadda ku ka sani ina da majinyaci a asibiti wanda ke buƙatar kulawata”

“Mrs Jibo (ya faɗi jibon kaman wani Jaebo) mun san halin da kamfanin nan ke ciki ba za ta iya siyan shares ɗin mu ba.”

Farida ta yi murmushin yaƙe ta ce ” waya gaya mu ku Kamfani ba ta da halin siya. Ni nan ni zan siya kunga abu ya dawo gida kenan. So mu fara cinikin $200,000,000 mi ku ka ce?”

“Mrs Jibo” Mr Smith ya kira kafin ya ƙara da wani abu Farida ta ce ” $205,000,000 wannan fa?”

Shiru su ka yi dan ba su zo don su siyar da shares ɗin su ba dama burga da barazana ne kawai.

“Ku na cewa ba ku yadda na shugabanci wannan kamfani ba a wani dalilin? Saboda ina mace?”

Mr Vladimir wanda bai yi magana ba tun ɗazu ya ce “mun yarda ki shugabanci wannan kamfani a bisa sharaɗi ɗaya”

Farida ta ɗan gyara zama ta ce ” wanni sharaɗi”

Mr Vladimir ya ci gaba da bayani ” akwai bidding da za ayi a Abuja nan da sati huɗu. Manya-manyan kamfanoni za su shiga wannan bidding su submitting picth ɗin su saboda duk wanda ya ci contract ɗin, its worth billions. Sau ɗaya wannan kamfani ta taɓa winning contract mai tsada kamar haka, but wannan ya ma fi wanchan da aka yi a Lagos.
Mu na so ki yiwa wannan kamfani register ki kuma jagoranci wannan kamfani har ta winning wannan contract ɗin. Idan Najeeb constructions ta samu wannan project, mu mun amince za mu sayar mi ki 5% na shares na mu amma idan wannan kamfani ta shiga gasan nan ta faɗi to za ki sayar ma na da 10% na shares ɗin ki”

“Idan kuma na ƙi shiga gasar fa?”

“Za mu cire duka 11% shares na mu wanda ka iya kassara wannan kamfani saboda halin da ta ke ciki”

Tsawon minti biyu ba wanda ya sake magana. Sai murmushi turawan su ke ganin sun sa ka Farida a wani hali.

” Najeeb constructions za ta shiga wannan gasa kuma za ta ci Insha Allah”

Anas ya kalleta yana faɗin “Farida akwai matsala, ba za mu iya…”

” Ni Aisha Farida Mrs Najeeb Jibo, na amince za mu shiga wannan gasa kuma za mu ci da yardar Allah”

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣3️⃣4️⃣


Tana shiga office yana biyota.
“Farida kin san abinda ki ke faɗa kuwa, a halin da wannan kamfani ta ke ciki shine za ki samu cikin gasa. Do you have any idea irin manya-manyan kamfanin da za su shiga wannan gasa, ko da Najeeb yana nan chance ɗin winning is very low balle kuma baya nan”

“Ya Anas so ka ke na ƙasƙantar da mu a gaban yahudawan turawan nan?”

“A’a so na ke ki cire girman kai, ki ce ba za mu yi gasan ba. Idan sun cire shares na su ko Daddy za mu iya neman taimako a wajen sa”

“Ya Anas kenan, mutanen nan sun san mi su ke fa, ɗaurin goro su ka ma na. By all means so su ke mu faɗi, mu ji kunya. Ni ban shirya turmusa wannan kamfani a ƙasa ba”

Wannan karan a hankali yai maganar ya ce ” kin zaɓi a shiga gasan nan mu faɗi, Najeeb ya rasa 10% na shares na shi?”

” wanda su ke zama wani abu a rayuwa mutane ne that are willing to take risk. Ya Anas i’m a risk taker, ba na kallon 10% da za mu iya loosing, abin da na ke kallo shi ne 5% ɗin nan, kuma sai mun samu Insha Allah”

“Farida please, ka da ki yi haka. Ka da ki jefa mu cikin wani hali da zai kawo mu ga dana sani. Idan Najeeb ya tashi ya tarar ya loosing 10% na shi saboda ke he will never forgive you”

“Tun lokacin da ka hango nasara wa kan ka, to nasara tana tareda kai. Ya Anas za mu shiga gasan nan”

“Ba zan amince ba Farida, ba zan bari 7yrs of hard work ya crumbling a sati huɗu ba. Zan yi magana da Daddy za mu samu wata mafutar”
Har ya juya zai fita ta kira sunan sa ” Ya Anas”
Daga bakin ƙofan ya tsaya bai juyo ba.

“Daddy kullum cikin kashe kuɗi ya ke, ta ya zamu tuntuɓe shi da maganan maƙudan kuɗi haka. Ka san ko nawa ya ke kashewa a kowanni rana yanzu saboda Najeeb? Ka san ko nawa ya ke biya wa kowani kwana ɗaya da Najeeb ya ke yi a gadon asibiti. Da ceto rayuwan ɗan sa zai ji ko da ceto kamfanin ɗan sa?”

Anas bai yi magana ba ya fita daga office ɗin.
Ta jima a tsaye kafin daga baya ta je ta zauna, ba ta jima da zama ba Mrs Confort Masoyi sabuwar sakatariyar ta ta kawo ma ta wassu reports da za ta duba. (yeeeh mu ma muna da sakatariya????)…

Ranan gaba ɗaya Anas avoiding ɗin ta yai. Ita kan ta ta san cinye gasan nan abu ne mai matuƙar wahala amma kuma ba za ta janye ba, ai ance sai an gwada akan san na ƙwarai.

……………………….

Tun kafin ta tashi Daddy ya kirata akan idan ta tashi daga kamfani ta zo ta sameshi a gida. Tunda su ka yi wayan ta san Anas ya mishi maganar gasa ne. Ta ƙudira a ranta idan Daddy ya ce ta haƙura da gasan za ta haƙura tareda kuma ajiye matsayin da ta ke yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button