SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Ni ban amince da wannan ba Anas. Idan ku ka raba kan ku kuna ga kamfani zai cigaba ne? Ka koma aikin ka, idan ba za taimaka ma ta har ayi gasan ba, ka cigaba da kula da sauran harkokin ai”
“Daddy ka yi haƙuri dan Allah. Kawai dai…”
“Ba na son jin wani ƙarin bayani. Gobe idan Allah ya kaimu ka koma aiki”
“Insha Allahu Daddy”
Juyawa yai kan Farida ya ce.
“Ku haɗe kan ku Aisha, saboda a samu cigaba mai inganci. Allah ya shige mu ku gaba” ta amsa da Amin…
Tana cikin yiwa Najeeb taɗi sai ga Lukman ya shigo da sallama. Ledar hannun sa ya ajiye wanda ke cike da fruits.
“Barka da yammaci Aisha” ya faɗa lokacin da ya ƙaraso wajen ta.
“An wuni lafiya?”
“Lafiya, ya mai jiki?”
“Da sauƙi Alhamdulillah”
Shiru ne ya ratsa ɗakin na ‘yan mintuna kafin Lukman ya ce ” zan wuce Abuja gobe amma Insha Allah zan dinga neman ki na ji ya mai jikin”
“Na gode” ta faɗa tana maida kallon ta ga Najeeb…
Bayan ya fita ta kalli Najeeb sai ga hawaye ma su ɗumi shaar su na zubowa.
“Kukan na miye? Tukunna ma waye wannan?” Najeeb ya faɗa yana haɗa rai
“Lukman, Dr Lukman sunan shi”
“Ina jin ki, miye alaƙar ku?” ya faɗa yana ɗaga ma ta gira. Nan ta fara bashi labarin soyayyar su da Lukman da yadda ƙaddara ta raba auren su.
“So kukan anga tsohon zuma kenan”
Kaman da gaske da Najeeb ɗin ta ke magana ta fara girgiza kai…
……………………….
Anas dai ya dawo amma kowa harkan sa ya ke. Ya ce ba zai sa hannun sa a maganar gasa ba. Farida ma ba ta damu ba tunda ya cigaba da ayyukan sa…
Mr Ogonna ya shigo yana washe ba ki ” Madam an gama duk wani shiri, umurnin ki kawai ake jira”
“Ok, ka sa kowa ya hallara a hall” …
Details ɗin tsarin gine-ginen da za a yi ta nuna a projector.
“Ba ni da masaniya kan harkan gine-gine amma kuma akwai wanda su ka jima a harkan kuma za su taya mu zaɓe. Akwai kyauta mai tsoka ga duk wanda aka zaɓi zanen sa. Sannan duk wanda ya shiga gasan kuma ko da ba a zaɓe shi ba, aikin sa ba zai tafi a banza ba domin akwai kyauta na musamman da za a bashi.”
“Mr Ogonna zai gaya mu ku sauran baya nan” ta yi hakan ne saboda jiri da ta ji yana ɗiban ta. Da sauri ta bar wajen saboda za ta iya faɗuwa a wajen idan ba ta yi a hankali…
A ƙasa ta zauna dirshan saboda yadda ta ke jin kan ta na sarawa. Ta sani stress ne da yunwa ba komai ba. Gaskiya sai yanzu ta ganin jarumtar Najeeb, despite all this stress ba ya wani cin abinci mai yawa. Ta jima a zaune a wajen har sai da ta ɗan samu nitsuwa kafin ta je wajen fridge ɗin office ɗin ta buɗe. Maltina ta ɗauko ta fara sha saboda ko za ta samu ɗan ƙarfin jikin ta…
…………… …………..
Wanda su ka shiga gasan zane da Farida ta haɗa, kowa ya shiga aiki tuƙuru wajen ganin zanen sa ya fi na kowa fitowa, kwana biyar aka ba su kowa ya kawo zanen sa. Anas kan ido ya zuba ma su dan bai yi kaman ya san ana wani abu makamancin wannan ba.
Su Mr Ogonna kam ganin Farida na tsoma shi cikin harkoki sai ya zaƙe yana ƙoƙarin ya ga an gudanar da komai lafiya saboda ya san ya kusa samun ƙarin matsayi.
Ranan da za a fitar da wanda ya ci kuwa ga mamakin kowa sai su ka ga manyan professors ne har uku a wannan ɓangaren Farida ta kira wanda connections ɗin Daddy ne ya sa su ka amsa wannan gayyata.
Cikin mutum sha uku da su ka submitting zanen su kowa ya yi ƙoƙari sai dai mutum huɗu aka fitar wanda na su ya fi fice. Arch Hassan yai na ɗaya sai Arch Bashir na biyu sai Arch Yakubu na uku da kuma Arch Thomas na huɗu, na biyar kuma Arch Bazu.
Bayan an ba su kyauta sannan taro ya watse. Farida sai da ta sake tattaunawa da professors ɗin nan kafin su ka tafi. Ranan da aka yi wannan abin ma Anas ko wajen bai leƙo ba, hakan ya sosa ran Farida amma ya za ta yi tunda yanzu gaba ya ɗaura ma ta ba gaira ba dalili…
Da yamma waɗanda su ka yi na ɗaya zuwa na uku su ka hallara a gidan Daddy. Chan wajen gazebo su ka haɗu su ka tattauna yadda za a haɗa kai a sake gyara zanen Arch Hassan, wanda although ko shekara bai yi da fara aiki da Najeeb constructions ba yaron ƙwaro ne kuma ana ji da shi. Sau biyu Najeeb na sa shi a team da su ka yi zanen wani project da aka ba su tare…
Duk wani aiki da su ke yi a ɓoye su ke saboda gudun munafukai. Dukkan su ukun sun haɗa kai kuma sun fito da abinda ya bada mamaki. Wannan karan ba wanda ya ga wannan zane a kamfanin.
……………………
Baffa Musa ne ba lafiya shi ya sa ta je gida, rabon da ta je gidan ma ta manta. Jikin sa ya fara sauƙi dan kwana ɗaya yai a asibitin aka sallameshi, sai dai bai fara fita kasuwa ba.
“Farida kin gan ki kuwa?” Baffa Musa ya faɗa ganin yadda Farida ta dawo.
” anya za ki cigaba da wannan auren. Ance ma su laluran sa fa sai su ƙare rayuwar su a haka, wassu kuma ba su jimawa su ke mutuwa cikin dogon baccin na su”
Girgiza kai ta farayi tana hawaye.
“Wata uku da wani abu, anya zai tashi. Ƙarshen zuwa na fa yadda ya ke haka ya ke ba chanji”
“Baffa zan jira shi, ko shekara nawa ne, zan jira shi” ta faɗa tana fashewa da kuka. Tausayin Faridan ne ya kama shi. Shi yana ganin tunda ba auren soyayya su ka yi ba dama za ta iya haƙura da auren. Amma abinda idon sa ke gani yanzu ko da ace da Farida ba ta son mijin ta, to yanzu soyayyar sa ya ma ta mugun kamu. Dama miji da mata sai Allah…
“My Champ gobe za mu je Abuja, please be with me. Anas ya cire hannun sa ya bar min komai. But Alhamdulillah da taimakon Allah komai ya zo min cikin sauƙi”. Ta ɗauko wayarta ta fara buɗe wajen hotuna sannan ta nuna ma sa hoton wani zane. “My love ga zanen mu, Allah shi ne gatan mu. Please be with me ka ji” ta manna ma sa kiss a lips ɗin sa…
Ta jirgi su ka tafi Abuja inda su ka sauka a gidan Uncle Abubakar, Daddy ne ya buƙaci hakan. Farida , Yakubu da Hassan kaɗai su ka tafi, su za su representing Najeeb constructions.
Kwana uku za a gabatar da wannan bid ɗin. Saboda ba su yi register da wuri ba sunan kamfanin su ya faɗo a rana ta uku…
Lokacin da aka kira Najeeb constructions Farida ne ta fara tashi ta yi ƙaramin bayani kafin Hassan da Yakubu su ka buɗe modelling na su, su biyun ne su ka bada bayani kan yadda na su zanen ya ke da inganci da kuma sauƙi wajen tsari, tareda nuna yadda kamfanin su zai ba da mahimmanci wajen ganin ginin zai tafi dai-dai da yadda aka tsara.
Farida na zaune ne amma hankalin ta ba ya wajen tana kallon yadda Yakubu da Hassan ke bayani amma kunnen ta ba maganganun su ta ke ji ba. Addu’a ta ke yi a zuciyar ta, dan ta san idan su ka faɗi ba ƙaramin kunya za ta sha ba, sannan ga Anas wanda zai ma ta madallah Allah shi ƙara.
Ji ta yi an kamo hannunta, ta ɗaga ido da sauri dan ta ga waye, idon ta ya sauka kan Najeeb wanda ya ke ma ta murmushi.
“Take it easy Aysherh, I’m with you” murmushi ta farayi hawaye na sauko ma ta…
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣3️⃣6️⃣
Ranan Jumma’a aka ce za a sanar da wanda ya ci wannan gasa. Sun bar wajen da ɗan hope a zuciyoyin su, base on yadda aka yi mu su tambayoyi da kuma nuna jinjina garesu.
Su na zuwa gida lafiyar gado ta bi. Ɗakin Afrah aka ba ta su Yakubu kuma ɗakin baƙi. Tana kwance zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Tana kwance sai rawan ɗari ta ke Najeeb ya shafa fiskarta ya ce “sorry love, zazzaɓi ko?”
Ta gyaɗa ma sa kai. Ɗaukan jakan ta yai ya fito da wayanta da ke ciki ya danna numban Yakubu ya sa ma ta a kunne.