SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

” Hello, Yakubu dan Allah ka zo banda lafiya” ta faɗa tana tura wayan gefe.
Najeeb ba ya wajen ita ɗin ce dai ta ɗauko wayan.

Bai jima ba Yakubu ya shigo ɗakin, har lokacin tana rawan sanyi. Dai-dai lokacin wayan Faridan ya fara ringing Yakubu ya ɗau wayan ya ga Dr Lukman.
Amsa kiran yai su ka gaisa ya ke ce ma sa Farida ba lafiya zazzaɓi na damunta. Lukman ya ce ya turo ma sa address ɗin gidan zai zo.

Da su ka gama wayan ya kalli Farida ya ce ” za ki iya jiran Dr Lukman ko kuma mu kai ki asibiti?”

Da ƙyar ta iya cewa za ta jira shi. Yakubu ya fita ya je ya sanar da mai aikin gidan akan ta haɗawa Farida tea…

Lokacin da ta buɗe ido Najeeb ta gani zaune yana karanta wani magazine.

“Sir Najeeb” ta faɗa a hankali

“Kin tashi, ya jikin?”

“My champ zan sha ruwa” ta faɗa tana ƙoƙarin tashi duk da kuwa hannun ta da canula an ɗaura ma ta ruwa.

“Kwanta za’a kawo miki ruwan”
Riƙe rigan sa ta yi da ɗaya hannun da ba canulan ta ce “kar ka tafi ka barni my champ, zan mutu idan ka barni, please my love”

A hankali Lukman ya gyara ma ta kwanciya ya ce ” ba zan bar ki ba”
Sai da ya ga ta sake komawa da bacci kafin ya fita daga ɗakin. Har yanzu yana son Farida, duk da kuwa ya sani sarai ya rasa Farida har abada. But seeing her like this breaks him. Tana tsananin son mijin ta, son da ta ke mishi ko lokacin da su ke soyayya bai yi tunanin ta ma sa rabin son da ta ke wa bawan Allah nan ba.

Sai yamma lis kafin Farida ta farfaɗo da kyau, ta dena ganin duk wanda ya shigo a matsayin Najeeb.
Bayan Isha ta fito falo saboda ta gajiya da zaman ɗaki da ta yi, kuma yanzu tana ɗan jin ƙarfin jikin ta.

Yakubu ne ya ce ma ta Mr Hafiz Olabode ya kira ta kuma ya ce su haɗu gobe ƙarfe tara na safe.

Yakubu ya ƙara da cewa “Mr Olabode yana ɗaya daga cikin wanda za su judging pitch ɗin nan. Na san ƙila cewa zai yi ki bashi wani abu dan ya voting zanen mu. Kin san yanzu komai ɗan bin ƙafa ne, ka bribing officials na Gomnati a baka contract”

Hassan ya ƙara da cewa “mu addu’a za mu musu amma gaskiya bribe ake bayarwa, wanda ya fi ba da kaso mai yawa a bashi”

Farida kan jin su ta ke amma ita kaɗai ta san mi ta ke ji…

Washe gari tareda Yakubu su ka je wani classy restaurant da Mr Olabode ya ce su haɗu. Ɗan gefe da su Yakubu ya zauna.

Yadda su Yakubun su ka faɗa hakan ta ke Mr Olabode ya ce ma ta zanen kamfanin su na ɗaya daga cikin wanda ya burge su, sai dai idan tana so sun cinye komai gaba ɗaya to ta yi abinda ake yi.

Kai tsaye ta ce ” ba kuɗin da zan bayar”

Mr Olabode yai murmushi ya miƙo hannun sa ya ɗaura akan na ta hannun yana faɗin “who is talking about money, when this heavenly beauty here is everything…”
Saukan mari da ya ji ya sa sauran maganan su ka kafe a bakin sa.

Ba ta tsaya haka ba ta ɗau juice ɗin da ke gaban ta ta watsa a fiskan shege. Ta ɗau jakarta ta fita ta bar Mr Olabode da buɗe baki.
Yakubu na jin ƙaran mari ya kalli wajen da su Farida ke zaune. Tana tashi ya bi bayan ta da sauri.

“Kuɗi ya ce ki bashi ko?”

“Wani kuɗi kuma, kana ganin baƙin kwarto a wajen”

Yakubu ya ce “Allah ya shige ma na gaba amma na karaya”

“Indai har sai mun ba da cin hanci da mu ci gasan nan to na haƙura. Mu koma gida kawai, ma san yadda za mu ɓullowa su Mr Vladimir”…

Yammacin ranan Lukman ya zo duba ta. Ya ji daɗin yadda ya ga ta murmure sosai. Da ya je ma ya samu tana ta masifan abinda Mr Olabode ya ma ta ne. Wai har Mr Olabode mai kaman angulu shi ne zai kalleta ya tsaya yana ma ta maganan banza. Uncle Abubakar ya ce ” to ai yadda ƙasar na mu ta koma kenan. Give before taking ake yi”

Farida ta ce “dole ai ba za mu taɓa cigaba ba. Cin hanci da rashawa ya mana katutu”…

Sai da ta rako shi bakin mota sannan ya ce ” so, yanzu gobe ba za ku jira ku ji result ɗin ba”

“Dr Lukman kenan, ka na ga bayan abin da na yiwa Mr Olabode za ma a saurare mu balle kuma ace mu mu ka ci gasa”

“You never know Aisha, ai ba shi kaɗai zai judging ba. Dan Allah ki je, ko da ba ku samu ba dai ya nuna kuna da jarumta you stayed till the end”

“Shi kenan” amma da ni na cewa su Yakubu gida za mu wuce gobe”…

Bayan Lukman ya shiga mota ya tafi sai ta ga Najeeb na tsaye ya harɗe hannun sa a ƙirji fiskar sa ba walwala.

“My champ lafiya ka haɗe rai? Ka min murmushi dan Allah”

“Aysherh ba na so, na ce ba na so” daga haka ta dena ganin sa ko na ce ya ɓace ma ta a idon ta…

Washe gari Jumma’a su ka je inda ake taron. Wassu ba su zo ba dan yanayin yadda ka ke jin kanada hope shi zai sa ma ka tsaya tunda dai mutum ɗaya ne zai ci.

Farida na zaune hankalin ta kwance ga Najeeb na gefen ta hannun su sarƙe cikin juna. Sai Yakubu da Hassan da kowannen su ya sha suit kaman a ranan za su yi pitching zanen su.

Mai gabatarwa ya gabatar tareda nuna jinjina ga duk wanɗanda su ka shigar da zanen su haƙiƙa kowannen su ya yi ƙoƙari. Amma akwai wani zane guda ɗaya wanda ya ɗau hankalin mu ba wai dan ya fi na kowa ba sai dan yadda tsarin zanen ya tafi da zamani kuma still its just simple tradional design. Haƙiƙa wanda su ka tsara zanen nan sun yi ƙoƙari. Mafiyawancin lokuta abun da bashida yawan ƙyale-ƙyale shi ke ɗaukan hankali. To mudai wannan zanen ya ɗauki hankalin mu. Harta baturen da ke cikin mu Mr Briston ya yaba da wannan zane matuƙa kuma a karan kan sa ya bada kyauta ta musamman ga wanda su ka yi wannan zane. Kafin na cika ku da surutu za mu kira Mr Briston ya faɗi kamfanin da su ka lashe gasan nan.

Duk yadda Farida ta so daurewa sai da ta dinga jin ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri.

Baturen Mr Briston ya hau stage ya fara bayani da turancin sa da ta ke kama da ta hanci ta ke fita.
Farida ba jin komai ta ke ba dan kunnen ta ya toshe a wannan lokacin.

Firgigit ta yi lokacin da muryan Mr Briston ya doki kunnen ta yana faɗin “we’ve selected the design presented by Najeeb Constructions company. I here by called on the team leader Mrs Farida Jibo of Najeeb constructions to come…”

Yakubu ne ya dafa kafaɗar Farida yana faɗin Alhamdulillah, ‘yar uwa Alhamdulillah.

Ƙwaƙwalwarta ba abinda ke yawo ciki sai ‘Najeeb constructions company’

“Farida ki tashi, ki tashi ana kiran ki” muryan Yakubu ya dawo da ita daga nisan kiwon da ta yi.

Sai da ta miƙe tsaye Najeeb da ke wajen ya kalleta ya ce “ni ba na son ƙauyenci, walk with class and elegance Mrs Jibo”

Hannun ta ya kama ya ce mu je na raka ki. Tafiya su ke tana jin kan ta a sama, ga shi sun lashe gasa ga Najeeb a kusa da ita.
Yakubu da Hassan kam kallon yadda ‘yar batalikan nan ke tafiya su ke. Tana tafiya kaman wanda ta ke jin tsoron taka ƙasa…

Akwai daɗi fa ka representing mijin ka a wani waje, musamman wajen da ake ganin kaman matan aure ba su da wani daraja da ya wuce su zauna a gida su yi girki.

Yakubu da Hassan kuwa Mr Briston kyautar kuɗi naira dubu ɗari biyu ya basu.

Ba ta taɓa jin daɗin a kirata da Mrs Jibo ba irin yau. Ko ina ta juya sai congratulations Mrs Jibo ake ta faɗi. Su na barin wajen Daddy ta fara kira dan tun jiya da ya kirata ya tambaya ko akwai wani haske, ce ma sa ta yi ita ta haƙura za su dawo gida kawai.
Daddy ya ji farin ciki sosai. Na farko 5% zai dawo hannun Najeeb sannan ga yadda kamfanin za ta sake samun ɗaukaka a ƙasar…

Da dare text ɗin Anas ya shigo
congratulations, ba ni da bakin magana Farida. Kin ƙara tabbatar min da maganar Najeeb da ya ke yawan gaya min cewa ‘duk inda akwai tsoro to babu nasara a wajen’ Allah ya dawo da ku lafiya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button