SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Farida ta yi tsaki ta ce daga baya kenan, wai anyi sadaka da bazawara. Haushin sa ta ke ji yanzu ko da ace bai so ta shiga gasan ba amma tunda ta riga ta shiga sai ya sa hannu ya taimaka wajen ganin an yi iya ƙoƙari akan abin. Amma ya bar ta tana ta wahala ita kaɗai.
Ba su dawo ba sai ranan Tuesday saboda sai da su ka tsaya ranan monday aka yi cike-ciken contracts document.
Daga airport da aka zo ɗaukan su cewa ta yi a wuce da su asibiti, kafin ta ga kowa sai ta ga lafiyan mijin ta.
Tare su ka wuce asibitin dan su ma rabon su da Najeeb ya fi wata ɗaya.
Tana shigowa ɗakin ta ga Sabreen tana kissing goshin Najeeb har da hawayen munafurci a idon ta tana faɗin.
“Noory i have to go, i’m sorry, but this movie means alot to me. I’ve always wanted to work with Keanu Reeves and now i got the chance. Please forgive me. I’ll come back for you after the shooting….”
Farida ta kama hannunta ta ja ta gefe. “Ba ya son jin komai daga gareki, so just go”
“If he wakes up Aisha, i’m going to do anything just to get him back. I promise”
“mtsssw aikin ɓur inji tusa. Ki wuce ki bamu waje karuwan banza karuwan wofi”
Sai da ta ɗau jaka ta tafi su Hassan su ka fara dariyan maganar ta.
Farida sai da ta goge wa Najeeb fiska kafin ta kissing ɗin sa tanajin haushin kissing ɗin da Sabreen ta ma sa.
“My Champ we got the contract, thank you for being with me”
Jin Farida ta manta da su a ɗakin ya sa su Yakubu su ka ma ta sallama su ka fita wanda ko iya amsawa ba ta yi ba dan hankalin ta gaba ɗaya na kan hiran da ta ke yiwa Najeeb…
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣3️⃣7️⃣
Tana tareda Najeeb, Anas da Daddy su ka shigo ɗakin.
“Masha Allah ‘ya ta Allah ya mi ki Albarka” Daddy ya faɗa lokacin da ya ƙaraso.
Ta amsa da Amin tana murmushi.
“Son ka ga abinda matar ka ta yi ko? She is a fighter, she’s a winner. Matar ka iron lady ce. Ka tashi ka ji, ka tashi ku gina rayuwar ku tare” ya kissing goshin sa yana shafa gashin sa.
“Daddy Mom ta dawo?”
“Sai next week” ya amsa ma ta.
“Allah ya dawo da ita lafiya”
Su ka amsa da Amin.
Anas kam kunya ta hanashi magana sai kau da kai ya ke. Daga baya Daddy ya bar su ya ce zai je yai magana da likita.
“Ya hanya” Anas ya katse shirun na su.
“Alhamdulillah mun je lafiya mun dawo lafiya. Sauro bai cize mu ba haka Cinnaka ba ta cize mu ba balle ayi tunanin mun wahala. Kuma dai girma ya faɗi”
“Farida dan Allah ki yi haƙuri. Na san ba ni da hujja akan abin da na aikata amma ki yi haƙuri ki yafe mun”
“Ya Anas a nan ka zo ka roƙe ni Allah Annabi akan na zama CEO amma mi ka yi bayan na zama CEO. Ka bauɗe min, ka ƙi goya min baya har ka na ganin gara ka bar aikin da zama na CEO ko?”
“Ba haka ba ne Farida, kawai dai ba na so kamfani ta shiga matsala ne”
“Da kyau, saboda ga Aisha Farida mai farar ƙafa ko?”
“Duk abinda ki ka ce i deserve it. Ban riƙe amanar abokina ba, i’m truly sorry”
“Ka san mi ake cewa namiji matsoraci? To Ya Anas kai matsoracin namiji ne kuma ragon namiji. Idan ba ka dena sa tsoro a lamurran ka ba to ba inda za ka je a rayuwa. Kuma ko a gidan ka za ka samu matsala. Kana ganin da ina da tsoro zan kai yadda na kai da Najeeb, ka san da ni matsoraciya ce da tun ranan da Najeeb ya koreni da na bar aiki a kamfani kenan. But i fight back, na nuna ma sa ni ba ƙwallo ba ne da zai dinga bugawa duk lokacin da ya ke so. Ka san miyasa Najeeb ya ka sa korata? Because he needs me. Najeeb na son mutum mai zafi, mutum da ba ya da tsoro ko kaɗan”
Ya ji haushin kiran sa rago da ta yi amma kuma gaskiya ta faɗa, sau tari ta inda su ke samun matsala da Najeeb kenan.
“Ki yi haƙuri dan Allah”
” na ji haushi kuma har yanzu ina jin haushin ka. Ka bani lokaci na huce tukunna”
“Ba komai, amma dan Allah ki yafe min”
“Na yafe”
Ba su sake wani maganan ba har Daddy ya dawo su ka tafi.
“My champ ka ga abokin ka ko, ka ganshi ko” …
………………….
Washe gari tana shigowa kamfani aka fara tafi, ana ma ta congratulations.
Duk wanɗanda su ke ma ta wani gani-gani to yanzu sun sha jinin jikin su. Madam Farida kamar yadda yanzu aka fi kiran ta ta zama Boss lady. Tundaga lokacin da ta ƙarɓi matsayin CEO kowa ya shiga taitayin sa saboda ita ma zafi gareta kamar Najeeb. Wani zubin ma gara Najeeb ɗin dan shi idan ya ma ka tsawa shi kenan amma wannan sai ta bika da baƙar magana wani lokacin idan ta yanko ma ka magana sai ka ji kamar ka kama kai ka rusa kuka.
Ga wanda ya bita sannu kuma tana da sauƙin kai…
Su Mr Vladimir bayan ya tabbata Farida ta leading team kuma anci gasa ba ƙaramin baƙin ciki su ka yi ba. Neman sulhu su ka fara yi dan kar su rasa 5% da au ka yi alƙawari amma kuma Farida ta ce bata san zance ba. Su su ka faɗi sharaɗi kuma dole su bi shi yadda ya ke. Haka dai ba tareda sun so ba su ma sa hannu a takardar da ke shaidar sun ba da 5% shares ɗin su a Najeeb. Ranan Farida sai da ta yi hawaye saboda hango farin cikin da ta yi a idon Najeeb idan ya farfaɗo ya ji abinda ta yi…
………………….
Gidan AbdulWahab kam yanzu zaman lafiyan ba kamar da ba. Tunda Aneesa ta dawo Lagos da aiki sai komai ya chanja. Kullum cikin taƙalar Maijiddah ta ke yi, duk da ma yanzu Maijiddan ta dena tsoron ta kuma ta na ɗan maida ma ta magana amma still wassu lokutan shiru ta ke ma ta. Aksarin lokaci Maijiddah tana burin inama ace itama ta iya magana kaman Farida da za su dai-dai ta tsakanin ta da Aneesa.
Haka kawai ta hana yaran shiga harkan ta, duk da yaran na so amma abinka da uwa da ɗa sai ya zamana ta yi musu tsawa shikenan. Ɗan gara ma Alizah wani lokacin tana ƙin bin umurnin Maman na su.
AbdulWahab na iya ƙoƙarin yin adalci tsakanin su duk da ma yanzu Maijiddah ta fara ganin chanji a tattare da shi lokacin da Aneesa ta dawo. Tana renon cikin ta lafiya amma wani lokacin gani ta ke tunda Aneesa ta dawo kaman yanzu AbdulWahab ya rage ba ta kulawa da kuma ɗokin cikin da ta ke ɗauke da shi.
Cikin ta na wata bakwai Aneesa ta fara laulayin ciki. Ta gano hakan ne ranan su na zaune suna cin abinci ta fita da gudu tana amai a banɗakin da ke guest room.
Daga baya kuma Aneesan ta fara tsirface-tsirfacen abubuwa irin na ma su ciki.
Lokaci guda hankalin AbdulWahab ya koma kan Aneesa. Ranan su na cin abinci da ke Maijiddan ne ta yi girki, Aneesa ta fara kushe abincin akan an hana ta yawan cin mai a asibiti kuma ga shi abincin Maijiddan ya cika mai.
“Sweetheart ba ka gaya ma ta abinda likita ya ce ba ne?” Ta faɗa tana kallon Maijiddah.
“Anny zan gaya ma ta ba yanzu ba akwai yara a nan”
“Na san ba za ka iya gaya ma ta ba. To Malama Maijiddah ciki ne da ni kamar yadda ki ka sani, kuma likita ya ce saboda mahaifata tana da rauni na guji aikin wahala da yawan stress na kuma rage cin wassu abubuwa saboda kar cikin ya zube. Sai ki kiyaye nan gaba”
Maijiddah ta buɗe baki da hanci tana ganin wannan cin fuskan. Ƙarin haushin ma AbdulWahab bai yi magana ba.
Ajiye cokali ta yi ta bar wajen. Da ya ke kwanan ta ne AbdulWahab da ya zo sai ya ke ƙara gaya ma ta report ɗin da likita ya ce gameda cikin Aneesa.
Haushi ya kawo ma ta har wuya, ka sa shiru ta yi ta ce “amma Abban Alizah ni ma fa ciki gare ni kuma ko da babu likitan da ya gindayamin sharaɗi, dai a matsayin da na ke yanzu ina buƙatar kulawa ta musamman”