SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Hauwerh dont get me wrong please, ba wai ina nufin ke baki buƙatar kulawa ba ne…”
“Sai yanzu na gane gaskiya. Dama saboda matar ka ba ta nan ka auro ni, to yanzu ta dawo ban da matsayi ko?”
“Shhhhh, kar ki sake faɗin haka Hauwerh ki na da matsayi babba a rayuwata”
” a rayuwar ka haka ne amma a zuciyar ka Anny ce kaɗai”
Kamo hannun ta yai ta wafce hannun.
“Plz Gimbiyata, ki yi haƙuri. Ki na da matsayi a zuciyata da rayuwata gaba ɗaya”
Ranan dai AbdulWahab da ƙyar ya shawo kan amaryar sa…
…………………
Ko mi zai ma ta ba za ta koma Lagos ba. Gara ya dinga zuwa yana dubata duk ƙarshen wata. Ta bar mu su waje su sakata su wala yadda su ke so. Sai da motar su ta ɗau hanya sannan ta jingina kanta da seat tana hawaye. Babbar motar Macapolo ta shiga da zai je Kano daga Lagos. Duk da kasancewa dare ne hakan bai sa ta ji wani fargaba ba. Su na tafiya tana tuno maganganun AbdulWahab…
Sai da su ka dawo daga asibiti sannan ya je ɗakin Maijiddah dan ya bata haƙuri tsawan da ya ma ta ɗazu. Ya sani sarai bai kyauta ma ta ba. Duk abinda ya faru bai kamata ya gaya ma ta magana haka ba.
Wayam ɗakin ba kowa. Ya duba ko ina ba ta nan. Mai aikin su dama ba ta nan ta yi tafiya. Fita yai ya je ya samu mai gadi inda ya sanar ma sa Maijiddah ta fita. Faɗa ya fara ma sa akan miyasa zai barta ta fita ita ɗaya da tsohon ciki. Maigadi ya ce shi ya je ya samo ma ta taxi ma domin kuka ta ke yi ta ce an musu rasuwa ne za ta je gida kuma kai ka ce ta tafi saboda kun fita da Madam Babba.
Tsaki yai ya koma ciki. Ya kira numbarta sau ba adadi amma a kashe. Ba dai Maijiddah gida ta tafi ba.
Aneesa na kwance sai nishi ta ke ita a dole ta yi ɓarin ciki kuma kishiyar ta ce sanadi. AbdulWahab ya shiga tashin hankali sosai ina ya san zai nemi Maijiddah da daren nan…
Washe gari da safe ya samu labarin ta shiga mota ta tafi Kano. Kiran Hajiyar sa yai dan ya ji ko ta iso sai ya ga Hajiya ba ta ma sa maganar ba sai ma tambayar sa da ta ke ina Maijiddah. Sai alokacin ya waske da cewa ai tana hanyan Kano ma yanzu.
“Ko kai fa amma ka ce wai ta zauna a chan ta haihu”
Dama Hajiya Yelwa ta nemi ya bar Maijiddah ta haihu a kano ya ƙi shiyasa ba ta kawo komai aran ta ba.
Ƙarfe goma na safe su ka isa Kano inda direct gidan su mijinta ta wuce. Yanayin yadda Hajiya Yelwa ta ganta ya sa ta gane ba tafiyar jirgi ta yi ba.
“Lafiya Hauwa na ga kin kumbura, duba ƙafafuwan ki”
“Ba komai Hajiya zama ne kawai ya sa yai haka”
Hajiya Yelwa ta kira AbdulWahab tana ma sa faɗa akan barin Maijiddah da yai ta zo ita ɗaya sannan a mota ba a jirgi ba.
Hamdala yai lokacin da ya ji Maijiddah ta isa gida lafiya. Ya bawa Hajiya haƙuri akan ayyuka su ka ma sa yawa.
“Hajiyata ki ɗan bawa Hauwa wayar na kira numbar ta baya shiga ina ga wayan ya mutu ne”
Hajiya ta miƙawa Maijiddah wayar wanda ganin idon Hajia ya sa ta karɓa.
“Haba Hauwerh kin min adalci kenan, idan wani abu ya same ki fa.”
“Na isa gida lafiya a gaida marar lafiya” ta kashe wayan saboda Hajia ta fita a ɗakin…
Kwanan ta na uku sai ga AbdulWahab. Tana zaune tana cin abinci a ɗakin Hajia sai ga shi ya shigo.
Ganin sa da ta yi sai da ta ɗan yi jim amma ta dake.
Zuwa yai ya zauna gefen ta ya kamo hannunta ɗaya ya ce “Gimbiya ta haka kike da zuciya dama. Haba dan Allah, kin san ina son ki kuma ba zan taɓa yin abinda zai ɓata miki dai ba”
“Amma ai ka yadda ai lokacin da matarka ta ce na tureta ta faɗi. Na yi sanadiyar rasa cikin ɗan Lele ko”
“Na san na yi kuskure Gimbiyata a min haƙuri”
Namiji dai da daɗin baki haka ya gama kwantar ma ta da hankali da kalamai ma su daɗi. Dole dai ta miƙa wuya ta haƙura ƙarshe ma ita ta koma tana bashi haƙurin kan tahowa da ta yi cikin dare ba tareda ya sani ba…
Washegari ya tafi dan ya san tunda ta riga ta zo sai ta haihu tunda dama tun farko Hajiya Yelwa ta nemi hakan…
…………………..
Sati biyu da zuwan Maijiddah kano ta haifo santalelen ɗan ta mai kaman uban sa. Haihuwan nan ya sa Aneesa ta tada daru akan AbdulWahab dole ya bi ma ta hakki tunda Maijiddah ce ta yi sanadiyar zubewar cikin ta. Shi kam bai biye ma ta ba dan sai a lokacin yake ganin wautarsa ranan. Domin ya san Maijiddah ba ta da faɗa kuma yadda ta ke ɗan jin tsoron Aneesa haka kawai ba za ta tureta ba dan dai maganar fatar baki. Balle Maijiddah na da tsohon ciki ita kuma Aneesa cikin ma wata biyu ne.
Ana saura kwana biyu suna ya tattaro yaran sa su ka zo Kano. Aneesa kam Abuja ta wuce ta ce ba za ta je sunan ba…
Daga gidan suna ta wuce asibiti.
“My Champ ka ga babyn Maijiddah kuwa? Wallahi kyakykyawa da shi. Ka tashi muma mu yi abubuwa na samu ciki na haifi Baby mai kaman ka. Ka ji miji na”
Ta ƙara kissing hannun sa tana faɗin “sunan Babyn na su Muhammad Al’amin, nima My Champ ina son suna Muhammad. Sunan ɗan mu na farko kenan Insha Allah”…
Ƙarƙashin jagorancin Madam Farida Najeeb Constructions ta samu cigaba sosai kuma an samu gyararraki kan abubuwa dayawa.
Yau ma wassu baƙi ta ke meeting da su da su ka zo daga Kaduna.
Tana shiga office ɗin ta Anas ya shigo.
“Farida ba ki sa hannu a wannan takardan ba”
Ya miƙo ma ta wani takarda. Ta ƙarɓa ta yi signing sannan ta miƙa ma sa.
Tana zama sai ga kiran sakatariyar ta.
“Hello Madam, Mr Rayyan Abdullahi is here to see you should i send him in?”
“Rayyan Abdullahi?”…
Mi Rayyan zai zo yi wajen ta. Rabon ta dashi tun ranan da ya zo office ɗin ta Najeeb ya ma sa kora da hali…
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣3️⃣8️⃣
“Faridah” muryan Rayyan ya doki kunnen ta. Ta ɗan ɗago ta kalleshi, kallonta ya ke yi mai cike da ma’anoni.
Da yatsar ta ta ma sa nuni da ya zauna ba tareda ta kalle shi ba. Har ya zauna bai ɗauke idon sa a kan ta ba. Ita kuwa tunda ta ɗago sau ɗaya ta maida kan ta ga takardun da ta ke dubawa.
“Farida” ya sake kira
Ta ɗago kai tana juya biron da ke tsakanin yatsunta biyu.
“Mr Rayyan what can i do for you?”
“Farida ni ɗin, ni ɗin ne Mr Rayyan” ya faɗa yana nuna kan sa.
” ok to Malam Rayyan mi zan iya ma ka”
“Lallai duniya!”
“As you can see aiki na ke yi. Idan ba ka da abin faɗi dan Allah ka ƙara gaba”
Jijjiga kai yai sannan ya ce “ya jikin Mijin ki?”
“Alhamdulillah da sauƙi”
“Stop pretending Farida, waye bai san halin da Najeeb ya ke ba a garin nan. He’s being in coma for months now, ba alaman zai farfaɗo balle…”
“Balle me? Balle me?” Farida ta daka masa tsawa.
“Kwantar da hankalin ki Farida ba faɗa na zo ba. Ina so ki sani cewa har yanzu ina son ki kuma ina son auren ki. An sa aure na da mai sunan ki nan da 2 months. Amma na roƙi Umma ta bar ni na aure ki bayan na auri ‘yar uwata Aishatu kuma ta amince. Kin ga by the time kin gama iddah sai mu maida auren mu”
“Ban san ka da shan giya ba Rayyan, ko dai ka fara ne bayan rabuwar mu?”
“Farida ke kan ki kin san har yanzu ina son ki…”
“Rayyan idan ba giyan wake ka sha ba ya kamata ƙwaƙwalwar ka ta gaya ma ka ni matar aure ce, ni matar Najeeb ce”
“Wanni Najeeb ɗin, Najeeb da ke chan kwance kamar gawa. How long has it being, kusan 8 months fa”
“Yes Rayyan. Yana chan kwance for 7months 9 days, kuma zan jira shi ko da zai ɗau shekaru kafin ya farfaɗo. I love him and i will wait for him till the end of my life. Get that into your thick skull Rayyan” ta faɗa tana miƙewa tsaye.