SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Far…”

“Leave!” Ta daka ma sa tsawa

“Farida ki…”

“Get out! Ka fita na ce!” Yadda ta yi tsawan wannan karan sai da ya ɗan tsorata.

Ba tareda ya sake yunƙurin magana ba ya tashi ya fita.

Zama ta yi ta fashe da kuka. Miyasa kowa ke ganin Najeeb ba zai tashi ba, miyasa su ke ganin a haka zai ƙarasa rayuwar sa. Haka jiya da su ka yi waya da Ummi ta ke ce ma ta ance ba lalle Najeeb ya farfaɗo ba, ko za a raba auren su. Miyasa ita ba ta gaji da jiran sa ba amma su sun gaji. Akwai wanda ta farfaɗo daga coma bayan shekara ishirin, ko da Najeeb zai shekara ishirin a haka za ta jira shi. Balle ta san ya na chan ya missing ɗin ta yana ƙoƙarin dawowa gareta…

…………………

A gajiye ta shigo ɗakin na su saboda aikin abincin sadaka da su ka yi. Duk Jummu’a ita ke zama da su Adama su girka jollof rice da naman rago su sa a take away guda dubu a kai wa almajirai da mabuƙata. Kullum sun sa ana mu su sadakan kunu da ƙosai da Masa.
Mom ma ba a barta a baya ba wajen sadaka. Ranan su Adama su ka tayata fitar da kusan duka kayayyakin ta da ke closet, wassu kayan ma ba ta taɓa sakawa ba, ga su kaya ne ma su matuƙar tsada, ta sa aka rabar sadaka. Mutum goma ta biyawa Umurah da lokacin azumi. Shi Daddy kam ba irin sadakan da yai Allah ne kaɗai ya san adadin sa. Ba wai dama ba ya taimako ba ne, amma abinda ya faru ya sa ya ƙara buɗe hanyoyin taimakon al’umma…

A Desk ɗin sa da ya ke zama yai aiki idan yana ɗaki ta zauna. Wani brown envelope ta gani, ta jawo shi. Wayoyin Najeeb ne guda biyu a ciki. Sai yanzu ta tuna cewa ita ɗin ce ta saka a wajen ranan da Anas ya kawo ma ta. Anas ya sa an buɗe wayan domin a duba wassu saƙonni. Ko lokacin da za aje Bank da Court wajen authorizing signature ɗin ta ya zama bayan Najeeb da Anas har da na ta signature ɗin wajen sarrafa abubuwan Kamfani har da wayan nan aka je. Ta tuna sai da ta yi rantsuwa a kotu sannan aka gama haɗa komai, abin tausayin ma maimakon signature ɗin Najeeb dole thumb print na sa aka sa.
Ranan da Anas ya kawo wayan tunda ta ajiye su a kan table ɗin ba ta sake bin kan su ba.

Ta ɗauki babban wayan ta kunna. Hoton sa ne a screen ɗin duk da ma screen ɗin ya ɗan tsatstsage. Ta ƙurawa hoton sa ido, ta sa hannu tana shafa kyakykyawan fiskar sa. Ta shiga gallery tana kallon hotuna wanda yawanci hotunan zane-zane ne, sai wani folder wanda hotunan Najdah ne da hotunan sa wanda su ka ɗauka da Anas wassu kuma da Daddy. Allah sarki ya yi hoto da yawancin ‘yan uwan sa amma ba hoton Mom ko guda ɗaya a wayan da ta gama ta koma kan text messages ta ga duk yawanci alerts ne sai saƙonni na ma’aikata ko clients.
Ɗaya wayan ta kunna, wannan kam da ta shiga gallery ɗin hotuna biyar kacal ta gani aciki. Hoton farko na Mom ne tana budurwa kaman ma ranan aure ne dan ta sha ado na gwalagwalai da dimond ga shi kayan da ta sa wani kaman bridal dress ne kalar pink. Sai ɗaya hoton kuma Mom ne da wani ɗan yaro a gaban cake. Ta zooming hoton sosai sai ta ga a jikin cake ɗin an rubuta Najeeb is one. Dariya ta fara tana ganin yadda Najeeb ya ke so cute har da murmushin sa a hoton.
“Ayya! Miji na yana ɗan yaro”

Ta jima tana kallon hoton kafin ta tura zuwa hoto na gaba. Wannan hoton family picture ne kaman a Birthday ɗin Najma ne lokacin tana shekara shashida. Mom, Daddy, Najma, Najeeb da kuma wata budurwa wanda ba ta gane ko waye ba ce. Hoto na huɗu ma na wancan budurwan ce, tana murmushi ta sa graduation gown ta ɗaga hulan sama. Cikin ranta ta ce kowaye ce wannan tana da muhimmanci a rayuwan Najeeb, cikin ran ta ta ke tunanin ko budurwan nan babban yayar su Najeeb ɗin ce? To amma kuma Anas ya ce ‘ya’yan Daddy uku ne. Hoto na biyar da ta gani sai da ta miƙe tsaye. Ƙwaƙwalwanta ne ya shiga tunani, jijiyoyin jikinta suka fara guje-gujen kai saƙo domin su taimakawa ƙwaƙwalwar ta yi bincike cikin gaggawa.

“Na tuna, Wallahi na tuna” ta faɗa da ƙarfin ta…

Watarana sun fita supervision aiki wani waje. Tana gefen Najeeb yana magana da wassu sai ga wani mai saida cucumber a wheelbarrow. Wassu ma’aikata su ka nufe shi su na siya. Yadda mai cucumber ke yanka ta yana zuba yajin ƙuli sai ta ji yawun ta ya tsinke.

“Sir Najeeb ina zuwa” ta faɗa tana barin wajen da sauri. Zuwa ta yi aka yanka ma ta cucumber ta ɗari, ga albasa da aka yanka siri-siri da shi abin gwanin sha’awa. Tun a wajen ma ta ke ta haɗiyan miyau. Ta ƙarɓi ledan ta bi bayan Najeeb da ɗan sauri-saurin ta saboda ya nufi wajen da motar sa ta ke. Tana shiga motar ta buɗe ledar, ƙanshin albasa da ƙarago ya cika motar. Maimakon ya tada motar sai ya tsaya yana kallon ta yadda ta ke sa hannu tana cin cucumber.
“Kai! yajin nan ba ƙaramin maggie ya ji ba” ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido.
“Sir Najeeb za ka ci ne?”

“Miss Salihu…” sai kuma yai shiru ya tada motar

“Sir Najeeb ka san ba na iya juran yunwa, ga shi tun ɗazu mu ke ta yawo cikin rana”

Bai kulata ba ya maida hankalin sa ga tuƙi da ya ke yi.

“Sir Najeeb Allah ka ci, kasan ance maza su dinga cin cucumber saboda yana ƙara mu su ruwa” ta yi saurin riƙe bakin ta jin abinda bakin ya riga ya faɗa

Ɗan juyowa da yai ya kalleta ya sa ta ce “Sir Najeeb ka ji mi na ce ne?”

“Wani irin ruwa?” Ya faɗa ba tareda ya kalleta ba.

“Nima ban sani ba, kai namiji ne ai ka san irin ruwan ai”

“Ke kuma mace da ki ke ci mi zai ƙara mi ki?” Ya faɗa yana kallon ta.

Basar da zancen ta yi ta ce “tunda ba za ka ci ba shikenan”

Wajen traffic light da su ka tsaya ta cigaba da cin abinta. Hoton da ya ɗauka daidai ta kai cucumber baki ne.

Rungume wayan ta yi tana dariya. Wani daɗi takeji a duk ilahirin jikin ta, rabonda ta ji daɗi haka tun ranan da su ka ci gasa. Kai ya ma fi. Hoton ta a wayan Najeeb, duk da ma ta san ya ɗau hoton ne dan ya dinga dariya saboda ga bakinta cike da abu kuma ga shi ta kai hannu tana son ƙara cusa wani cucumber.

“I love you Najeeb, I love you” yanzu kam ta yadda ko ba so bane to Najeeb yana jin wani abu gameda ita…

Wajen message ta shiga tana duba saƙonnin wayan wanda ba su da yawa kaman ɗaya wayar.
Text ɗin da ta ci karo da shi an tura wa wani number da aka saving da Aysherh ne ya tsaya ma ta a rai. Duka texts ɗin sai da ta bisu ta karancesu. Ta gane text ɗin amma kanta ne ya ɗaure. Numban Ayshern ta duba wanda ya sa numfashin ta ya tafi hucin gadi na ‘yan daƙiƙai.

” N-J, Sir Najeeb shi ne N-J” ta faɗa tana dafa ƙirji.
Sai yanzu ta gane shirmenta na baya. Tana ta neman ma su suna da ya fara da N a kamfani bayan ga mai Kamfanin nan da ke da sunan NJ
“N-J, Najeeb Jibo” ta furta tana dariya kaman wata zararriya.

Its true kenan abinda Anas ke faɗa. Najeeb has feelings for her. Zama ta yi tana tuno abubuwan da su ka faru tsakanin su tun daga farkon fara aikin ta da shi har ƙarshen haɗuwar su. Duk wani abu da zai yi hinting feelings ɗin Najeeb sai da ta zaƙulo shi…

Tana cikin mota ma sai murmushi ta ke wani lokaci kuma sai ta yi dariya. Hatta Dreban ta Abdullahi sai da ya tsargu ko Madam ɗin na sa ƙalau ta ke yau ɗin.

“Hajiya amma dai lafiya?”

“Lafiya Malam Abdullahi” ta amsa tana sake duba hoton da Najeeb ya ɗauketa.

Ba su yi nisa da gida ba Daddy ya kirata akan ta zo gidan Hajiya Mama. Ta so ta ƙarasa asibiti ta ga mijinta ko da na minti ɗaya ne amma dole ta bari ta gama da komai dan ƙilan idan ta je wajen sa ba za ta iya barin gefen sa ba yau.
Cewa ta yi Abdullahi ya kai ta gidan Hajia Mama…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button