SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ta san Hajia Mama ba lafiya tun kwanaki to amma kusan sati kenan da aka sallamota daga asibiti. Rabonta da ‘yar tsohuwan ma kusan kwana takwas, tun tana asibiti rabon ta da ita.

Gaskiya ‘Yar tsohuwa na jin jiki dan yadda ta ganta ba ƙaramin bushewa ta yi ba. Tana kwance akan gado su Mom, Daddy, Uncle Sulaiman da Hajia Fatima su na kewaye da ita.

Har ƙasa ta tsugunna ta gaida su, kafin Daddy ya ce “Mama ga Aishatun na ki ta zo”

Hajia Mama ta ɗan miƙa hannu tana yiwa Farida alamar ta zo. Farida ta ƙaraso ta tsugunna a bakin gadon tana riƙe hannun Hajia Maman.

“Aishatu ce ko?”

Hajia Fatima ta ce “e ita ce, ba kin ce a kira mi ki matar Najeeb ba”

“Najeebullahin ya tashi ne?”

Farida da idon ta ya ciko da hawaye ta ce “zai farfaɗo Insha Allahu Hajia”

Hajia Mama ta ɗan yi murmushi, ta san Allah bai bata haihuwa ba amma ya bata ‘ya’ya da jikokin da za su tuna da ita bayan rai yai halin sa.

Akwai wani awarwaro kaman bangle na zallan azurfa da ke hannun Hajia Mama. Ko su Daddy da shi su ka tashi su ka gan ta. Ba su taɓa gani ta cireshi ba.

Hajia Mama ta sa hannunta ta cire awarwaron azurfan ta miƙawa Farida.
“Mutane dayawa sun nemi na bar mu su wannan awarwaron amma na ƙi, kin san miyasa na baki?”

Farida ta girgiza hawaye na zubowa a idon ta.

“Na yiwa Najeebullahi alƙawarin zan bawa matar sa awarwaron nan…”

Tari ne ya ƙwace ma ta. Ta jima tana yi kafin ta cigaba.

“Kyautar budurci ne, tundaga ran da Alhaji ya sa mi ni a hannuna ban taɓa cire shi ba sai yau. Ki riƙe shi da daraja”

“Insha Allah Hajia” ta faɗa tana sa awarwaron a hannun ta.

“Allah Sarki Najeebu na. Allah ya tashe ka”

Kowa a wajen sai hawaye.

Mom ta taso ta durƙusa gefen Farida da ke sheshsheƙar kuka.

“Hajiya” Mom ta faɗa cikin raunatacciyar murya

“Nabilatu ce”

Mom ta gyaɗa kai.

“Ki yafe min dan Allah. Najeeb ya yi gaskiya ni ba uwa ta gari ba ce, ranan da Aisha za ta rasu ta kira ni sau biyar, kuma daga jin yadda take nishi na san tana jin jiki amma kishi ya rufe min ido ban je na taimaketa ba, ban kuma kira an je an taimaketa ba har ta haihu ita kaɗai ta rasu ba kowa a wajen ta. Ki yafemin”

“Allah Sarki Najeebu ashe dai dalilin da ya sa ya ke gudun ki kenan. Na yafe miki, ai dama sababin mutuwar Aisha rubutacce ne tun kafin ta zo duniya. Allah ya yafe mu gaba ɗaya. Na yafe wa kowa”

………………

Duk wani ɗokin zuwa asibiti da ta ke sai ta ji ya fita a ranta. Tana so ta tsaya da tsohuwar nan wanda ta ke cike da tarin barkwanci.
Ranan ba ta bar gidan ba sai taran dare. Da ta je ma kuka ta dinga yiwa Najeeb tana nuna ma sa awarwaron da Hajia Mama ta bata…

Da asuba bayan ta yi sallah ta yi azkar ta ɗau alƙur’ani ta zo saitin kunnen Najeeb tana karanta ma sa kamar yadda ta saba. Da ke asabar ne ba za ta je aiki ba. Kusan ƙarfe shida da rabi sai ga kiran Mom akan Allah ya yiwa Hajia Mama rasuwa tsakar daren jiya, tun daga wajen ta fara hawaye…

Tareda ita aka yi karɓan gaisuwa har na kwana uku. Cikin kwanaki ukun nan sau ɗaya ta ke zuwa duba Najeeb…

7days later

Daren ranan jummu’a tana zaune akan kujera tana karatun ƙur’ani bacci ya sace ta. Tana bacci ta yi mafarki Najeeb ya farka yana kiran sunan ta. Da murmushi ta buɗe ido lokacin da ta farka. Haka kawai sai ta tsinci kan ta da zuwa dubashi ko dai da gaske mafarkin ta zai zama gaskiya.
Ƙura ma sa ido ta yi, kaman a mafarkin sai ta ga gashin idon sa yana ɗan rawa, chan kuma sai idon ya buɗe, ido ta zaro ganin idon sa ya buɗe. Sake rufe idon yai ya sake buɗewa a karo na biyu a karo na uku kam da ya buɗe bai sake rufewa ba.

Farida da ta yi suman tsaye na ɗan daƙiƙai ka sa yarda da abinda idon ta ga gani ta yi ta fara murza idon ko dai har yanzu bacci ne a idon ta. Ganin idon sa a buɗe ta mari kumatun ta da ƙarfi dan ta tabbatar dai ba mafarki ta ke ba. Bakin sa ta ga yana motsawa kamar zai yi magana amma bakin ya ma sa nauyi. A hankali ta ƙarasa wajen sa hannun ta na rawa ta kai yatsar ta kaman za ta sa a idon sa sai ta ga ya fara ƙyafƙyafta idon.

“Sir Naj…” maganar bai ƙarasa fitowa ba ta faɗi wajen a sume…

Team Najeeb ku sha rawan shoki wannan page na ku ne

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣3️⃣9️⃣

Yana son ɗaga hannun sa amma hannun ya mai nauyi banda yatsun sa da su ke motsi ya kasa ɗaga hannun sama. Da farko baƙi ya ke gani daga baya kuma ya ci karo da idon mutum. Ba zai iya cewa ya san mai idon ba hakanan kuma ji ya ke kaman ya jima yana kallon mai idon. Ƙaran na’ura da kuma abubuwan da ya ga an jona ma sa a ƙirji ya tabbatar ma sa a asibiti ya ke. Ƙoƙarin tuno dalilin da zai kawo shi asibiti ya ke amma ya kasa. A hankali ya fara ƙoƙarin tursasa ma ƙwaƙwalwar sa domin ta gano abinda ya kawo shi asibiti. Yana so yai magana amma ya kasa, haka ya cigaba da kallon sama still yana ƙoƙarin gano miya faru da shi da kuma inda ya ke.

Tun ƙarfe huɗu na dare sai ƙarfe biyar da kwata ta farfaɗo. Initially ƙwaƙwalwarta bai tuno ma ta miya faru ba, amma cikin rabin sa’a da ta tuno abinda ta gani sai ta yi wuff ta tashi.
Har lokacin idon sa a buɗe ya ke.
“Da gaske Sir Najeeb ka farfaɗo?” Ta faɗa tana shafa fiskar sa.
Da yana da bakin magana da zai tambayi dalilin taɓa shi da ta ke.
Dariya ta ke, murmushi da kuma kuka duk a haɗe. Ta jima tana kissing kumatun sa duka biyu kafin daga bisani ta ankara ko Sujudish shukri ba ta yi ba.
Ta gyara ɗaurin ɗankwalin ta sannan ta yi kabbara ta yi sujjada. Bayan ta ɗago da gudu ta je wajen jakarta ta fito da waya, ba za ta iya barin ɗakin nan ba. Idan ta fita zai iya rufe idon sa ya ƙi buɗewa.
Numban Daddy ne a kusa dan haka shi ta kira, har wayan ya katse ba a ɗauka ba. Ba ta yi ƙoƙarin sake kira ba sai ta kira numban Mom. Sai da ta kusa yankewa kafin aka ɗauka.

“Hello Mom ya tashi, ya tashi mom. Idon sa a buɗe har yanzu, Mom ku zo ya tashi” wassu maganganun ma ba ta san ta yi su ba dan abin na ta har da shirme.

“Najeeb ya buɗe ido?” Mom ta tambaya da mamaki

“Yes Mom wallahi idon sa a buɗe ya ke har yanzu”

“Muna zuwa yanzu ki kira likita” har za ta ajiye wayan sai ta kuma cewa “Aisha dan Allah ki turomin hoton ɗana na gan shi”

“Yanzu ma kuwa Mom”

Tana katse kiran ta shiga camera ta fara video ɗin Najeeb.
Shi kan kallon ikon Allah kawai ya ke yi yana ƙyafta ido. Bai san me wannan matar ke yi ba, ihun da ta ke ma ya sa bai gane maganganun da ta ke faɗa.

38sec video ta turawa Mom wanda ta ke saukowa daga stairs. A ƙasa ta haɗu da Daddy daya dawo daga masallaci.

“He’s awake, our son is awake” ta faɗa tana fashewa da kuka.
Karɓan wayar da ta ke nuna ma sa yai ya kunna video ɗin, and there it is, idon ɗan sa Najeeb a buɗe har yana ƙyafta ido.

“Alhamdulillah, Alhamdulillah” ya faɗa yana mai sujudi. Mom ma ganin haka ita ma ta bi shi ta yi sujjadar…

Tana turawa Mom video ta fara kiran numbar Dr Sadiq da ke shima na masallaci bai ɗauka ba, sai ta kira Dr Johnson, shi kam ya ɗauka amma ya sanar ma ta baya asibitin ta kisa Dr Usama. Duk ma su kula da Najeeb tun daga doctors zuwa nurse tana da numbobin su. Hatta cleaner da ke zuwa gyara ɗakin musamman idan bata nan tana da numban su…

Kusan minti shida sai ga Dr Usama ya shigo.

“Doctor ka gani ko, ka gani idon sa a buɗe ko?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button