SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Mutumina ka san yarinyar nan ta bi waiter har kitchen ɗin su. Na ji tausayin saurayinta wallahi, haka yai wani lafau da shi abin tausayi”
Najeeb ya ce ” its his fault ai, ta ya zai dating lousy girl kamar wannan”
“Yarinyar tana da kyau ba laifi, sai dai surutu kam Tabarakallah ko gidan radio iya ka ci” …
Rayyan da Farida kuwa ba su suka bar restaurant ɗin ba sai da Farida ta sauke masifar ta ta huce. Shi Rayyan abincin ma kasa ci yai, ita kuwa aka kawo ma ta fried rice ta naɗa harda take away ta yi.
………………..
“Gaskiya Yaks idan na ce ma ka akwai vacancy a ƙasa na yi ƙarya, sai dai ka bani lokaci nan zuwa next week zan bincika, idan ma ba ta samu anan ba zan iya nema ma ta a wani wajen. Ai ƙanwar mu ba za ta rasa aiki ba Insha Allah”
Yakubu yai ma sa godiya sannan ya fice daga office ɗin.
Anas kenan, yana da sauƙin kai ba kaman Oga kwata-kwata ba, wanda mulki da girman kai ya hanashi sakewa da mutane. A shekarun sa na uku da fara aiki a Najeeb constructions sun saba da Anas sosai, tamkar yayansa haka ya ɗauke shi…
Anas na tattara wa su files kiran Najeeb ya shigo wayar sa, dama files ɗin wajen Najeeb zai kai su dan haka ya amsa wayan da sauri dan ya san abokin na sa da gajen haƙuri.
“Mr Man yanzu na ke shirin kawo ma ka files ɗin”
Cikin huci Najeeb ya ce ” Anas ka san that stupid boy bai zo ba, and numbar sa ba ta shiga. Find a replacement, ba zan iya da shi ba”
“Calm down Yallaɓai, barin zo office ɗin sai mu yi maganar…
Duk yadda Anas ya so Najeeb ya ƙarawa Joseph lokaci hakan bai yiwu ba, ƙarshe dai cewa yai ya nemo ma sa wani ko wata.
“Gaskiya you need to change abokina, this guy is good, and kai ma tsakani da Allah ka san kwana ukun da ka bashi ya yi ma sa kaɗan”
“I dont bloody care. Zaman shi a chan ba zai dawo da wanda ya mutu ba neither will it profit him in anyway. So why will he risk his job for that”
“It’s his mother’s burial, kuma kasan al’adun su da namu ba ɗaya bane”
“And so freeking what?. Just ka nemo wani kawai”
Anas ya kalli abokin na sa cike da takaici ya ce ” ba kowa ke da mummunan ra’ayi irin taka ba Najeeb, just because ba ka ɗauki mahaifiyar ka a bakin komai ba doesnt mean kowa ma haka ya ke. Joseph yana son mahaifiyar sa, shiya sa ya tsaya yaiwa mahaifiyar sa proper burial kaman yadda al’adar su ta tanada. I hope you understand that”
“Oh please Anas! Not this talk again”
“Ka na so, ba ka so, gaskiya ce dole na faɗa ma ka duk min ɗacin ta kuwa”
“Find another secretary for me Arch Anas Ali Almustafah”
Kallon-kallo su ka yiwa junan su kafin Anas ya fice daga office ɗin.
????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Free page
0️⃣0️⃣4️⃣
Ranan Tuesday sai ga Joseph ya zo office, ya sani sarai Najeeb zai yi fushi da shi amma bai ɗauka abin zai kai ga kora ba. Infact, irin koran walaƙancin da Najeeb ya ma sa sai da yai dana sanin fara aiki da Najeeb. Tun farkon zuwan sa kamfanin ya samu labarin halin maigidan na sa a wajen sauran ma’aikata, sai dai bai ɗauka abin na sa ya kai yadda ake faɗi ba sai da ya gani muraratan.
Anas dai ba yadda ya iya ne amma ran sa ya sosu da abinda Najeeb yai wa Joseph.
“Sir, he gave me 3 days, only 3days. I left Kano on tuesday morning, i reached my village on wednesday. My mother was buried on saturday and i make sure i squeezed myself and came back to Kano on Monday night. But he wont listen”
Joseph ya faɗi yana goge hawaye. Shi takaicin sa ma bai wuci yadda Najeeb ya nuna halin ko in kula da mutuwar mahaifiyar sa ba.
Anas ya kalle shi ya ce “please dont take it personal, Najeeb doesnt even respect his own mother. I’m sorry about your loss Joseph, i lost my mother when i was only 7yrs so i know how you feel”
Kalaman Anas su suka kwantarwa Joseph hankali har ya ƙarɓi check ɗin da Anas ya bashi sannan ya tafi…
…………………
Ido Yakubu ya zaro lokacin da Anas ya gaya ma sa akwai vacancy na ɓangaren secretary ɗin Najeeb.
Indai kana aiki da Najeeb Constructions to dole ne ka san halin Najeeb balle kuma jiya-jiya Najeeb ya gama koran Joseph wanda harda kira ma sa security su fita da shi, ba dan Anas ya sa baki ba Allah kaɗai ya san halin da Joseph zai shiga.
“Kana tsoron kar a walaƙanta ƙanwarka ko?” Anas ya jefa ma sa tambaya
“Na ma ka alkawari zan yi ƙoƙari na ga ƙanwarka ba ta walaƙanta ba, za tai aiki da Najeeb na lokaci kaɗan ne ana samun wani vacancy ɗin zan chanja ma ta aiki”
Yakubu ya sauke ajiyar zuciya ya ce ” Aikin Farida da Sir Najeeb ba mai yiwuwa bane, idan Farida ba ta ƙona shi ba to shi zai murɗe ma ta wuya ya kasheta. Ka san Farida kuwa? Ai Najeeb da Farida su ka haɗu anan kamfanin inaga ƙonewa kawai zai yi dan wuta da wuta ne”
Dariya Anas yai ya ce ” har akwai yarinyar da za ta iya karawa da Najeeb? Gaskiya zan so ganin wannan Faridan”
“Hmm, na san halin Sir Najeeb na kuma san ‘yar uwata Farida, amma wallahi duk inda Sir Najeeb ya kai da jin kai da miskilanci to Farida ta taka shi. Maganar ta zama Sakatariyar sa ma bai taso ba. Farida Farida Hmm…”
“Wallahi ni kuma da ka yi bayanin nan sai na ga sun dace gara a samu wacce za ta iya taka ma sa birki ko zamu huta da halin san nan”
“Allah akwai matsala idan Farida ta yi aiki da Sir Najeeb, yaƙi za’ayi fa a kamfanin nan”
“Kar ka damu mutumina, ka turo ta kawai na ma ta interview”
………………………
Ɓangaren turaruka ya nufa a Mall ɗin saboda favourite perfume na shi ya kusa ƙarewa. Kamar daga sama ya fara jin muryan ta, kamar ranan da ya fara ji yau ma masifa ta ke yi. Zuciyar sa ce ta raya ma sa ba ita bace amma kunnensa ya ƙaryata hakan, domin kuwa muryar sak da wadda ya ji ranan a restaurant. Yana so ya maida hankalinsa kan abinda ya ke dubawa amma kuma idanuwan sa na ƙwaɗayin gaskata abinda ya ke ji, shin yarinyar ranan ce? ko kuwa wata ce mai irin muryarta.
Kasa daurewa yai sai daya juya ya maida dubansa ga inda ya ke jiyo muryan. Ita ɗince dai, ‘yar mitsilar yarinya mai shegen surutun nan. Ya kai duban sa ga wanda ta ke wa masifan ya ga ba saurayin ranan bane wani ne daban, haka kawai ya ji tsanar yarinyar dama ma su irin halinta kam ina za su iya kama kai.
He couldn’t believe it, garin kallonta sai ga shi har turaren da ya ɗauka yana shirin faɗuwa daga hannunsa. Yai saurin taro turaren tareda sake murmushi saboda wautar da yai, garin gulma. Abin haushin ma ba wai ya san yarinyar bane amma kuma gashi halayyarta ya dameshi. Ya saurin kauda kan sa lokacin da su ka zo za su wuce shi, tana tafiya tana surutu, kafaɗarta ya ɗan gogi bayansa kaɗan, yai saurin juyowa ya bi bayanta da kallo amma she’s too busy talking to even notice what happened.
“Lousy girl” ya faɗi a fili sannan ya ɗau turaren ya bar wajen…
“Ni wallahi da na san ɗan abinda za mu saya kenan da ban biyoka ba Yaya Faruƙ. Duk abinda mu ka ɗauka ka ce yai tsada. Dama ai abu mai kyau shi ake siya da tsada”
“Wallahi mijin ki ya shiga uku Farida, ke fa ki ka ce mu zo nan ba ni ba. In ba dan ke ba mi zai sa na zo siyayya a nan”
“Amma Yaya ai ba ka cemin ba ka da kuɗi ba ko!”
“Allah ya shiryeki dai”
Har su ka bar Mall ɗin ba ta dena complain ba, dama wasu kaya ne Yaya Faruƙ zai siya na bikin ƙannen sa. Ƙarshe dai daga Mall ɗin kasuwa su ka wuce…