SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Wanni na’ura ya ɗauko mai kaman torchlight ya fara haska idon Najeeb da shi. Farida na gefe tana sauke numfashi.
Duk wani response na ido Najeeb ya yi. Ya ci first step a cikin glasglow coma scale da ake yiwa wanda su ka farfaɗo daga coma.

“Ka na jina?, are you hearing me?” Dr Usama ya faɗa

Najeeb sai motsi ya ke da baki amma maganar ta ƙi fitowa.

“Idan kana jina ka motsa hannun ka” ya faɗa yana kallon hannun.
Najeeb ya fara motsa hannun sa a hankali.

“Alhamdulillah” Dr Usama ya faɗa.

“Dr Usama ya baya magana?”

“Malama Aisha kenan watanni fa yai a kwance ba magana ba motsi, a hankali komai zai dawo dai-dai. Alhamdulillah ma tunda har ya fahimci mai na faɗa”

“Allah ya baka lafiya miji na” ta faɗa tana goge hawaye.
Ƙarfe shida ta gota kafin su Daddy su ka iso.

Har lokacin Dr Usama na wajen tareda Dr Wunmi. Duk abinda su ke a kan idon Farida. Ta ƙi matsawa ko nan da chan.

Daddy dai ya yi ta maza bai yi kuka ba amma Mom kam kuka ta fara ganin yadda ake Ƙoƙarin juya kan ɗan ta saboda wuyan da ya riƙe. Ƙwanciya waje ɗaya tsawon watanni ba wasa ba…

Su ukun suna tsaye a kansa sun ƙura ma sa ido, yadda su ke kallon sa ka ce jaririn yaro ne sabon haihuwa.
Ƙarfe takwas aka ce za’a ma sa Computerize Tomography Scan (CT-scan)
saboda a gano ko akwai matsala a ƙwaƙwalwar. Najeeb ma idon ya zuba mu su. Daga ya kalli Daddy sai ya kalli Mom da ke hawaye sai ya kalli Farida da ta kasa rufe baki.

Yanda ya ke jan numfashi ma ka san a wahale ya ke yi.
Duk cikin su ba wanda ya matsa daga gefen sa har aka zo aka fita da shi. Sai da aka tafi da shi tukunna Daddy ya kira Najdah ya faɗa ma ta sannan ya kira ƙanin sa…

Kafin a gama yi ma sa komai ‘yan uwa sun cika wajen. A kwance aka turo shi aka dawo da shi ɗakin. Kowa sai tausayi yadda ya ke abin tausayi. Ga baki amma ba magana.
Likitan ne ya kira su gefe yana briefing na su akan abubuwan da za su yiwa Najeeb saboda taimakon sa har ya warware. Kafin result ɗin scan ɗin sa ya fito kar a dinga hayaniya a wajensa kuma mutanen da su ka fi kusa da shi ne kaɗai za su tsaya kusa da shi dan idan yana ganin baƙin fuska zai confusing ɗin sa…

Kwana biyu kafin aka fara ɗaura Najeeb akan wheel chair, har lokacin baya magana sai dai wani lokaci idan likitoci na tambayar sa yana gyaɗa mu su kai tunda kan ya fara motsawa yanzu. Da ke an hana hayaniya, banda wanda su ke kusa da shi ba wanda ya ke zuwa wajen sa.
Farida kam duk da yanayin da ya ke ciki na rashin magana da rashin iya motsa jiki tafi kowa farin ciki saboda yanzu idon Najeeb a buɗe su ke, zai kalleta za ta kalle shi.
A rana na biyar ya fara iya ɗaga hannun sa har ana bashi abu yana iya riƙewa kuma har lokacin ba magana.

Bayan CT scan da aka ma sa sai da aka kuma yin MRI wanda aka tabbatar mu su Najeeb yana da severe traumatic brain injury. A yadda su ka mu su bayani Najeeb zai jima kafin ya iya yin komai da kan sa hakanan kuma zai iya manta wasu abubuwan gaba ɗaya, wasu abubuwan kuma sai a hankali zai dinga tuno su.
Farida kam ta dena zuwa office, ko da abu ya taso sai dai Anas ya kawo ma ta ta yi cike-ciken da za ta yi a asibitin. Yanzu kam ita da Mom su ke kwana da shi. Har gara itama ta dena kuka yanzu, amma Mom idan ta ga ana ma sa neuropsychological assessment ko excercise sai abin ya dinga sa ta kuka. Hatta juya kai sai da aka koya ma sa.
In every theraphy section da aka yi ma sa Mom da Farida su na manne da shi. A kwana na sha uku aka fara koya ma sa tsayuwa. Sai a bashi abu ya dafa ya tsaya idan ya daɗe sai a zaunar da shi kafin a kuma ɗaga shi a haka ake yi har sai an ga ya gaji kafin a bar shi haka nan.

Ranan da aka fara bashi abinci, amai ya dinga kwarawa ƙarshe jikin sa ya fara jijjiga da ƙyar aka samu jikin sa ya dawo normal. Sai da ya kwana biyu ana bashi maganin da zai sa shi iya cin abinci kafin da ya ci bai amayar ba. Mom ce ke bashi abincin amma yana ci kaman wani ɗan koyo.

A rana na goma sha tara ya fara magana. Mom na sallah ita kuma Farida na zaune a kujera tana karanta ma sa labari taji kaman magana. Maganar ta fito kaman mai koyon magana ko na ce irin maganar wawaye.
“Yuu a yuu?”

Ta yi saurin ajiye littafin ta kai kunnen ta saitin bakin sa dan ta ji da gaske Maganar yai.

Maganar ta sake fitowa kaman ta da. Da farko ba ta gane me ya ce ba sai a na biyu da ya maimaita ta gane cewa “who are you” ya ce.
Dam ta ji ƙirjin ta ya buga.
“Sir Najeeb ba ka gane ni ba?, Aisha Farida, Miss Salihun ka”

Mom ta dafa kafaɗarta ta ce “Aisha ki kwantar da hankalin ki, kin ji dai mi likita ya ce” sai a lokacin ta ji zuciyarta ya yi sanyi.

“Whhhhere…Whhha” sai yai shiru saboda maganar da ta maƙale ma sa.

Mom ta fara shafa kan sa tana cewa ” its ok son, a hankali maganan zai fita”

Da therapist ɗin da ya ke ma sa rehabilitaion theraphy section ya zo su ka gaya ma sa ya yi magana. Sai ya fara ma sa wassu tambayoyi, wassu ya amsa da ƙyar wassu kuma shiru yai.

Tambayar farko sunan sa ya tambaya. Bawan Allah Najeeb kam da ƙyar ya iya furta “YaaJeeb” Najeeb ɗin ya ke son faɗa amma saboda bakin sa da be koma dai-dai ba maimakon N to Y ne ta fito.

A kwana na ashirin da shida ya fara gwada tafiya da taimakon sanduna biyu. Yanzu maganan sa ta ɗan fara kyau ba kaman ranan da ya fara magana ba…

Fiskar Daddy Dr Kenneth wanda ya ke shi ne rehabilitation therapist ɗin sa ya nuna ya tambaya ko ya gane shi.

“Dad” ya faɗa a hankali.

Ya nuna Mom ya tambayeshi, ya jima yana kallon ta kafin ya ce “Mom”
Hawaye da Mom ke ƙoƙarin ɓoyewa ne su ka fara zubowa. Shekara nawa rabon da Najeeb ya kira ta da wannan sunan.
Najdah aka nuna ita ma ya furta “baby”
Ƙirjin Farida bugawa ya ke da ƙarfi-ƙarfi yadda ka san zuciyar ta ne zai fito.

A karo na uku ya sake tambayar shi ko ya san Farida amma bai yi magana ba. Najma ya nuna ita ma ya kira sunan ta Najma.

Wannan karon hawayen da Farida ke ɓoyewa kan su ke zirya a idon ta.
Najeeb ya zuba ma ta ido yana son gane a ina ya san ta amma ya kasa, kuma idon na ta ya ma sa kama da idon da ya ke yawan gani cikin baccin sa.

Hannu ya ɗaga ya nuna Farida da yatsa ya ce “who is she?”

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣0️⃣

jiya na ga comments ɗin ku na kuma sha dariya. Princess Salma shugaban ‘yan team Farida, ina mai ban haƙuri????. No brain injury is the same haka healing process ɗin ma ba ɗaya bane. Normally waɗanda su ka farfaɗo daga coma su na shiga wani yanayi da ake cewa traumatic brain injury. Ya danganta idan aka gwada mutum a samu ko mild ne ko acute ko kuma severe. Ko da wanda aka yiwa induced coma ba sa farfaɗowa a take su dawo normal. Wassu idan su ka farfaɗo manta komai su ke tundaga magana zuwa tafiya zuwa duk wani abu da su ka iya da. A hankali-ahankali ana sake koya mu su sai brain ɗin su ya dinga picking da sauri, waɗansu abun ma kafin a nuna musu sai su tuna da kan su. Najeeb ya fara tuna ‘yan uwansa ne saboda sun fi kusa da shi. It will be odd ace daga farko-farko ya gane Farida tunda ba wai sun jima tare ba ne. Koda ya ke Najeeb ɗan duniya ne zai iya ganeta ma ya waske???? i dont know, ba ri mu bi su mu ga ya za ta ƙare

Najdah ne ta yi saurin cewa “she’s your secretary” Daddy ya buge bakin ta.
Najeeb cigaba dai da kallon Farida yana son fahimtar miye ma’anar secretary da kuma dalilin da ya sa ita wannan secretary ɗin ta ke tareda shi koyaushe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button