SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Dr Kenneth ya ce “za ka tunata a hankali. Yanzu ka tuna ya aka yi ka zo nan?”

Najeeb ya girgiza kai still idon sa na kan Farida da idon ta ke cike da hawaye amma tana ta dannesu kar su zubo.

“Ba ka san ya aka yi accident ɗin nan ya faru ba?” Najeeb ya sake girgiza kai.

“Ka tuna wani abu a iya kasancewar ka cikin yanayi na coma?”

“I dont know, there was darkness, then voices then her eyes” ya faɗa yana nuna Farida

“Za ka iya tuna voice ɗin da ka ke ji?”
Najeeb ya girgiza kai.
Dr Kenneth ya miƙa ma sa wani littafi ya ce duk abinda ya tuna ya rubuta a ciki.

Kafin Dr Kenneth ya fita sai da ya tabbatar mu su da kada su dinga damun sa da tambayoyi, su bari a hankali zai dinga tuno komai. Za dai su iya dinga yi ma sa labarin abinda ya ke so ko kuma su dinga nuna ma sa abubuwan da zai sa ƙwaƙwalwar sa ta yi saurin dawowa dai-dai…

Najeeb ya buɗe littafin ya fara zane. Idan akwai abinda ya farayi bayan ya fara iya riƙe biro to zane ne. Dan har yanzu ma rubutun sa bai dawo dai dai ba.

Dukkan su su ka zuba mishi ido su na ganin yadda ya ke zanen wani gida. Duk da freehand sketch ne hakan bai hana gidan ya fito da kyau ba. Da ya gama sai ya zana wata mace a bakin gidan tana murmushi wanda yanayin fiskar ya ɗan yi shige da fiskan Farida.

Farida kam ba zanen ta ke kallo ba tana tsaye ne amma ta yi nisan kiwo. Tunanin ta bai wuce ya za ta ji idan aka ce kwata-kwata Najeeb ya manta da ita kuma ya kasa tunowa da ita.

“Aisha” mom ta faɗa tana dafa kafaɗarta. Ta ɗanyi firgigit ta kalli Mom, Mom ta nuna ma ta Najeeb.
Idon ta ya sauka akan Najeeb da ke miƙa ma ta takarda. Hannu na rawa ta karɓi takardar. Duban zanen ta yi sai ta fashe da dariya wanda ya sa hawayen da ta ke ta ɓoyewa su ka samu damar saukowa.
Shima Najeeb ɗin murmushin yai.

Ba abin da ya fi ɗaukan hankalin Farida irin abinda ya rubuta a ƙasar zanen Plz smile

“Allah sarki yanajin ta ajikin sa ne fa” Daddy ya faɗa yana shafa kan ɗan na sa.

Najdah ta cika ta yi fam, tana ta hararan Farida ta gefen ido.

Mom ta ajiye album a gaban sa ta buɗe tana faɗin duk wanda ta tuna a ciki ya faɗa. Hoton baby tana jinjira ne a farko, ya fi minti biyu yana kallon hoton kafin ya ce Baby. Gaba ɗaya sai su ka sa dariya.
Hoto na gaba kuma na shi ne yana ɗan shekara huɗu anyi hoton a wani amusement park ne yana cikin motan wasan yara. Wannan kam bai ɗau lokaci ba ya nuna kan sa. Hoto na uku hoton shi da Sabreen ne lokacin da Sabreen ta yi graduation ɗin gama high school. Ya jima yana kallo, ya gane ta amma sunan ya maƙale ma sa. Kusan minti huɗu ya ce “Sa Sa Sabreen”…

Har lokacin da Farida ta zame jiki ta bar ɗakin ba su ankara ba. Tafiya ta ke amma ba abinda ke yawo a ƙwaƙwalwarta irin sunan da Najeeb ya ambata.
Wato ya iya tuna Sabreen amma ita bai tuna ta ba, Sabreen fa!…

Hoton Aisha aka buɗe ma sa lokaci guda idon sa ya fara kawo ma sa hoton ta kwance cikin jini. Dafe kan sa yai yana numfashi da ƙyar nan kuma seizure ya kama shi ya fara jijjiga. Su Najma su ka fita kiran likita, bayan seizure ɗin ya tsaya Dad ya gyara ma sa kwanciya ya maida shi kwance ta gefen sa…

……………….

Tana zuwa ɗakin su gado ta hau, kukan ma da ta ke son yin ma ta kasa. Zazzaɓi ne ya rufeta tun tana rawan sanyi har bacci ya tafi da ita. A ƙalla ta yi awa uku tana bacci kafin ringing ɗin wayar ta ya tashi.

Ta ɗau wayar tana mai goge gumin da ke goshinta da ɗaya hannun.

“Aisha ki na ina?”

“Ina gida Mom”

“Yaushe za ki dawo?”

“Sai dare”

“Ok”

Sai da ta ajiye wayan ta tashi da ƙyar. Ko’ina a jikin ta ciwo ya ke a haka ta shige banɗaki dan ta yi wanka…

Da dare da ta isa ta tarar da abun mamaki. Mom na tsaye gaban Najeeb tana hawaye tana bashi haƙuri, shi kuma ya kauda kai gefe.
Daddy baya nan dan ya bar asibitin tun da yamma. Najdah ne a wajen bayan Mom, itama Sallah ta ke yi.

Mom ta zagayo gaban Najeeb ta tsugunna har ƙasa. Da gudu Farida ta ƙarasa wajen tana ƙoƙarin ɗaga Mom.
“Mom so ki ke ki ja ma sa bala’i. Bai kamata ki tsugunna ma sa ba”

“Ki bar ni Aisha, ya tuno abinda na yi ya ce baya son ganina. Plz ki ce ya yafe min, ba zan iya rayuwa ba tareda ina kusa da shi ba”

Farida sai da ta tabbatar ta ɗaga Mom kafin ta sa hannu ta fara goge ma ta hawaye.
“Dan Allah ki dena kuka, kukan ki masifa ce a gareshi”
Da ƙyar Mom ta iya haɗiye kukan ta yi shiru.

Farida ta juya ta kalli Najeeb da ya ƙura ma ta ido, cikin ɗaga murya ta ce “kai Sir Najeeb, ka kiyayi fushin mahaifiyar ka. Kar ka ga dan kana cikin wannan yanayi ana tausaya ma ka ka maida mu bamu san mi mu ke ba, ka sanni sarai zafi gareni, kuma idan ba ka shiga taitayinka ba duk abinda ke cikin ƙwal…”

“To kashe ma na shi. Munafuka, kin san yana cikin wani hali amma ba za ki bari hankalin sa ya kwanta ba, kashe shi tunda abinda ki ke so kenan, dan ki gaji dukiyar sa ko”

“Najdah!” Mom ta daka ma ta tsawa.

“Mom ki ga abinda ta ke ma sa fa, anan ɗazu ya shiga wani hali saboda wani abu ya tuno amma yanzu ta dinga ma sa masifa kaman wani ɗan ta”

Shikan ido ya ke bin su da shi. Yadda Farida ke masifa haka ya dinga ji ƙwaƙwalwarsa na tuno ma sa wassu masifan da ta yi a baya. Abin ya confusing na shi, domin yana ta ƙoƙarin gano a ina abubuwan nan su ka faru kuma yaushe su ka faru.

“Ki tafi ki bamu waje zamu iya jinyar sa” Najdah ta faɗa tana kallon Farida ido cikin ido.

“Yarinya kenan, ki je ki yi aure za ki fahimci minene tsakanin miji da mata. Jinya kuma ko uwar da ta haifeshi ba ta ma sa ɗawainiyar da na ma sa ba.”

“Mom kin ji maganar banzan da ta ke yi ko?”

Mom ta ce “gaskiya ta faɗa. Babu wanda yai wa Najeeb hidima kaman ta, kuma ba abinda za mu saka ma ta da shi sai addu’a. She’s the only one that never stop believing in him kuma na tabbata da ya yi shekaru a haka to a hakan Faridan za ta jira shi”

Najdah haushin maganan Mom da ta ji ya sa ta je ta ɗau jakan ta fuuuu ta fita ko sallama babu.

“Koyaushe haka ki ke da faɗa?” Najeeb ya tambaya yana kallon Farida

“Haka na ke, a haka ka sanni dan haka idan za ka tuno ka tuno, idan ma ba ka tuno ba to zamu cigaba daga inda mu ka tsaya”

“Son please forgive me” Mom ta faɗa tana haɗa hannun ta alamar magiya.

“Ka san Allah Sir Najeeb ba inda za ta je sai ka ce ka yi haƙuri”

Dariya yarinyar ta bashi.
“A matsayin ki na wa?”

Confidently ta ce “a matsayina na matar ka”

“Mata na?” Ya tambaya looking confused

“Yes ni matar ka ce” …

…………………….

Bai gama yadda da maganar Farida ba sai da Washegari da Najdah ta zo ya tambayeta ya aka yi ya auri Farida ba Sabreen ba. Da ke tana jin haushin Farida ba ta faɗi laifin Sabreen ba, sai ta ce Daddy ne ya aura ma sa Farida kuma ba son ta ya ke ba.
Maimakon ya bibiyi miya faru. Sai zuciyar sa ta fara kawo ma sa soyayyar sa da Sabreen, take kuma tausayin Sabreen ya kama shi. Sai dai kasancewa bai gama gane abinda ya faru da shi ba ya sa yai shiru…

Duk da ya tuno abinda ya haɗa su da Mom amma tundaga ranan da Farida ta ma sa masifa sai ya dena ɗaure ma ta fiska amma dai still ya kasa sake jiki da ita.

A kwanan sa na talatin da bakwai da farfaɗowa sai ga Sabreen. Shi da Farida da therapist ɗin sa ne a chan wani fili, yana gwada tafiya da walking stick ɗaya maimakon biyu da ya ke amfani da su da.

Najdah da Sabreen ne su ka nufo su. Sabreen na ƙara tabbatar wa idon ta ga Najeeb nan a raye kuma yana tafiya ta yanka da gudu ta je ta faɗa jikin sa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button