SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Noory you’re back, i miss you Noory, i miss you”

Ji ta yi an damƙi gashinta da ƙarfi, dama ɗan gudun da ta yi ya sa gyalen da ta yafa ya faɗi.

“Ah Ah…Noory help” Sabreen ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwatan kan ta. Amma ba ƙaramin damƙa Farida ta yiwa gashin ba.

“Wallahil Azim ko ki koma inda ki ka fito ko na lahira ya fiki jin daɗi. Idan ma hauka ke kan ki to nawa sun fi na ki”

Ganin yadda idon Sabreen ya firfito, goshinta yai ja, jijiyinta su ka mimmike ya sa Dr Kenneth ya fara bawa Farida haƙuri akan ta sake ta za ta illata Sabreen.

Najeeb kam tsayawa yai a gefe yana kallon ikon Allah.
Da ƙyar Farida ta haƙura ta sake Sabreen wanda ta faɗi ƙasa tana numfashin wahala, har da hawaye.

Cikin zuciyar sa ya ke tunanin ashe Najdah ta yi gaskiya da ta ce ma sa Farida is mentally not stable.

Zuwa yai zai taimakawa Sabreen ta tashi. Farida ta riƙe shi ” inka ɗaga ta na mutu kafira”
Bai ɗaga tan ba sai ma Dr kenneth ne da Najdah su ka ɗaga ta…

Ranan dai Sabreen ba ta sake dawowa ba sai washegari.
Duk zuwan ta gaishe shi sai dai ta zo da Najdah dai-dai lokacin da Mom ko Daddy ke wajen sa. Shegiya ta ji damƙan manya????…

Har yanzu dai bai gama tuno komai ba, yadda memory ɗin ke dawo ma sa tsilla tsille ne ba direct ya ke tuno abu ba. Wani lokaci sai anyi magana sai abinda aka faɗa ya triggering ma sa wani memory.

Yau ma magana ya ke da likitan sa a office likitan ya excusing kan sa yana amsa waya. Juyawar da zai yi ya kalli Tv da ke ɗakin likitan sai ga Sabreen a cikin TV. A church su ke ana ɗaura ma ta aure da wani, bayan priest ya ce you may now kiss the bride sai ga shi ɗaya actor ɗin ya kama waist ɗin Sabreen su na kissing. Najeeb ya rintse ido wassu abubuwa na dawo ma sa….

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣1️⃣

Dafe kan sa yai yana jin wani irin zogi. Komai ne ke son dawo ma sa lokaci guda. Likitan ne ya lura da yanayin sa.

“Are you Ok?”

Da kyar Najeeb ya ɗago kan sa idon sa sun yi ja.

“Mr Najeeb ka dinga yi a hankali, kar ka takura wa kan ka, ahankali za ka tuno komai”

Najeeb ya gyaɗa kai…

Tun bayan abinda ya tuno gameda Sabreen ƙoƙari ya ke ya tuno ya su ka yi zaman auren su da Farida. Although Najdah ta gaya ma sa ba auren soyayya su ka yi ba, he still wants to remember something gameda auren su. Yawancin abubuwan da ya ke ɗan tunowa gameda ita time to time bai wuce aikin su tare a office ba. Tun ranan da ya tuno abinda Mom tayiwa Aisha ya ke ƙoƙarin ɓoye wasu abubuwan da ya tuno. Ko ranan da ya tuno accident ɗin da yai bai gaya mu su ba, he pretends bai tuna ba.

Farida ce bashi abinci, su biyu ne a ɗakin. Duk da yanzu yanada ƙarfin jiki sosai zai iya cin abinci da kan sa amma Farida sam ta hana. Dole sai dai ita ta feeding ɗin sa, su yi ta daru akan rashin son cin abincinsa. Yana cin kaɗan idan ya ce ya isa Farida za ta hau shi da faɗa. Wani lokaci idan ta takura ya kan ƙara kaɗan amma ma fi yawancin lokutan kau da kai gefe yakeyi ya ƙi ci.

Yau ma ɗin ita ke bashi abinci.
“Aysherh” ya kira sunan ta. Ranan da ya fara kiranta da wannan suna ya ga farinciki da ɗoki tattare da fiskar ta, har da cewa “My Champ sake kira dan Allah”

Lokacin da ya tambayeta ko ya ya ke kiranta da kafin wannan abu ya sameshi ƙin gaya ma sa ta yi, tace ya kira ta da Aishern kawai. Shi kam sai ya ke ji kamar ba Aysherh ya ke kiranta ba. Sunan a bakin sa ya yi daban, like there’s more to sunan Aysherh da ya ke kira.

Yayi gyaran murya ya ce “Ehm Aysherh…Ehm….did we?” Ya sake gyaran murya
“Have we…..?”

“Ina jin ka mijina” ta faɗa tana goge ma sa baki da tissue.

Wannan karan daurewa yai ya ce “lokacin da mu ka yi zaman aure da ke muntaɓayin wani abu?”

Dariya ne ya cika ta amma ta gimtse ta ce “wani abu kuma?”

Sai da yai gyaran murya kafin ya ce “abun aure”

“Abun aure ai dayawa My Champ. Wanne a ciki?”

Ya marairaice ido ya ce “please Aysherh. Kin san abun da na ke nufi fa”

Daɗi kashe ni. Abin da zuciyarta ya faɗa kenan, wai Najeeb na hira da ita, hiran ma irin hiran su ta da.

“I’m serious Aysherh”

“Abubuwan aure ai dayawa My Champ. Akwai cin abinci tare, wanka tare, wasa da dariya tare, akwai kuma abubuwan da ake yi da dare, ko kuma ayi abun idan ɗaya ya ji abu sai ya taƙali ɗayan sai a haɗu ayi abubuwa. So wanne aciki ka ke tambaya?”

Maganan nan ya tuno ma sa da wassu abubuwa amma har yanzu bai iya tuno ko sunyi abun da shi ya ke tambaya ba.

“So, we did everything that couples do?”

“Mun yi komai hadda gyara”

Zaro ido yai lokaci guda kuma ya sa hannu yana tare gaban sa.

Farida ta fashe da dariya tana faɗin “to na nawa kuma. Bayan angama ganin komai”

Har lokacin bai ɗaga hannun sa ba ya ce ” you’re lying”

Tana cikin dariya Anas ya shigo.

“Wannan dariya haka, Farida ko dai ya tuno komai ne?”

Farida ta girgiza kai. As usual ya kawo ma ta wasu documents ne ta duba.

Anas ya gaida Najeeb wanda har lokacin yana kare gaban sa da hannu.

“Abokina ya dai? ko wani abu ya samu wajen ne?”

Pillow ya jawo ya sa a wajen kafin yai wa Anas wani mugun kallo.

“Mutumina ka godewa Allah da ya ba ka jarumar mace. Ba dan ita ba da kamfanin ka ta samu matsala”

“Ko a wanni duniyan ne secretary ta ke zama Oga oho?”

Ya kalli Farida da ido ya ce “what did you know Miss Salihu?”

Farida ta zaro ido, shi kuwa murmushin yaƙe ya mata ya maida hankalin sa kan Anas.

Abubuwa dayawa ne ke yawo a cikin ƙwaƙwalwarta. Kenan Najeeb ya tunata, komai ya tuna? ko kuma dai ba komai ba.

“Alhamdulillah mutumina. Ka tuna Miss Salihun ka, the stubborn Miss Salihu”

“Ko ba Miss Salihu ba ne ta sa min superglue a seat?”

Anas ya kwashe da dariya. Ita kuwa Farida jikinta ne yai sanyi.
Najeeb ba wai ya tuna abin ba ne da kan sa. Ranan ne Najdah ta nuna ma sa video ɗin da Anas ya nuna mu su ranan birthday ɗin sa, yana gani kuma wassu abubuwa su ka dinga dawo ma sa gameda Farida, musamman lokacin su na office…

Bayan Anas ya tafi, Farida ta ce ” My Champ ka tuna komai ne?”

“The last time i remember ba da wannan suna ki ke kirana ba. What changed?”

Da gayya ya gaya ma ta haka, shima rama abinda ta ma sa ɗazu yai.

“Saboda…” sai kuma ta kasa magana.

Ranan gaba ɗaya gwiwarta yai sanyi. Duk yadda ta yi dan ta fahimci ko ya tuno komai na rayuwar su amma ta ka sa. Sai ya dinga gwaleta idan ta tambayeshi…

Washe gari da safe ƙarfe goma sai ga Lukman. Bayan ya yiwa Najeeb ya jiki sai ya ke faɗa ma sa cewa gaskiya ya riƙe Farida da kyau domin ta ma sa abinda ba ko wacce macce ne za ta iya yi ba.

“Oh! and how do you know?”

Lukman ya ƙaƙaro murmushin dole ya ce “saboda na gani da ido na”

“Nagode da gaisuwa, Dr Lukman right?”

Lukman ya gyaɗa ma sa kai tareda barin ɗakin, chan ƙasan zuciyarsa kishi na cin sa…

“Shi kuma wannan daga ina ya ke?” Ya tambaya yana tsare Farida da ido

Ba tareda ta kalli idon sa ba ta ce “he’s my ex husband”

“Ashe ma bazawara na aura ban sani ba”

Ɗago rinannun idanunta ta yi tana ma sa wani kallo. Abinda ma zai ce ma ta kenan wai bazawara. Anya za ta taɓa samun matsayi a wajen Najeeb musamman yanzu da bai gama gane kan sa ba…

………………………….

Bayan anyi sunan ɗan Maijiddah da kwana uku AbdulWahab ya koma Lagos. Bai samu Aneesa a gida ba, dama ta ce ma sa Abuja za ta je. A washe garin ranan da ya dawo ta dawo. Ita ba ta ma san ya dawo ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button