SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Tana zaune a falo tana kallo tana cin pringles sai ga kiran wata ƙawar ta.

Bayan sun gaisa ƙawar ke tambayarta ya kishiyar ta.

” shegiyar fa haihuwa ta yi, namiji kuma”

Ɓangaren ƙawar ta ke ma ta faɗa akan ta yi sake da har ta bari Maijiddah ta haihu a gidanta.

“To ya zan yi Binta, kwanan baya har cikin ƙarya na ce ina da shi dan na samu attention ɗin AbdulWahab kuma na samu a lokacin. Daga baya na mata sharri akan ta tureni cikin ya zube. Da farko ya yarda daga baya ya ƙaryata zancen. I really dont know what to do again…”

Ko mi ƙawar ta ce oho. Aneesa dai cewa ta yi “ni kin san ba na son shige-shigen nan. Ka je ma duk su ci kuɗin ka a banza ba biyan buƙata”

Jayayya su ka fara yi da ƙawar akan zuwa wajen Boka, daga ƙarshe Aneesa ta kashe wayan tareda cewa za ta yi tunani akai.

“Nonye….Nonye”
Ta fara kiran mai aikin ta. Jin shiru ya sa ta miƙe tsaye, ai kuwa da sauri takoma ta zauna daɓas tana riƙe baki.

“Sweetheart” ta faɗa baki na rawa.

Yana tsaye ya harɗe hannuwan sa a ƙirji yana kallon ta, idon sa yai wani irin ja.

“Aneesa why? Why? Ki rasa abinda za ki yi sai ƙarya”

“I can explain AbdulWahab, please” ta faɗa tana haɗa hannuwan ta biyu.

“Wajen Boka ko, ki je Allah ya bada sa’a” yana faɗin haka ya haura sama.

Jikin ta na rawa ta tashi ta bishi da sauri…

Buga ƙofar sa ta ke yi amma bai kulata ba balle ya buɗe, ta zauna a bakin ƙofar tana ba shi haƙuri tana hawaye…

Kwanaki uku su ka gifta amma kalma ɗaya ba ta ji daga bakin AbdulWahab ba. Ta yi kukan ta bada haƙurin amma bai ma kulata ba balle ta san ko ya yafe ko bai yafe ba.
A rana ta biyar ya ce ma ta idan har ta zaɓi zama da shi to za ta ajiye aikin ta ta zauna ta kula da shi da kuma yaranta, amma idan ta zaɓi aikin ta to zai sawwaƙe ma ta.

It was a very tough decision for her. Tana son AbdulWahab tana kuma son aurenta. Duk da dai ta san ba ƙaramin asara za ta yi ba idan ta ajiye aiki amma kuma ba za taɓa zama bazawara saboda aiki ba. Ta kira Mama neman shawara, inda Maman ta ce ma ta ta zaɓi abinda ta ga ya fi ma ta, amma ta sani ba za ta taɓa samun wani miji kamar AbdulWahab ba musamman ma a shekarun da ta ke yanzu.
Ƙarshe dai shawaran da ta yankewa kanta shine ta ajiye aiki…

Duk da ta ajiye aiki hakan bai sa AbdulWahab ya koma ma ta kamar da ba. Cewa ma yai ta je ta bawa Maijiddah haƙuri. Girman kai ba zai bar ta ba, ta girmi Maijiddah sosai, kusan shekara shashida ta bata. Da ta ga uwar bari dole dai sai da ta kira Maijiddan a waya ta ba ta haƙuri. Maijiddah kam ta yafe tuntuni tunda mijinta ya gane gaskiya kuma ya yarda da ita ai an wuce wajen… kafin Aneesa ta samo kan mijinta sai da ta kai wajen wata ɗaya…

……………………………

Yau aka sallami Najeeb daga asibiti bayan kwanaki hamsin da huɗu da yai da farfaɗowa. A report ɗin da su ka bayar sun nuna cewa ba shida matsala, a hankali zai dawo da dukkan ƙarfin sa, haka kuma bisaga tambayoyi da kuma shaidar ‘yan uwansa sun tabbatar da cewa ya tuno kaso tamanin na rayuwar sa ta baya kuma a hankali zai ƙarasa tuna komai…

Gefen sa na dama Farida ɗayan kuma Najdah a haka su ka fito daga asibitin Daddy da Mom kuma na gaba farinciki yana nan tattare da fiskokin su. Motar Farida su ka shiga, yadda Najdah ke maƙalewa Najeeb ba dan su Daddy na wajen ba da ta gaya ma ta maganar banza.

Maimakon Najdah ta bi motar su Daddy sai ta shiga tasu motar.
Su uku ne a baya sun sa shi a tsakiya.
“Dan Allah ki fita ki bamu waje, mata da miji suna son ganawa da junan su”

“Wayaga mata. Ba inda zan je. Yaya na son kasancewa da ƙanwar sa”

“Tunda sirrin miji da mata ki ke son gani, Bismillah” ta faɗa tana hawa kan cinyar Najeeb, kafin ya ce wani abu ta haɗe bakin su, yana so ya tureta daga jikin sa saboda Najdah da ke motar amma gangan jikin sa ya betraying ɗin sa. Maimakon ya tureta sai ma ƙara matseta yai a jikin sa, yayinda kuma hannunsa duka biyu su ka fara yawo tsakanin bayan ta zuwa hips ɗin ta.

“Dreba tsaya zan fita” Najdah ta faɗa tana jan tsaki.
Sun fito daga gate ɗin asibitin kenan ko nisa ba su yi ba.
Ya samu waje yai parking

“Karuwa kawai” ta faɗa tareda banko mu su ƙofar motar.
Abdullahi dreba ya fara dariya ƙasa-ƙasa yana faɗin “to kema miji ya kwanta a asibiti tsawon watanni ba lafiya, yanzu ya samu lafiya ki zo ki liƙe ma sa, ai duk abinda ki ka gani ke ki ka jawo”

Lokacin da ta ji Najdah ta fita ta fara ƙoƙarin janye bakinta.
“My Champ” ta faɗa cikin sarƙewan numfashi tana nuna ma sa ƙeyar dreba wanda bawan Allah kam kiɗa ma ya sa a motar ya ƙure volume sosai, dan kar kunnen sa ya jiyo ma sa ba dai-dai ba.

Kallon-kallo su ka fara yiwa junan su, idon Najeeb yai wani ja guguwar sha’awa ta bugeshi.
Ya san a mota su ke amma kuma duk wani ƙoƙarin hana jikin sa aikata wannan abu ya ka sa, jikin sa har rawa ya ke yi. Ƙoƙarin tashi ta ke yi daga jikin sa gaba ɗaya. Ya maidata da sauri, “My Ch…” Najeeb bai bari ta ƙarasa ba ya jagoranci wannan kiss ɗin, wannan karan da zafi zafin sa ya ke yi, ya cire ɗankwalin ta ya sa hannun sa cikin gashin ta yana shafawa. Kafin ta ankara yai wani juyawa da ita sai gashi tana ƙasa yana samanta still bakin su haɗe da na juna. Ta san glass ɗin motar tinted ne amma kuma ko da Abdullahi dreba bai juyo ya leƙa su ba, ya san dole su na aikata wani abu a bayan motar.

Ƙoƙarin zuge zip ɗin doguwar rigarta ya ke ta yi saurin riƙe hannun sa. “A mota mu ke My Champ” ta faɗa lokacin da bakin su ya rabu. Ya jima yana kallon idon ta kafin ya tashi daga kan ta. Itama ɗin tashi ta yi ta ɗau ɗankwalin ta tana ɗaurawa. Tunda ya juyar da kam sa gefe bai sake juyowa ya kalleta ba, numfashi kawai ya ke saukewa da sauri sauri. Ita kan kwantar da kanta ta yi a kafaɗar sa tana ayyana abubuwa dayawa a ranta…

Najdah kiran Mom ta yi akan su dawo su ɗauketa, da ke motar su ta riga ta yi nisa.
Cikin Daddy da Mom ba wanda ya tambayi dalilin da ya sa ta sauka a motar su Farida. Tunda dama tun farko bai kamata a ce ta shiga ba. Ta zauna a gaban mota sai tsaki ta ke yi tana ƙara jin tsanar Farida. Ita fa tun day one da ta ga Farida yarinyar ba ta mata ba, balle yanzu da ta ke jin ina ma tanada yadda za ta yi ta raba Najeeb da Farida saboda tsanar da ta ma ta…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣2️⃣

Motoci ne cike maƙil a compound ɗin gidan lokacin da su ka shigo.
“Ya na ga gidan ya cika haka?”

Juyowa ya yi ya kalleta kallon irin kin fini sani ai.

Wayarta ta ɗauko ta kira numbar Mom.

“Mom gidan a cike sosai kaman wanda ake biki?”

“Dear, Walima ce za’ayi”

“Oh”

“Gamunan ma mun iso”

Katse wayan ta yi tana jira motar su Daddy ta shigo.

“My Champ” ta kira shi a hankali

Ɗaga ma ta gira yai.

“Wai an shirya ma ka Walima. Yadda aka cikan nan na san za ayi hayaniya, ko mu wuce kawai ka je ka yi wanka ka kwanta?”

Girgiza ma ta kai kawai yai.
Sai da Mom ta zo ta ƙwanƙwasa mu su window kafin su ka buɗe ƙofa su ka fito. Yana fitowa daga motan ya fara kallon gidan na su. Tabbas ya tuna gidan, hakanan kuma ya tuna cewa shi ya zana gidan, lokacin ma yana degree ɗin sa na farko ne.

Wannan karon Daddy ne ya kama hannun sa su ka nufi hanyar garden inda aka shirya Waliman.
Farida kam cikin gida ta wuce bayan sun yi musayar harara ita da Najdah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button