SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“Aishatu anya wannan uban turarukan bai yi yawa ba?” Ta tambayi kan ta tana shinshina jikin ta…

Wajen Daddy ya je a chan ɗakin sa, shima dawowan sa kenan daga rakiyan baƙi.

“Dad you called me”

“Ya ƙarfin jiki?”

“Alhamdulillah”

“Son abu biyu ya sa na kiraka. Na farko lokacin da ba ka da lafiya Anas ya turo magabatan sa kuma na bashi Najdah. Mun saka biki ƙarshen shekara lokacin ta ƙare karatun ta. Alhamdulillah along the line sai ka farfaɗo, saboda hankalinmu na kan samuwar sauƙin ka shiyasa mu ka jingine maganan aure a gefe. Amma yanzu tunda ka samu lafiya sosai me ka ke gani mu ɗaga bikin ne ko kuma a bar shi a date ɗin da ɗin?”

“Duk abinda ku ka ga ya dace ni bani da abin cewa”

“Abu na biyu shine maganar mahaifiyar ka. Najeeb dan Allah ka gyara tsakanin ka da mahaifiyar ka. Ta yi kewan ka sosai, na san yanzu ba kaman da bane tunda har kana kiran ta da kalmar uwa. Amma still ka raɓeta ka samu albarka ajikin ta. Uwa fa Uwa ce Najeeb…” haka Daddy ya cigaba da yi ma sa nasiha mai ratsa jiki

Ya jima yana hawaye kafin daga baya ya bawa Daddy haƙuri tareda alƙawarin zai gyara…

Ya so ya samu Mom a wannan dare sai dai kuma bai san waɗanne kalmomi zai yi amfani da su ba, shiyasa ya haƙura har sai ya samu nitsuwa sosai…

Ana murɗa ƙofa ta yi saurin rufe idon ta kamar mai bacci. Tana kwance ne tun ɗazu tana jiran kaza da kuma abinda ake yi bayan kaza sai dai Najeeb bai shigo ɗakin da wuri ba.

Jin bai zauna akan gadon ba ya sa ta ɗan buɗe ido ɗaya ta leƙa shi. Mug ne a hannun sa yana shan tea, ta sake buɗe ɗayan idon ta duba gefe da gefen sa da kyau ko za ta ga leda ko take away ba ta ga komai ba. Tana bin sa da ido har ya ƙarisa shan tea ɗin ya shiga banɗaki yai wanka.

Pyjamas ya sa ma su laushi baƙaƙe kamar yadda ya saba, ya zo ya kwanta gefen ta. Kashe wuta yai ya jawota jikin sa sannan ya fara bacci bayan ta ji bakin sa na motsi alamar addu’a yai. Ta jima tana ta tunani kafin bacci yai gaba da ita ba tareda abin da ta hasaso ya auku ba. Ba maganar kaza ba maganar abubuwa…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣3️⃣

Washe gari ma baƙi ne su ka yi ta zuwa gaisuwa, tun da safe har yamma. Kafin su samu sarari ma sai da aka yi kwana huɗu da dawowar shi gida…

Da sassafiyar Jummu’a ya shigo ɗakin mahaifiyar sa. Dad bayanan ya tafi wani taro a Minna.
Tana zaune akan sallaya tana jan carbi ya shigo.
Gwiwowin sa ya sa a ƙasa ya ɗaura kan sa a kafaɗar ta.
“Mon ki yafe min dan Allah, for years i treated you…”

“Shhhhhhh” ta dakatar da shi, hawaye ne ke zubowa a idon ta wani na bin wani.

“Son na yafe ma ka. Ba laifinka ba ne kaɗai, har da ni. You were young, you’re traumatize, maimakon na ja ka ajikina na nuna ma ka kulawa sai na barka hakanan har abin ya zo ya girma a ranka. I’m sorry son”

Ita hawaye shi hawaye. Uwa da ɗa sun jima rungume da juna kafin daga baya Najeeb ya janye jikin sa ya ce “Mom zan sake yin wani laifin. Ki yafemin kafin lokacin”

“Son minene?”

A hankali ya furta Sabreen…

………………………..

Farida ta shiga kitchen tana ƙoƙarin haɗa Alala saboda sha’awarta da ta tashi da shi yau da safe sai ga Najdah ta shigo kitchen ɗin. Da alama shigowa ta yi dan ta ɗauki wani abu, ba gaisuwa balle sannu da aiki. Farida ma ta yi kamar ba ta gan ta ba.

“Adama, Adama, Adama” Najdah ta fara ƙwala kiran sunan baiwar Allah.

“Wai ke wacce irin daƙiƙiya ce. Kin dai ga ba ta kitchen ɗin nan dai ko, sanin kan ki ne sarai tana shayarwa yanzu. Ki dinga kiran ta kamar wata ‘yar cikin ki. Matar nan idan ba ta baki shekara goma ba za ta baki takwas amma ki wage baki ki dinga kiran sunan ta kamar wanda ku ka yi wasan ƙasa tare. Adama…Adama”

“Kin ga bana son shishshigi Farida, ban yi da ke ba dan haka kada ki shiga harkata”

“A hakan za’ayi auren, yarinya ba tarbiya ba komai”

“Uban ki da uwar ki ne ba su koya min tarbiyan ba”

Maimakon Farida ta bata amsa sai ta zo ta kama hannun ta.

“Ki sake ni, ki sake ni Farida”

Jan ta ta ke yi Najdah na tirjewa, amma da ta ga uwar bari sai ta haƙura ta bi ta dan taga iya gudun ruwan ta, ta san ƙarshe wajen Mom za ta kai ta.

Ba ɗakin Mom su ka shiga ba sai ɗakin su Faridan.
Yana zaune akan kujera yana ƙoƙarin duba wassu takardu, yana so ya fara fita aiki ranan monday, tunda yanzu ya gane kusan komai gameda ayyukan sa.

Buɗe ƙofar da aka yi ya sa shi juyowa. Yanzu su ka gama daru da Farida kafin ta fita akan wai ta chanja ma sa tsarin da ya jera kayan sa.

Gaban Najeeb su ka tsaya kallon su ya ke yana so ya gano mi ke faruwa.

Farida ta zage hannu ta falle Najdah da mari. Shi kan sa Najeeb sai da ya tsorata da marin nan.

“Matar yayan ki na ke Najdah, ni ba kishiyar ki ba ce. Idan ba za ki bani girma da matsayi da Allah ya bani a kan ki ba. To kuwa ki shirya dan kafin ayi bikin ki sai na gyara miki zama a wannan gida”

Ta juya ta kalli Najeeb ta ce ” ka gayawa ƙanwar ka cewa ba na son raini, ko kuma idan na sa ma ta ƙahon zuƙa a gidan nan sai na zuƙeta zuut”
Ta juya ta fita ba tareda ta jira amsar da zai bata ba.

Najdah ta tsugunna a gaban Najeeb riƙe da fiskarta tana kuka.

“Big B she slapped me. Ba yau ta fara ba, she’s being doing this for along time now”

Dafa ƙafarsa ta yi ta ce “Big B ka rabu da ita, she’s not good for you wallahi ba ta son ka kuɗin ka kawai ta ke so”

Duk surutun Najdah bai ce komai ba kawai kallon ta ya ke. Bai rarrasheta ba dan haka da kanta ta bar kukan ta share hawayen ta.

“I love her Najdah” ya furta a hankali.

Najdah ta ɗan zaro ido dan ta yi mamakin kalaman Najeeb. Ita tunanin ta duk yadda ta dinga gaya ma sa aibun Farida lokacin yana asibiti abin ya shigeshi.

“Why? Big B why her? Akwai mata dayawa da ke son ka wanda su ka fi Farida komai. A hankali za ka ga wadda ta dace da kai”

“Because i love her”

Najdah ta haɗe rai.

“Ina son ki Baby, you’re my dearest sister. Na san abinda ki ke so na yi bai wuce na zaɓa tsakanin ki da Aysherh ba. Kar ki nemi hakan a wajena domin za ki sha mamakin wanda zan zaɓa”

“Big B…”

“Na yadda bakya son ta, ba ta kuma burgeki amma ina so ki ba ta girma a matsayin ta na wacce na ke so”

“Big B you’re confused, har yanzu ba ka san wacece Farida ba, har yanzu ba ka tuno rashin mutuncin da ta yi ta shuka ma ka ba. The girl is just a gold digger”

Najeeb yai murmushi ya ce ” ki na son Anas ko?”

Najdah ta yi shiru.

“Ba kya tunanin yadda ki ka ƙi ɗan uwan ki Mustafah ki ka amince da Anas haka ƙannen Mustafah za su dinga ganin Anas a matsayin wanda ke son yin auren jari”

“Accept this simple truth Baby. I love Aysherh. Bana tunanin kina yiwa Anas rabin son da ta ke mini”

To mi za ta ce ma sa? wani ƙorafi za ta kuma yi?.tunda wanda ta ke tunanin zai ɗau mataki akan Farida ya nuna ma ta yana tsananin son Farida. Gwiwa a sace ta tashi ta fita daga ɗakin…

………………………..

Yana ɗaura tie ta shigo ɗakin ɗauke da tray. Ta riga ta shirya tuntuni, fita ta yi ta ƙarɓo mu su breakfast.
Bayan ta ajiye tray ɗin ta ƙaraso gaban shi. He looked so handsome a grey three pieces suit ɗin kamfanin Brioni Vanquish II.

Hannu ta sa tana gyara ma sa tie ɗin.

“You look great My Champ”

“I think the right word is handsome” ya faɗa yana kissing hannun ta.

Murmushi ta yi ta ce”Mu je ka ci abinci”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button