SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Tea kawai ya sha sai ya ɗan tsakuri soyayyan dankali. Farida kam bayan toasted bread da ta ci guda biyu sai da ta ci soyayyen ƙwai da potato fries ɗin sosai.

Kallon yadda ta ke cin abincin ya ke yi yana sipping tea. Lokaci guda ƙwaƙwalwar sa ta tuna ma sa ranan da Farida ke cin cucumber a mota, yai murmushi.

“Na sani za ka ce wannan matar ta cika ci ko. Ba na juran yunwa ne ga ulcer da ta haɗumin biyu”

Kalmar ulcer da ta faɗa ya sa shi tunowa da ranan da ta sawa Sabreen yaji a gado har ta yi ƙaryar ulcer. Dariya ya farayi saboda tunowa da yai da abinda ya faru.

Tsayawa ta yi tana kallon yadda ya ke dariya, ya mata kyau sosai…

Driver ne ya ja su dan a asibiti sun hana shi tuƙi, atleast sai ya ɗau lokaci. Ita kuma Farida har yanzu ba ta iya tuƙi ba…

Su na fitowa daga mota ya bi building ɗin kamfanin da kallo, akwai so many memories a wannan waje wassu ya tuna su wassu bai tuna su ba. Tafiya su ke a hankali dukkan su biyun kowa da abinda ya ke saƙawa a zuciyar sa.
Dai-dai sun zo ƙofar shiga ya saka hannunsa cikin na ta. Kallon sa ta yi ya ɗaga ma ta gira…

Suna shigowa aka fara tafi, wajen ya sha decoration na flowers ga ƙatuwar banner da aka rubuta Welcome back Mr and Mrs Najeeb Jibo
Mutane dayawa da basu halarci waliman gidan su Najeeb ba su ka zo su na musabaha da Najeeb su na ma sa fatan alkhairi. Unlike Najeeb ɗin da yana amsa musabahar ne fiskar sa shimfiɗe da murmushi hatta ma su ƙananan matsayi kamar masinja ko cleaners sai da su ka gaisa da Najeeb.

Anas ne ya ja su suka je wajen da aka ajiye mu su cake, shi da Madam ɗin sa su ka haɗa hannu su ka yanka. A baki ya sa ma ta itama ta sa mishi a baki.
Sun ɓata kusan awa ɗaya a wajen kafin su ka shiga lifter zuwa third floor.

“Ga Mrs Comfort Masoyi ita ce sabuwar Sakatariyar ka”

Mrs Comfort ta rusuna ta gaishe da Najeeb.

Da Bismillah ta shiga office ɗin. Abin mamaki sai ta ga office ɗin ya chanja ma ta. Rabon da ta shigo office ɗin tun farfaɗowan Najeeb. Sau ɗaya ta zo ta yi meeting da wassu ‘yan china da su ke son siyan hannun jari amma ba ta basu dama ba.

Office ɗin ne aka raba biyu an saka glass an raba tsakani.

Ba ta san anyi gyaran nan ba hakanan ba ta san wayayi ba.

Waya ta ɗauko tana ƙoƙarin kiran Anas Najeeb ya karɓi wayan.
“I made the changes” ya faɗa yana kama hannun ta su ka shiga ɗaya ɓangaren da aka raba. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan kujera.

“You’re good in marketting strategies, abinda ya sa ki ka iya bunƙasa kamfanin nan kenan. Ba zan iya yin aiki ni ɗaya ba, kafin na gane kan zaren aikin sai an ɗau lokaci. But with you beside me komai zai zo da sauƙi”

“My Champ…”

“Shhhhh” ya sa hannu ya rufe ma ta baki.

“We’re going to work together now and always”

Faɗawa jikin sa ta yi tana kuka.

Ya fara bubbuga bayan ta yana lallashinta…

Shirye-shiryen bikin Najdah aka fara dan an mayar da date ɗin bakwai ga watan January kusan wata ɗaya da sati ɗaya kenan yanzu. Tun daga ranan da Najeeb yai wa Najdah magana ta dena shiga harkan Farida, magana ba ta haɗasu hakanan ba ta iya ma ta kallon banza kamar da…

Najeeb da Farida tare su ke fita aiki su dawo tare. Kusan komai ma ita ke jagoranta dan har yanzu wassu abubuwan sun sha ma sa kai.
Ana saura sati huɗu aure Mom ta sa aka fara yiwa Farida gyaran jiki tareda Najdah, wata mata ce aka kawo daga Sokoto. Farida dai dan Mom ta takura ne amma da ba abinda za ta yi, shi mutumin da za ayiwa gyaran jikinma domin shi har yanzu bayan kiss ɗin cikin mota ba abinda ya kuma yi. Daga ya rungumeta tsam ajikinsa idan za su kwanta sai wani lokaci ya kissing hannun ta ko goshi. Ita idan ba dan ranan a mota ta ji tudun abun shi ba, da sai ta ce ko ba shi da lafiya ne.

Da ke an ɗau hutun ƙarshen shekara ba sa fita aiki yanzu. Daga gida sai gida, ita Najdah har haushin Mom ta fara ji saboda yadda Mom ke wani ɗari ɗari da Farida, duk abinda aka mata na gyara sai ta ce a yiwa Faridan irin sa…

Saura kwana goma shashida a ɗaura aure sai ga Sabreen. Farida tun washegarin da aka yi walima ba ta sake ganin Sabreen ba. Da ke ba ta gabanta shiyasa ba ta tambayi ina ta je ba. Yadda ta ɗauka ma shine Sabreen ɗin ta bar ƙasar kenan har abada, amma da ya ke ba ta da kunya sai ga ta ta dawo. Ta san dai ba wai dan bikin Najdah ta zo ba, wani neman fitinan ne kawai…

Suna zaune a falo dukkan su, lokacin da ta shigo tareda tawagarta su uku. Biyu larabawa ne suma ɗaya kuma baturiya ce.

Najdah da Farida na zaune ƙafafuwan su na cikin ruwan ɗimi wanda aka cikashi da kayan ƙanshi.
Sabreen ta zo da gudu ta rungumi Mom tana kissing ɗin ta. Sai da ta gama shiriritar ta kafin ta nuna team ɗin da ta kawo. A matsayin ma su taimaka ma ta.

Ta kalli wata dattijuwa aciki wacce za ta kai 50yrs ta ce “this is Sarah, ita ce za ta kula da gyaran jikina” sai ta nuna ɗaya matashiyar wacce ba za ta wuce 25-26yrs ba. “Wannan ita ce Arfa, ita ce za ta dinga min kwalliya” ta nuna baturiyar ta ce “Najdah i brought her specially for you. Sunan ta Jean ita sexologist ce, i know you’re a virgin, so she’ll help you get rid of the fear and educate you on how to…”

Hahhahaha ta fashe da dariya.

Mom ce ta iya ce mu su sannu da zuwa ta ƙara da cewa ” Najdah da Farida ga Sabreen itama ta kusa zama amarya”

Kaman bugun guduma haka Farida ta ji saukan maganan Mom ” Sabreen ta kusa zama amarya. Amaryar wa?”

Ka sa zama ta yi a wajen ta cire ƙafafuwan ta acikin ruwan ta sa room slippers ɗin ta da ke gefe ta bar falon ba tareda ta ce komai ba. Ta sani Najeeb baya
nan, tun safe ya fita shi da Daddy. Waya ta ɗauka ta fara kiran sa amma bai ɗauka ba. Abu ɗaya ta sani idan har Sabreen za ta auri wani ba Najeeb ba to ba abinda zai sa ta baro chan ƙasar su ta zo nan ta zauna da niyyar wai ta zo gyaran jiki. Mi ke shirin faruwa?

Ranan har yamma ba ta kuma fitowa ba. Zazzaɓi ne ma ya rufeta. Tana nan haka Najeeb ya shigo ɗakin da sallama.
Ba ta kulashi ba har ya gama abinda zai yi ya zo ya kwanta gefen ta. Ƙanshin jikinta na ratsa duk wani jijiyar jini a jikin sa.

“Mi ya faru na ga ko sannu da zuwa ba ki min ba”

Idonta da su ka yi ja ta ɗago ta kalleshi ta ce “mi Sabreen ta ke yi a gidan nan?”

Ɗan dafe kan sa yai yana danne dariyar da ta taso ma sa.

“Oh sorry” ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce “i’m going to marry Sabreen, rana ɗaya za a ɗaura mana aure da su Anas. You see Aysherh ki na da kyau kuma kin min abinda ba zan taɓa mantawa da ke a rayuwata ba. You’ll always be my first wife amma kuma Sabreen will always be my first love”

Dariya Farida ta fara dan maganar Najeeb bai kama hankali ba kwata-kwata.

“Wasa ka ke yi Najeeb, kuma ba na son irin wasan nan, zuciyata za ta iya bugawa”

“I’m serious Aysherh. Na san Sabreen ta yi ba dai-dai ba a baya amma yanzu ta chanja. She loves me”

“Da Sabreen da soyayyar ta sun ci kutumar uban su. Wai Najeeb me ka ɗauke ni ne. Shashasha ko? Wallahi ba zan yadda ba. Yau ko mata uku za ka auro ka auro amma banda Sabreen. Wai tukunna kan ka ɗaya kuwa. Sabreen fa, Sabreen da ta gudu ana saura kwanaki a ɗaura mu ku aure, Sabreen da ta shiga harkan film tana sheƙa ayarta yadda ta ke so, Sabreen da kana kwance baka da lafiya ta shure ƙafa ta tafi ta barka wai za ta je ta yi film da Kwano Reeves ne ko Keanu Reeves ne ma…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button