SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

“I know, na san komai Aysherh but kin san soyayyar farko ba ta taɓa gushewa”

Hawaye fal a idon ta ta ce “ni tawa soyayyar fa? Duk son da na ke nuna ma ka a banza kenan, ba ka ɗauke shi a bakin komai ba ko?”

“Aysherh i have feelings for you amma kin san Sabreen…”

“Ya isa haka!” Ta daka ma sa tsawa.

“Ni ba zan zauna da kai ba matuƙar za ka auri Sabreen. Idan ma ba za ka iya zama dani ni ɗaya ba, ka nemi wata mana. Ko acikin cousins ɗinka ka aura amma banda Sabreen. Wallahi ba zan zauna da Sabreen ba”

“Aysherh please, na yafewa Sabreen ke ma ki yafe mata” ya faɗa yana kamo hannunta. Tureshi ta yi ta tashi ta je wajen closet ta fara haɗa kayan ta. Zan bar ma gidan ka, zan bar rayuwan ka, ka zauna da Sabreen ita kaɗai tunda matacciyar zuciya gareka”

“Kin san ina buƙatar ki, Kamfanina tana buƙatar ki. Please Aysher”

“Kai wanni irin mutum ne Najeeb. Ba ka sona, ba ka tausayina, ni dai kawai na zauna da kai saboda amfanin kamfani”

“Ba haka ba ne Aysherh please ki fahimceni”

Tsugunnawa ta yi a wajen tana kuka. Zuwa yai zai rarrasheta ta buge hannun sa ta ce ya bar wajen ta. Yana tsaye a gefe har ta gama kukan ta ta tashi ta shiga banɗaki ta jima a banɗakin dan aƙalla ta kai kusan minti talatin kafin ta fito. Direct gado ta je ta hau ta kwanta ta rufe dukkan jikin ta…

Yana jin kukan ta a ransa, he wants to tell her it was all a trick amma ya san halin ta, idan ya gaya ma ta komai za ta nuna rashin damuwa, hakanan kuma abinda ya shirya ba zai tafi dai-dai ba dan Sabreen za ta iya ganewa.

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣4️⃣

Ba baccin daɗi Farida ta yi ba, bacci ne ta yi na wahala. Da huturun sanyi aka tashi da asubahin ranan. Da ƙyar ta tashi ta shiga banɗaki ta yi alwala. Sanda ta farka Najeeb ya fito kenan yana shirin fita masallaci.
Tana idar da sallah ta nemi wata ƙatuwar rigan sanyinta wanda aƙalla ya yi shekara shida da ta ke amfani da shi. Rigan sanyin doguwa ce mai hula, dan idan ta sa yana wuce gwiwanta. Ko lokacin tana Jos idan ana tsananin sanyi idan ta sa shi ta sa dogon wando da socks shikenan ta yi maganin sanyi. Tana son rigan saboda Ummi ce ta siya ma ta…

Daga sallaya gado ta koma, kan ta ke wani mugun sara ma ta, ga cikinta da ke ta kukan yunwa.
Ba bacci ne a idon ta ba, asali ma jiyan ba ta kwanta da wuri ba. Yadda cikinta ke juyawa ya sa ta tashi dan ta sha gestid ko za ta ji sauƙi duk da kuwa ta san ciwon cikin ba na magani ba ne na yunwa ne. Tana tsaye a wajen dressing mirror tana shan maganin Najeeb ya shigo.
Ta yi kaman ba ta ganshi ba, maimakon 10ml da za ta sha sai ta ƙara wani 10ml ya zamo 20ml, tana tsayen ma wani jiri-jiri ta ke ji.

Yana tsaye yana kallon ta. Har ta ajiye maganin ta je ta hau gado. Bai ce ma ta ƙala ba, zuwa yai ya buɗe fridge ya ɗauko apple guda biyu da su ka saura a ciki. Dama shi kam bayan ruwa to fruits kawai ya ke sawa a ciki.
Sai da ya zauna gefen ta sannan ya ce “Aysherh tashi ki ci apple, bai da ce ki sha magani ba tareda kin ci wani abu ba”

Shiru ta yi ba ta ce komai ba.

“Aysherh”

A harzuƙe ta tashi ta na masifa “ina ruwan ka da ni, na ce ina ruwan ka dani. Na ci abinci, ban ci ba, wannan ba matsalar ka ba ce”
Juyawa za ta yi ta kwanta ya ce “Aysherh amma rigan sanyin kin nan gwanjo ce ko? As in Okrika, fairly used cloth…”

“Eeh shi ne, gwanjo ne, amma ka san me? ta fi designer cardigans ɗin da ka ke sawa. Tunda shekara da shekaru tana min maganin sanyi”

“Oh really, kinga banbancin ki da Sabreen kenan. Sabreen ba za ta taɓa saka irin wannan kaya ba”

“Mugu, butulu, ka bi ka damu mutane da Sabreen Sabreen, daɗin abin ma karuwa ce. Karuwa mai lasisi ma. Idan ita ba ta sa gwanjo ni a ina sa gwanjon ka ganni ka ɓata min aure saboda ka aure ni. Ka ga gwanjo kuwa sun min rana”

Sake miƙa ma ta apples ɗin yai wannan karan ta wafce a hannun sa.

Sai da ya ga ta fara ci sannan ya ce ” Sabreen ta tuba Aysherh. Kuma Allah Gafurun Rahimun ne zai gafarta ma ta”

“Allahu Akbar, Ashsheikh Najeeb Adam Jibo Rahimahullah. Aje dai a ƙarata da ragowar kafirai” fa faɗa tana hararar sa

“Yawwa Uwargida na, Aysherh mai gwanjo”

Dundu ta fara kai ma sa da apple ɗin a hannunta tanayi tana kuka, dayaga abin na yi ne ya tashi a gadon da sauri yana dariya…

………………………….

Ƙarfe shaɗaya ta fito dan ta maida plates ɗin abinci kitchen. Sabreen ta gani da tawagarta a falo su na duba wassu jewelries.

“Aishah” Sabreen ta kira sunan ta.

Farida ba ta juya ba, ta dai tsaya.

Sabreen ta taso ta zo gaban ta riƙe da sarƙa. Ta kai hannu za ta gwada sarƙan a wuyan ta Farida ta buge hannun.

“Kar ki taɓa ni!” Ta faɗa da tsawa.

“I wanted to give it to you Ayshah, i mean no harm”

“I dont want anything from you, you whore” ta faɗa tana barin wajen.

Sabreen ta yi murmushi dan ta san kishi ke cin Faridah…

Daga kitchen ɗakin Mom ta wuce. Mom ɗin ma jewelry box ta buɗe tana ware jewelries da za ta bawa Najdah da wanda za ta bawa Farida.

Da sallama Farida ta shigo, ko gaisuwa babu ta tsugunna a gaban Mom ta ɗaura kan ta a cinyarta tana kuka.

“Miya faru?, Aishah talk to me, miya same ki?” Dan ta tsorata da yanayin ta.

“Mom dan Allah ki ce Najeeb kar ya auri Sabreen, Mom mutuwa zan yi idan ya aureta. Mom dan Allah”
Tana maganan tana kuka.

“Farida, Najeeb yana son ki. He loves you so much”

“Mom ƙarya ne baya sona, idan yana sona ba zai ce zai auri Sabreen ba. Mom yaushe ma ya samu lafiya da har zai yi zancen aure. Wallahi idan har ya aureta ba zan zauna da shi ba” ta sake fashewa da kuka

“Farida sai ki barwa wata mace mijin ki, mijin da ki ke tsananin so”

“Mom ba zan iyaba, mutuwa zan yi, Mom please ki ma sa magana”

Tausayin Faridan ne ya kamata. Tsoron ta kar garin neman gira a rasa ido. Ya sa ta yanke shawaran gaya ma ta gaskiya.

“Barin gaya mi ki abinda ke faruwa, amma ba na so ki nuna kin sani”

Farida ta girgiza kai tana share hawayen da ke shimfiɗe a fiskarta…

………………………

Bisa shawaran Mom ta fara attending class ɗin da Miss Jean ke yiwa Najdah. Ranan da ta zo kunya ne ta cika ta, da ƙyar ta iya ƙarasa class ɗin. Baturiyar matar nan ba kunya ba komai ta ke bubbuɗe mu su abubuwa, tun daga sizes na girman abun zuwa yadda su ke idan suna cikin aiki. Bayan an gama bayani aka koma kan su mata. Da Faridan da Najdan dukkan su ashe shatara su ke cikon ishirin. Sun Jahilci abubuwa dayawa gameda jikin su da kuma yadda za su sarrafa mazajen su saboda kar a samu matsala…

A ranan lecture na biyu Jean ta fara nuna mu su different sex positions. Farida ganin abun na wuce gona da iri ya sa ta tashi za ta fita, sai ga Sabreen ta shigo.

Ɗan dariya ta yi ta ce “you’re still a virgin? You mean Noory never …” sai ta sake kwashewa da dariya.

Haushi ya cikata har wuya, ba dan ta san gaskiya ba, da yanzu ba abinda zai hanata marin Sabreen.

“Dont be shy Ayshah. Na san kin fi Najdah buƙatar lectures ɗin nan. Domin sai kin yi da gaske kafin ki samu kan Noory idan mu ka yi aure”

Farida ta cize leɓen ƙasa tana huci. Sabreen zuwa ta yi ta gayawa Jean saƙo sannan ta fita. Sai da ta fita Farida ta koma ta zauna, duk da dai tana jin kunya haka ta daure tana ƙaruwa da bayanan Miss Jean…

Najeeb kan bai fahimci komai ba saboda Farida ba ta nuna ma sa ta san plan ɗin shi ba. Har yanzu ba ta sake mishi fiska, maganan kirki ba ta shiga tsakanin su…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button