SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Tun daga James Anderson rayuwar ta ta sauya. She have sex whenever she wants to, tana shan giya kai har ƙwaya ta sha. Sai da ta shekara shida kafin ta dawo dai-dai ta dena shan giya da ƙwaya bayan dogon theraphy section da ta rinƙa zuwa akai-akai. Being a celebrity is not easy. Fans su yi ta tunzura ka. Fans ne su ka yi ta tunzura ta har ta je aka gyara ma ta shape ɗin bakinta saboda fans sun ce tana da kyau amma lips ɗin ta sun yi manya. Daga lips kuma ta yi butt enlargement…

Kiran wayanta aka fara yi hakan ya sa ta dawowa daga dogon tunanin da ta tafi. Tana zaro wayan ta ga Larry ne manager ɗin ta.

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣4️⃣7️⃣

Sabreen na ɗauka wayar Larry ya fara magana cikin masifa. Ba ta gane mi ya ke faɗi ba amma ta ɗau abu ɗaya, wato ta duba whatsapp na ta ya tura ma ta saƙo.
Ta cire wayan a kunne tana ƙoƙarin duba mi Larry ya turo ma ta.

Ba ta yi mamaki ba ganin video clip ne na wajen da ta ke durƙushe a ƙasa tana kuka yayinda Najeeb ke kwararo bayani, sai ɗayan kuma wajen da ta riƙe ƙafan Najeeb tana ba shi haƙuri.
Ta sani cikin su Jean, Arfah da Sarah da ta zo da su ne wani ya ɗau wannan video ɗin. But at the moment da video ɗin da wanda ya ɗau video ɗin duk ba sa gabanta. Babban damuwarta shi ne Najeeb, ta sani daga wannan rana ta rasa Najeeb rasawa ta har abada kenan.
If only ba ta gudu ba, da yanzu suna nan tare cikin farinciki.

Larry ya cigaba da kiran ta amma ta ki ɗagawa. Su Mom da Mouna ma sun yi ta kira amma ta ƙi ɗagawa.
All she needed is a quite place where she can cry her eyes out…

Receptionist da ya ga Sabreen sai da ta bashi tausayi. Wedding dress ne a jikinta amma kuma babu farinciki a tattare da ita ko kaɗan.
Ya miƙa ma ta key ɗin ɗaki tareda cewa “sorry Madam” ko kallon sa Sabreen ba ta yi ba ta ƙarɓi key ta ja akwatin ta. Da ace akwai yadda za ta samu jirgi da zai ɗauketa a wannan lokaci yai nisa da ita da Nigeria da za ta biya ko nawa ne ta samu wannan Jirgi. Amma dare ne kuma yau Friday ne.
Receptionist ɗin ya bi bayan Sabreen da kallo wanda ke tafiya a ƙafa ba ko takalmi ga takalman tana riƙe da su a hannu. Tunanin shi ya bashi ƙila ta zo daga wata ƙasa dan ta auri ɗan Nigeria ne shi kuma ya ƙi ta, ƙila ma irin online dating ɗin nan su ka yi…

Sabreen na shiga ɗakin hotel ɗin ta rufe ɗaki ta durƙusa a wajen ta fara kuka. Tana son ta yi kukan rayuwan ta, tana so ta yi kukan rashin masoyin da ta yi. Wannan karan da gaskiya ta ke son ajiye film na har abada bayan sun yi aure da Najeeb. Tana so ta zauna da shi, ta nuna ma sa kulawa, ta nuna ma sa tsantsan so. Yadda ta ke ta kukan tana dafe da ƙirjinta sai ga tari ya ƙufce ma ta. Hannunta da ta ke tare tarin ne ta ga jini, she’s coughing blood, nishi ta ke yi a hankali. Ko da za ta mutu she has to ask Noory for forgiveness. Ta tashi da ƙyar tana dafe bango idon ta na ganin bibbiyu. Da ƙyar ta buɗe ƙofa ta fito daga ɗakin tana furta Noory a hankali. Ko ta ku biyar ba ta yi ba ta faɗi a wajen…

………………………..

Da sauri Anas ya miƙe daga kan gadon ya shiga banɗaki da gudu. Ruwa ya ɗebo a wata roba ya fito da gudu jikin sa na rawa. A hankali ya ɗeba ruwan ya shafa ma ta a fuska nan da nan ta ja dogon numfashi.
“I’m sorry baby love, i’m very sorry” ya faɗa kaman zai yi kuka.

Wani matsanancin zafi da ta ke ji daga ta ƙasanta ya sa ta sake fashewa da kuka. Ji ta ke the pain was unbearable.
Anas ya fara hura ma ta iska a kunne yana ce ma ta sorry. Ganin kukan ba mai tsayawa ba ne ya sa shi tashi dan ya haɗa ma ta ruwan zafi…

“Sannu kin ji, i’m sorry my love” ita kam kukanta kawai ta ke yi duk da ma ruwan zafin da ya saka ta ya sa ta ɗan farajin sauƙin zogin da gabanta ke yi, ba kamar da farko ba.

Da ƙyar ya samo pcm a na shi ɗakin ya kawo ma ta dan ta sha. Shan maganin ma sai da ta ma sa kuka…
A hankali ya dinga bubbuga bayan ta har baccin wahala yai gaba da ita tana kwance a jikin sa…

………………………….

Farida ta zage ta cinye omelete ɗin nan tas, saboda ita ne ma ya haɗa ƙwai huɗu, shi kam ba zai taɓa iya cinye ƙwai huɗu a lokaci guda ba. Yana mamakin ma yadda duk yawan cin ta ba ta yi ƙiba ba.

“Alhamdulillah ba laifi ka iya soya ƙwai” ta faɗa tana kora sauran tea da ke mug ɗin ta.

Ganin yadda ya ke kallon ta ya sa ta ce “mi ye?” Da ɗan ƙarfi

“I love you”

“A hakan shi ne jiya ka kusan kashe ni”

Ya shafi kumatun ta ya ce “sorry my Queen, ni ma ba a son rai na ba ne”

“Kaman da gaske, abunda duk sauran Sabreen ne”

Dariya yai ya ɗau tray daga kan gadon ya ce ” kaman sauran Wannan likitan na gani jiya ko? Tunamin ma sunan shi?”

Ta jawo pillow ta wurgeshi da shi ya goce yana dariya…

Bayan ya dawo ɗakin ya ce ta fito ya nuna ma ta gidan ta kuma ga ɗakin ta. Kukan sakalci ta sa mi shi wai ba za ta iya tafiya da ƙafarta ba. Haka ya tsugunna ta hau bayan shi ya fita da ita daga na shi ɗakin. Ko’ina su ka zaga a cikin gidan, gidan ba ƙaramin burgeta yai ba. Ɗakin ta ya yi kyau sosai, akwai walk-in closet a ciki wanda ya ke cike da kaya.

“My champ ina da kaya a gidan su Daddy fa”

“Tuna min wa ki ke aure ma?”

Ta ɗan ranƙwashi kan sa a hankali ta ce “Mai girma Sir Najeeb, my Hero my Champion, my Mr BLTD”

Sanda su ka sauƙa falon ƙasa su ka ji doorbell ɗin na ƙara. Still Najeeb na goye da Farida ya je ya buɗe ƙofan.
Tasallah ce ɗauke da kwandon abinci.

“Alhaji an tashi lafiya?”

“Lafiya” ya faɗi a hankali yana matsa ma ta dan ta shigo.

Daga bayan Najeeb Farida ke yiwa Tasallah ina kwana.

A kan dining ta jera food warmers ɗin. Suna tsaye ta gama ta zo za ta tafi Farida ta ce “Baaba Tasallah ya su Mom?”

“Hajiya na lafiya, amma jiya a asibiti su ka kwana wannan ɗiyar yayanta ba lafiya”

“Wacce ɗiyar yayantan?”

Tasallah ta ce ” wannan Sabeera ko Sareena ne ma. Wacce de ta ke tafiyan magen nan”

“Sabreen?”

“E ita”

“Mi ya sameta”

Tasallah ta ce ba ta sani ba.

Bayan Tasallah ta fita dukkan su shiru su ka yi kowa da abinda ke saƙawa a ransa.
Tasallah kam ta fita tana mamakin Najeeb da Farida. Ko kunyar ta ba su ji ba haka su ka tsaya ƙato na goye da ƙatuwa. Chan zuciyar ta ya ce to ai duk cikin so ne…

Farida ce ta fara katse shirun da cewa “my Champ mu je sama ka kira Mom mu ji labarin mai jiki”

Ok kawai ya faɗa ya haura sama da ita chan ƙasan zuciyan ta yana addu’ar Allah ya sa Sabreen ta samu sauƙi dan ya san saboda shi ta shiga wannan hali.

Farida ce ta kira Mom ɗin tana tambayar ya jikin Sabreen, Mom ta ce da sauƙi domin ta farfaɗo yau da safe amma an ma ta alluran bacci tana bacci.

Farida ta ce “Allah ya ƙara sauƙi” Mom ta amsa da amin.

“Aishah” Mom ta kira sunan Farida a hankali

“Na’am”

“Dan Allah ke da son idan kun samu dama ku zo ku duba Sabreen. She’s in pains kuma ɗazu da ta farfaɗo sunan Son ta ke ta kira”

Wani tukuƙin kishi ne ya tasowa Farida. Lokaci ɗaya ta hango Sabreen da Najeeb. Kunnen ta ne ya fara jiyo ma ta kalaman Mom tana faɗin ” Ayshah ki yi haƙuri an ɗaura auren Sabreen da Najeeb saboda zuciyar Sabreen za ta buga idan ba ta samu Najeeb ba”

“Ayshah ki na jina?” Mom ta maimaita a karo na uku. Sai a lokacin ta ɗan dake ta ce “ba matsala za mu zo”

Tana ajiye wayan ta haɗa rai ta ce “Mom ta ce ka je ka duba Sabreen anjima”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button