SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ta yi murmushi ta ce “ƙila wayar ba ta kusa da shi ne, bari mu ɗan hira shi”
Lukman ya miƙe tsaye ya ce “Aishah zan wuce, kawai duk yadda ku ka yi da shi sai ki sanar da ni”
“Insha Allahu wannan karan za a dace”
A zuciyar sa ya amsa da amin amma a fili murmushi kawai yai.
Har ga Allah tausayin shi ta ke ji. Lukman ya haɗu ta ko’ina musamman ma da ya kasance mutum ne da ya ke da tarin ilimi a ɓangaren addini, hakanan yana da kyawawan halaye…
Ta cigaba da kiran Najeeb amma shiru. Hakan ya sa ta kira Abdullahi. Bugu ɗaya ya ɗauka. Ta tambayeshi ko har yanzu Najeeb bai gama abunda ya ke bane. Abdullahi ya ce yanzu ma muna hanyar gida ne.
“Gida kuma?” Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.
“Hajiya ai daga kamfanin ne ya ce mu wuce gida” ya amsa ba tareda ya fahimci mi ke faruwa ba.
Farida ta kashe kiran ta cigaba da kiran Najeeb amma still bai ɗauka ba.
Jakarta ta ɗauka ta fito.
“Ma, za ki fita ne?” Naomi ta faɗa tana murmushi.
Farida ba ta kulata ba ta cigaba da tafiya, har ta kai ƙofa sai kuma ta juyo ta ce “Naomi miji na ya zo ne?”
Naomi ta yi saurin cewa “No ma”
Farida ta fita cike da tunani a ranta…
……………………….
Tunda ya fito daga cikin Kamfanin ya ke jin shi kaman marar lafiya. Yana ganin kiran Farida amma ya ka sa ɗauka. Daga an kira wayan idan ya duba ya ga My Queen sai ya maida ta ya ajiye.
Ko wanka bai yi ba da ya shiga ɗaki ya kwanta a kan gado. Jin jikinsa ya ke kamar ba shi ba, kamar akwai abinda aka cire ma sa a jiki.
Yana kwance a haka har Farida ta shigo. Ganin sa kwance da kayan office a jiki ya sa ta san ba lafiya ba. Duƙawa ta yi ta cire ma sa takalman sa kafin ta ƙarasa dai-dai kan sa tana faɗin ” miji na lafiya? Are you Ok?”
Bai ce komai ba sai ma juya ma ta baya da yai.
Tunanin ta ko ciwon kan sa ne ya tashi. Dan tunda aka sallameshi daga asibiti yake fama da ciwon kai amma ya fi tashi ma sa idan ran sa ya ɓaci ko kuma he’s stressed. Likita ya ce a hankali ciwon kan zai tafi gaba ɗaya, amma kuma ya dinga samun isashshen bacci, sannan duk lokacin da ya jima yana aiki to ya tabbatar ya ware lokacin da zai kwanta dan ya huta. Hakanan ya guji duk wani abu da zai ɓata ma sa rai.
“My Champ dan Allah mi ya sameka? Wa ya ɓata maka rai?”
” ba na son surutu” ya faɗa a hankali
“Shikenan tunda ba za ka gayamin miya faru ba, amma dan Allah ka tashi ka rage kayan jikin ka za ka fi jin daɗin baccin”
Mirginawa yai ɗaya ɓangaren ba tareda ya amsa ma ta ba.
Ganin dai ba tashi zai yi ba ya sa ta tashi ta fita tunanin ta idan ya huce zai gaya ma ta koma minene.
Ɗakin ta ta wuce ta je ta yi wanka ta chanja kaya. Sai da ta kira Ummi su ka gaisa kafin ta wuce kitchen dan ta taya Tasallah aiki…
Su na jera abinci a dining ya fito ya sha wanka. Baƙin riga da wando ya sa sai ya ɗaura farin blazer a kai.
“My Champ fita za ka yi ne?”
“My Champ…My Champ” ta cigaba da kira har lokacin da ƙofar ta rufu. Baki tasake tana bin ƙofar da kallo. Ya kalleta sun ma haɗa ido kuma ya ji maganar da ta yi amma ya shareta.
Mi ke faruwa, abinda ta tambayi kan ta kenan.
Tun tana jiran shi nan da awa biyu har ta koma cewa nan da ƙarfe takwas na dare zai dawo amma shiru. Ta kira duka nambobinshi amma a kashe.
Tana kwance a kan kujera da ke falon ta ji takun sa. Ta yi firgigit ta tashi dan dama ba wai ta jima da bacci ba ne, baccin ma rabi da rabi ta yi.
“My Champ, My Champ” da sauri ya dinga taka stairs ɗin har ya ƙule ma ta.
Agogon falon ta duba ta ga ƙarfe goma har da rabi. Tunda su ka dawo gidan su bai taɓa wuce ƙarfe tara a waje ba…
Tashi ta yi ta bishi dan ba ta ga ta zama ba. Yana banɗaki lokacin da ta shigo. Itama banɗakin ta je za ta shiga dan ta taya shi wanka ko za su shirya daga nan amma ta ji banɗakin a rufe. Mamaki ya kamata dan indai wanin su ya shiga banɗaki yo baya rufewa tunda su biyu ne a gidan Tasallah ɗakinta na ƙasa.
Ta zauna a bakin gado tana jiran fitowar sa. Tana zaune ya fito, ya shirya yai ɗan shafe-shafe da feshe-feshen sa ya zo ya kwanta.
Mamakin yadda yai kamar babu mutum a ɗakin ya sa Farida ka sa magana. Ganin ya ja bargo ya kwanta ya sa ta lalubo sauran maganan da ke bakin ta ta ce “My Champion dan Allah ka yi haƙuri, idan ma wani laifin na maka ka yi haƙuri ka yafemin. Dan Allah miji na ka min magana. Ka gaya min laifina” tana maganan ne kaman za ta yi kuka
“Idan ba za ki iya kwantawa shiru ba, to ki koma ɗakin ki”
Kan ta ya ɗaure. Najeeb ba zai taɓa gaya ma ta haka ba, ko lokacin da ba sa shiri ma duk shirmen ta ba ya cewa ta bar ɗakin.
“Miji na dan Allah, hankalina ba zai kwanta ba idan ban san laifin da na yi ma ka ba”
tsaki yai ya tashi ya ɗau pillow ya koma kan kujera ya kwanta.
Haushi ya cikata. Idan ma laifin ta mishi bai ci ya ma ta wannan walaƙancin ba. Ta ja tsaki itama ta kwanta, a zahiri ranta na raya mata kar ta kuma bashi haƙuri zai zo da kan sa ya bata amma kuma chan cikin ranta tana tsoron wannan chanji bagtatan da Najeeb yai ma ta. Ta dinga tariyo abubuwan da su ka faru ko za ta tuna wani furuci ko wani abu da ta ma sa da zai iya ɓata ma ta rai amma ba ta gano komai ba. They are just fine, tun jiya har safiyan yau, infact san da zai fita a office ma sai da ya kissing ɗin ta sannan ya kissing cikin ta amma komai ya wargaje ne tun daga tafiyan sa. To ko a inda ya je ne aka ɓata ma sa rai? To ai koma wani ya ɓata ma sa rai bai kamata ya sauke fushin a kanta ba musamman saboda condition ɗin da ta ke ciki.
Da ire-iren waɗannan tunani ne bacci ya sace Farida.
Da asuba ma gum ya ma ta ba magana. Bayan ya dawo daga masallaci ta gaishe shi amma bai amsa ba. Haka kawai jikinta yai laushi ta fashe ma sa da kuka. To her uttermost shock maimakon ya rikice ya fara ba ta haƙuri sai ya shige banɗaki ya barta zaune tana kuka.
Innalillahi kawai ta ke ta maimaitawa a fili.
Najeeb ne zai ga tana kuka ya share, yai kaman bai ganta ba, gaskiya da matsala.
Ta zauna har ya fito ya fara shirin fita office still ignoring her. Tsoro da fargaba su ka cika ma ta zuciya.
Ba ta san ma ya za ta fassara wannan yanayi ba. Wannan yanayi mai kama da mafarki ko almara.
Wai Najeeb ɗin ta ke ma ta wannan walaƙancin. Yadda ta ke zaune tana kallon sa haka ya ƙarisa shiryawa ya fita daga ɗakin. Tunda su ka shirya ya dena fita da sassafiya haka, tunda tare su ke fita office ɗin, amma sai ga shi bayan ma yai fitar sassafiya bai ma damu ya san ko wani hali ta ke ciki ba balle ya ji ko za ta fita office ko ba za ta je ba.
Farida ta jima zaune a kan sallaya ta rasa ma abinyi Allah kawai ta ke kira a ranta. Dan wannan sauyi ya fi ƙarfinta, nan gaba kaɗan za ta iya shiga wani hali…
Shi kuwa Najeeb yana shiga mota ya ce Abdullahi ya kai shi gidan su Naomi. Tun jiya Abdullahi ya shiga ruɗu, ya kai Najeeb kamfani inda ya ɗau Naomi su ka fita, wani haɗaɗɗen restaurant su ka je daga nan ya kai su wata babbar shopping Mall inda su ka fito da kaya niƙi-niƙi. Gidan su Naomin ya kai su ta shiga ta ajiye kaya sannan ta sake shiryawa cikin wassu matsatstsun kaya ta fito.
Sunan hotel ɗin da Naomin ta faɗa ne ya sa shi sake maimaita sunan da ɗan ƙarfi alamun mamaki.
Najeeb ya ce ya kai su inda ta ce. Lokacin kusan shida na yamma ta wuce, har ma wassu wajen ana kiraye-kirayen sallan magriba. Sun kusa isa hotel ɗin Daddy ya kira Najeeb akan ya zo yanzu-yanzu.
Najeeb ya cire kuɗi ya bawa Naomi akan ta je ta jirashi. Idan ya dawo daga wajen Daddy zai zo.
Bai bar wajen Daddy ba sai ƙarfe tara na dare. Har sun kama hanyar hotel ɗin Naomi ta kirashi akan ta koma gida an kirata mamanta ba lafiya. Wannan ya sa su ka dawo gida…