SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Naomi ta shiga mota tana zuba murmushi. Cikin kayan da su ka siyo jiya ta sa wani shegen gown ɗan guntu da shi. Har gashin wig da ke kamta ta chanja shi. Ta kamo hannun Najeeb tana kaiwa kan nonuwanta tana shashshafa su. Najeeb bai hana ta ba bai kuma yi yunƙurin yin wani abu ba. Kallon ta ya ke yi zuciyar sa na raya ma sa abubuwa dayawa. Naomi ta kai baki za ta kissing Najeeb Abdullahi ya ce ” Alhaji yau Hajiya ba za ta aiki ba ne?”

Naomi ta koma baya tana hararan ƙeyar Abdullahi ita shaɗaf ta manta da wani driver. Abinda ya cika ma ta zuciya shine yadda za ta ji idan Najeeb ya shigeta. Yau kan ko ma wani irin uzuri ne ba za ta yadda ba sai ta san yadda za su je hotel su je su yi abubuwa…

Farida kam wani zazzaɓine mai zafi ya rufeta.
Kusan ƙarfe shaɗaya sai ga Sabreen ta kirata.

“Mi ya sa za ki min haka? Ba na son shiga rayuwar kowa Ayshah”

Ta sani ƙila Lukman ya kira ta ne dan jiya ta bashi numbar Sabreen ɗin.

Ta danne duk wani baƙin ciki da ke ranta ta shiga ba ta labarin Lukman a taƙaice. Ta ƙare da cewa ” Sabreen kince kina son gyara rayuwar ki. Shiyasa na miki kwaɗayin ki kasance tareda mutumin da zai taimaka miki wajen cimma burin ki. Lukman mutum ne da zan iya bugan ƙirji na ce shi ɗin namiji ne na gari wanda ya san kima da darajar mace. Wanda ya ke da ilimi ya ke kuma ƙoƙarin amfani da wannan ilimin da Allah ya bashi. Amma idan kina ganin na miki shishshigi a rayuwar ki to kiyi haƙuri”

Shiru Sabreen ta yi na kusan rabin minti kafin ta ce za ta yi tunani a kai. Farida ta kashe wayar tana fatan Sabreen ta amince da Lukman. Bayan wayan su da Sabreen shiryawa ta yi dan ta je gida. Ko idan ta ga Ummi hankalin ta zai kwanta har ta iya tambayarta shawara bisa yadda za ta ɓullowa wannan baƙon lamari da ta tsinci kan ta a ciki…

SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….

Azizat……✍
Wattpad @000Azee

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

0️⃣5️⃣2️⃣

Aure Rahama ne, musamman idan ka samu kwanciyar hankalin mijin ka. Ummi har wani ƙiba ta ƙara ga haske da ta yi, annurin fiskar ta ya ninka na da.

Kunun Aya da Ummin ta yi ta kawowa Farida. Farida ta ƙarɓa ta tsiyaya a kofi. Ta riƙe ƙofin amma ba ta kai baki ba. Zuciyarta ne ya tafi ga abinda ke faruwa da ita tsakanin jiya da yau.

“Farida lafiya?” Ummi ta tambaya ganin ‘yarta ta yi nisa cikin tunanin da ta ke.

“Dan Allah Hajiyata ina da tambaya”

“Minene?”

“Shin dama akwai lokacin da Namiji zai juya ma ka baya ne bayan kuna zaune lafiya?”

“Kin yiwa mijin ki laifi ko?”

“Ummi ba abinda na ma sa fa, idan ma akwai to ni duk iya tunani na ban gano ba. Ummi na bashi haƙuri amma ko kallo ban isheshi ba”

Ummi ta yi shiru tana nazartar Farida wanda damuwa ya bayyana ƙarara a fiskarta.

“Yanzu haka cikin yawar maganar ki ki ka gaya mi shi abinda ya ɓata ma sa rai”

“Najeeb bai taɓa fushi dan na gaya ma sa magana. Ba halinsa ba ne”

“Yanzu dai idan kin koma ki tsugunna har ƙasa ki bashi haƙuri. Ko ma minene Insha Allah za ki ga ya sauko”

So ta ke ta yiwa Ummi bayanin yadda Najeeb ya iya ganinta tana kuka amma ya wuce bai nuna ya damu ba. Amma kuma kar hakan ya sa Ummi ta shiga damuwa.
Ta daure ta ce “Insha Allah zan yi hakan”

“Dan Allah ki riƙe addu’a sosai. Domin addu’a da haƙuri su ke riƙe aure”

Farida ta ce “na ji Hajjaju na”

Ƙoƙarin sake fuska ta yi dan kar Ummi ta sa damuwa a ranta…

…………………………..

Shigar su ɗakin hotel ɗin Naomi ta shiga cire kayan jikin ta. Najeeb na tsaye bai iya yin komai ba. Sai da ta gama fidda komai na jikinta sannan ta fara jujjuya jikinta tana faɗin ” ya ka ga sexy body. Ko’ina a cike ya ke fam domin ka”

Idon sa yai ja zir yana fidda numfashi da sauri-sauri. Idon ta ke sa shi samun nitsuwa, idon ta ke sa ya ji sanyi a ransa. Amma yanzu da ta ma sa tsirara sai ya ke jin wani ƙunci da baƙin ciki, kan sa ne ya hau sarawa ya dafe goshin sa yana jin kan kaman zai tsage biyu.

“Sweetheart mi ya faru? What’s wrong? Are you sick?” Naomi ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe shi. Gaba ɗaya rikicewa yai yana jin kamar idan ya sake goshin sa kan shi fashewa zai yi.

Ganin yadda ya ke yi ya sa Naomi ta tsorata, ta shiga maida kayan ta…

……………

Tun kan su isa asibiti Abdullahi dreba ya turawa Farida text akan Najeeb ba lafiya su na hanyar asibiti.

Ta fito daga wanka kenan ta ji ƙaran shigowar saƙo. Da sauri ta je ta ɗau wayar saboda tunanin ta Najeeb ne ya ma ta reply ɗin texts ɗin da ta tura ma sa ɗazu.
Tana ganin Abdullahi hankalinta ya tashi. Ta buɗe saƙon da sauri.

Oga ba lafiya muna hanyar asibiti

Innalillahi ta faɗa tana kiran numbar Abdullahi…

Su na zuwa asibitin aka shiga da shi emergency saboda kafin su isa asibitin ya riga ya suma.

Naomi jikinta ɓari ya ke yi. Tsoro biyu ne a ranta, na farko kar asirin da ta ma sa ya zama ya karye na biyu kuma kar Najeeb ya mutu domin za ta shiga hali na ƙunci ga zargin ta da mutane za su yi…

A birkice Farida ta shigo asibitin. Ganin Abdullahi da Naomi su na tsaye cirko-cirko ya sa zuciyar ta ya karaya.

“Malam Abdullahi mi ya samu miji na? Ina ya ke?”

“Hajiya dan Allah ki kwantar da hankalin ki. Insha Allahu ba abinda zai sami Oga”

“Ina ya ke?” Ta faɗa da ƙarfi.

Kafin Abdullahi yai magana aka buɗe ƙofan ɗakin da ya ke. Da sauri ta ƙarasa gaban likita tana tambayar lafiyar Najeeb.

“Hajiya yana bacci yanzu. Sai dai dan Allah ku dinga kiyaye ɓacin ransa, yanzu haka jinin sa ne ya hau sosai”

“Can i see him?” Ta faɗa da raunatacciyar murya.

Likita ya ce e amma ta bari za a chanja ma sa ɗaki yanzu.

Su na tsaye aka fito da shi akan gadon marasa lafiya, aka turashi zuwa ɗakin da aka ba shi.
Farida da Abdullahi su ka bi nurses ɗin har ɗakin da aka maida shi, yayinda Naomi ta juya da baya ta tafi. Ta ji kaf abinda likita ya ce, amma zuciyarta ta rasa gane ko mi ya sa ran Najeeb ya ɓaci har ta kai ga haka. Normal su ka je hotel ɗin, infact da murmushi a fiskar sa lokacin da su ka shiga ɗakin. Tana cikin keke tana tariyo duk abinda ya faru tun safiyar yau. Ba wani abinda zai ɓata ma sa rai sai dai…. karaf ta tuna dai-dai lokacin da Najeeb ya fara chanja fuska. Tabbas tsiraicin ta da ya gani ne. Idan har saboda ba su yi aure ba ne ya ke jin ba zai iya kusantar ta ba to tabbas za ta gaya mi shi su yi aure nan ba da jimawa ba…

Awa uku kafin Najeeb ya tashi, lokacin duk ‘yan gidan su sun zo har da Sabreen. Kowa tambayar abinda ya faru ya ke amma Farida ba ta da bakin magana tunda itama ba ta sani ba. Tunaninta ko saboda ita ne ya shiga wannan hali. “My Champ laifin mi na ma ka ne?” Ta faɗa a zuciyarta.

Daddy ya tambayi Abdullahi ko daga ina su ke. Ya san matuƙar ya faɗi gaskiya to iyayen Najeeb za su shiga tashin hankali musamman ma Farida da ciki gareta.
Ya chanja maganar da cewa sun je wani site ne yai magana da ma’aikatan da ke wajen to da su na dawowa shi ne ya fara riƙe kan sa yana nishi sama-sama.

Daddy ya ce ” Allah shi kyauta, amma daga yanzu duk wannan aikin fita supervision ɗin ya isa haka. Anas ko wani daban zai dinga zuwa”

Lokacin da ya farfaɗo garau ya ke jin sa sai dai rashin ganin Naomi a wajen ya sa ya ji ba daɗi. Yana son tambaya amma Mom da Farida sun ƙi bashi dama kowa nan da nan ya ke da shi. Ya haƙura ya zuba mu su ido.
Chan dare aka sallamesu saboda ya ce ba zai kwana ba, shi lafiyarsa lau…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button