SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Anas ya ce ” ai mutumina sai ka ganta kawai. Wannan karan kai da chanja Secretary sai dai in ita ce ta ajiye aikin”…
Sai da Najeeb ya tsaya har Hajiya Mama ta gama ganin likita sannan ya maida ta gida. Da zai tafi kamar kullum sai da ta tsokale shi
“A dawo lafiya tuzuru”
“Ke fa tsohuwar nan kinada matsala” ya faɗi yana ɗan hararanta
“Matsala ta ɗaya ce, kai aure ka ajiye iyali kamar kowa. Ko sai ka gama tsohewa kafin kai auren”
“Ke zan aura ai, zan ɗau ragowar Alhaji Mustafah”
“Allah ya jiƙan rai, ai shi bai fi rabin shekarunka ba ya ajiyeni a gidan sa”
“Tsohuwa na tafi, kar ki riƙeni da surutu”
“Allah ya bada sa’a tuzuru”
Girgiza kai kawai yai sannan ya fice daga falon. Idan da sabo ya saba da tsokalar kakar ta sa, wanda da ita ya ke sakewa yai walwala kamar mahaifiyar sa. Kulawar da bai nunawa mahaifiyar sa ba a Hajiya Mama ya ke ba wa…
????SAKATARIYA TA????
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Free page
0️⃣0️⃣5️⃣
Daga Najeeb constructions kai tsaye gida Farida ta wuce, ba ta samu Maijiddah a gida ba dan haka kaya ta chanja su ka wuce kasuwa da ƙanwar Maijiddan, amarya Salima. Da ke ita ɗin tafi Hajara mutunci shiyasa ta su ta ɗan zo ɗaya da Farida, duk da ba ta kai Maijiddah kirki ba inji Faridan.
Ɓangaren Maijiddah kuwa da ta je ta samu jikokin Hajiya Yelwa suna karyawa dan haka sai da ta jira su ka gama sannan ta mu su kitson, da ke ba wannan ne karan farko da ta ke mu su kitso ba, su na yi su na hira. Yawanci in sun zo hutu wajen Hajiya Yelwa to ita ke mu su kitso.
Ta tsantsara mu su kitso mai kyau harda adon beads. Dama ga yaran ‘yan gayu da su. A Lagos su ke da zama ko hausan kirki ba sa ji. Maryam da su ke kira da Baby saboda sunan Hajiya Yelwa da ta ci ‘yar shekara bakwai ce, sai ƙaramar Alizah ‘yar shekara huɗu.
Maijiddah ta na zaune a ɗakin Hajiya Yelwa tana jiran ta, ta riga ta gama yiwa yaran kitso tun ɗazu amma Hajiyar ba ta nan, ta ce kuma ta jira ta har ta dawo.
Tana zaune kan carpet tana danna ƙaramar wayarta ƙirar Tecno wanda ya ji jiki ya tsufa. Tun wanda Yaya Faruƙ ya siya ma ta ne lokacin da ta yi sauka shekara huɗu da su ka wuce.
Ba ta ankara ba ta ji shigowar Alizah ɗakin da gudu. Ɗago idon da za ta yi ta ga ƙatuwar kyanwa ta yo kanta, ƙwalla ƙara ta yi ta hau gadon Hajiya Yelwa da sauri, ai kuwa kyanwar ma kawai sai ta hau gadon da alama kyanwar gudun Alizah ta ke. Maijiddah ba shiri ta dira a gadon ta nufi ƙofa da gudu. Ɗaga labulen da zai yi yai karo da ita, da ke guntuwa ce kanta ya tsaya ma sa iya ƙirjinsa. Ƙoƙarin tureshi ta ke ta wuce dai dai nan kyanwar ta shuri ƙafarta ta fice daga ɗakin. Laushin jikin kyanwar da ya taɓa ƙafarta ya sa Maijiddah ta yi suman tsaye a wajen.
Alizah ta fara cewa ” Daddy, please catch the cat for me”
Bai saurari yarinyar ba, ya ɗauki Maijiddah cak yai kan gadon Hajiya Yelwa da ita. Miƙar da ita yai sosai sannan ya cire ma ta hijabi dan ta samu iska ya shigeta sosai, Ƙaramin fridge da ke ɗakin ya buɗe ya ɗau goran ruwa mai sanyi. Ya zuba ruwan a hannunsa ya shafa ma ta a goshinta da wuyanta amma still ba ta farfaɗoba. Ya sake yin haka a karo na biyu wanda yana shafa wuyanta da ruwan sanyin ta jaa dogon numfashi ta buɗe ido, ta fara ƙoƙarin tashi dan ta zauna, ya sa hannu ya tallafa ma ta tareda faɗin “relax”
Sai alokacin ta fara wuri-wuri da ido saboda ganin ba hijabi ajikinta ɗankwalin kanta ma ya zame.
“Duk a dalilin kyanwa ki ke son hallaka kan ki. Miye abin gudu a jikin kyanwa?”
Ba ta bashi amsa ba sai ma ta sunne kanta cikin cinyoyinta. Ƙananun ƙitson kalaba (braids) da ta yi su ka zubo.
Ganin yadda gashin ke da tsantsi ya sa shi taɓawa dan ya tabbatar gashin kanta ne ba na aro ba (wig). Yana son mace mai gashi, haka nan ya tsani mace ta ƙara gashi abinda har yau matarsa Aneesah ba ta dena sawa ba kenan tun yana faɗan har ya gaji.
Tabbas gashin ta ne ya faɗi a ransa. Ga shi baƙi ga tsawo ga tsantsi.
Shigowar Hajiya Yelwa ya sa yai saurin cire hannunsa.
“Alhamdulillah!, ka ga yadda na tsorata da Alizah ta ce wai Hauwa’u ta mutu”
Yai saurin miƙewa ya ce ” ai Hajiya ba dan ina wajen ba ƙila mutuwar za ta yi. Kin ga yadda ta firgita kuwa, sumewa fa ta yi”
“Ai Hauwa’u kam sai dai Allah shi albarka kawai. Tukunna ma waya fito da kuliyar ne?”
Alizah ta ɓuya bayan Daddynta dan ta san ita ce ta tafka aika-aikar nan. Tun kafin Maijiddah ta zo Hajiya Yelwa ta sa aka rufe kuliyar kuma ta mu su kashedin kar su yadda su buɗe ta.
Hajiya ta kama hannun Maijiddah ta ce ” dan Allah ki yi haƙuri kin san sha’anin yara. Fatan ba ki ji ciwo ba?”
Maijiddah ta girgiza kai sannan ta lalumo hijabinta ta saka.
Yana tsaye ƙikam yana jira ta ɗago yaga fiskarta da kyau, ɗazu cikin ruɗu ya ke bai tsaya ya kalleta sosai ba. Sai da ya ƙare ma ta kallo sannan ya ce “Hajiya an gama haɗa kayan ne?”
“Angama Yaya, na ce da Faty ma ta kai su cikin mota”
“Barinje in gani kar su yi mantuwa”
Har ya kai bakin ƙofa sannan ya sake juyowa ya kalleta, har a lokacin bata gama nitsuwa ba jikinta na ɗan kakkarwa, yai murmushi sannan ya fita…
Hajiya Yelwa sai da ta tabbatar Maijiddah ta nitsu sannan ta sa autarta Faty ta raka ta har bakin gate duk da kuwa Fatyn ta tabbatar da an sake kulle kuliyar.
Hannunta riƙe da ledar da Hajiya Yelwa ta bata su ka fito da Faty.
Yana gindin mota ya ga fitowar su dan haka yai saurin ɗaga wa Faty hannu alamar ta zo.
“Kinga barinje Yaya na kira na” Faty ta gayawa Maijiddah.
” Lah ba komai, sai anjima” Maijiddah ta faɗi ta yi hanyar gate ɗinsu. Ba ta yi wasu taku mai yawa ba Faty ta ƙwala ma ta kira.
Da ta juyo ta ma ta hannu alamar ta zo. Tsayawa ta yi ta rasa mi za ta yi. Ga Daddyn su Alizah ya ƙura ma ta ido.
“Ki zo inji Yaya” Faty ta faɗi da ɗan ƙarfi. Ba yadda za ta yi haka ta fara taku a hankali har ta kai wajen motar, gefen Faty ta tsaya tana kallon ƙasa a hankali ta furta ” ina kwana”
“Ki shiga ya kai ki a mota” Faty ta faɗi tana ɗan murmushi ƙasa-ƙasa.
A hankali ta ce ” Lah Faty sai ka ce ba ki san gidan mu ba, ƙasan layi ne ba nisa”
“Wato dai ladar ne ba kya so na samu” Ya katse ta
“A’a Yaya, Allah ba nisa. Na gode”
” ki shiga mota ko na sa akawo kyanwar ɗazu”
Ai cikin firgici ta kama handle ɗin ƙofa tana kokawa da shi. Faty ta fara ma ta dariya.
Shi ma murmushin yai sannan ya danne key ɗin hannunsa ƙofar ta buɗu…
Sai da su ka fita daga cikin gidan ya ɗan kalleta ya ga ta takure gefe ya ce ” ki na tsoron kar na sayar da ke ne?”
Ta girgiza kai
“Ko nima ina da kamannin kyanwa ne”
“A’a”
“To ya kika takure, kin ƙi ki sake jiki haka nan ba ɗan hira”
Shiru ta yi dan ba ta san mi za ta ce ba. ” ashe ke ce me yiwa Hajiyata kitso. Kin san yadda ta ke yabonki kuwa. Ga ki ‘yar ƙarama da ke, anya kin kai shashida kuwa?” Yai tambayar ne dan samun damar gabatar da ƙudirinsa, yanayin tsayinta da ƙaramin fiskarta ya ke ganin kamar ba za ta kai 18yrs ba shi kuma a gaskiya ba zai iya auren under 18 ba.
“Na wuce mana” ta faɗa a hankali
“Faɗamin gaskiya, shekarun ki nawa?. Idan ki ka min ƙarya ma zan gane”
“20”
“Ishirin! Kai yarinya ba ki kai ba”
“Yaya kawai ƙaramin jiki ne dani fah, amma anyi auren ƙannena har biyu yanzu ma an kusa wasu biyun” sai da ta yi maganar sai kuma taji haushin maganar da ta yi.