SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Su na cikin mota amma ba wanda yai wa ɗan uwansa magana. Farida ta kamo hannun sa ta kai kan cikin ta tana faɗin “baby ya missing ɗin ka sosai”
Zare hannunsa da yai daga kan cikinta ya sa ta zaro ido. Tana binsa da kallon mamaki, juyar da kan sa yai yana kallon titi.
Hawayen baƙin ciki su ka fara zubo ma ta.
“Wai mi ke faruwa ne?” Ko lokacin da bai gane ta ba a asibiti farkon farfaɗowan sa ai ba ya ma ta wannan walaƙanci balle yanzu da su ke tsaka da soyayya. Wai har cikin da ke jikinta ma bai damu da shi ba.
Ba ta kuma yunƙurin yin wani abu ba har su ka isa gida. Ido kawai ta ke binsa da shi duk abubuwan da ya ke yi.
Tana ganin ya zauna a bakin gado yana shirin kwanciya ta zo gaban sa. Tsugunnawa ta yi ta riƙe gwiwowin sa duka biyu.
“Na roƙe ka da girman Allah Ubangiji Mai Rahama. Ka yafe min mijina, na yadda na yi ma ka laifi a rashin sani amma ka yafe min. Horon rashin magana da halin ko in kula ya min tsauri. Mijina abin so na, abin muradi na. Kai kaɗai ka mallake zuciyar Aisha Farida. Ba ni da tamkar ka kuma ba zan taɓa samun tamkar ka ba, ka yi haƙuri dan Allah ka gaya min mi na maka ka kuma yafe min. Idan ka cigaba da haka ciwon zuciya zai kasheni….” kuka ya kufce ma ta.
Duban ta ya ke yadda ta ke ta sheshsheƙar kuka, maimakon ya ji tausayin ta sai ma ran sa ya ɓaci.
Da kakkausar murya ya ce ” you liar, ba ki da wani bayan ni? Oh really! Shi ne daga fita na ki ka kira tsohon saurayin ki ya ɗebe mi ki kewa kafin na dawo ko?”
Shiru ta yi tana rarraba ido dan ba ta gane maganar sa ba.
“Tsohon saurayina kuma? My Champ….”
“Oh please! Ba na son jin komai ki je ki yi duk abinda ki ke so”
“Wai Lukman ka ke magana? Haba My Champ, haba. Tsakanina da Lukman ya zama tarihi”
Miƙewa yai ya ɗau pillow zai fita ta riƙe ƙafar sa.
“Dan Allah ka tsaya na ma ka bayani. Wallahi ba abinda ka ke tunani ba ne”
Turata gefe yai ya fice abinsa.
Farida ta fashe da wani sabon kukan. Ba abin da ya fi damunta irin wai duk hukuncin nan akan zargi ne. Ta ya zai zargeta, wani irin so za ta nuna ma sa ta tabbatar babu wani namiji a rayuwarta da ya wuce shi. Tafi minti talatin tana kuka kafin ta tashi ta shige banɗaki ta ɗauro alwala.
Bayan ta yi sallah ta zauna a sallayar tana kuka tana gayawa Allah buƙatunta. Ta jima tana addu’a kafin ta naɗe sallayar ta je ta kwanta. Ba abinda ke ranta irin cin uban Naomi da za ta yi gobe, tunda ita ce ‘yar burauban da ta haɗa ta da mijinta, ta ma ta ƙaryan mijinta bai zo ba ranan. Ashe ya zo har ya ganta da Lukman.
Ta jima tana saƙa da warwara kafin bacci yai gaba da ita.
…………………….
Washegari tun da sassafe ta kira Sabreen akan dan Allah ta shirya za ta mata wani taimako. Sabreen ta amsa da ba matsala.
Karyawan kirki Farida ba ta iya yi ba. Zuciyarta ke tafarfasa yana zafi. Ba ta san sadda ma Najeeb ya fita ba tana tsammanin ƙila lokacin da ta koma na ta ɗakin ne…
Kamar jiya ma dai Najeeb cewa yai ya kai shi gidan su Naomi. Jin haka ya sa Abdullahi ɗaura aniyar dole ya sanar da Farida, domin gaskiya akwai lauje cikin naɗi a wannan al’amarin.
Naomi ta yi farin cikin ganin Najeeb garau ba kamar jiya da ya ke rai a hannun Allah ba. A cikin motan hannunsu sarƙe cikin na juna har su ka isa kamfani…
Suna isowa sai ga Anas shima motar sa ta yi parking. Da sauri ya fito ganin Najeeb da Naomi sun fito mota ɗaya.
“Najeeb… Najeeb” Anas ya kira shi da ƙarfi da ke sun riga shi fitowa a mota.
Najeeb ya juyo ya kalli Anas. Kallon tuhuma Anas ke wa Najeeb ɗin har ya iso.
“Good morning Sir” Naomi ta gaishe da Anas tana murmushi.
Ko amsawa bai yi ba ya ce ta basu waje. Naomi ta yi gaba tana tafiya tana yauƙi.
Anas ya kalli Najeeb ya ce “mi ke faruwa Najeeb? Mi ya sa za ku taho tare kai da sakatariyar ka? Ina Farida?”
” Dude ka ci sa’ido. Ina Baby? Fatan ka na kula min da ita sosai”
“I’m serious Najeeb. Mi ke faruwa?”
Najeeb ya ɗan buga kafaɗar sa ya ce ” kar ka cika ni da surutu we have board meeting today”
Girgiza kai Najeeb ya fara yi yana neman yaƙi da abinda zuciyar sa ke raya ma sa. Najeeb ba zai taɓa haka ba, ba halin sa ba ne, No.
Ya jima tsaye kafin ya bi bayan Najeeb wanda tuni ya shige ciki…
Ƙarfe tara da rabi Farida da Sabreen su ka iso Kamfani. Tun a mota Sabreen ke tambayar Farida me ke faruwa amma ta ka sa gaya ma ta. Cewa kawai ta yi za ta ba da wani shaida ne.
Farida kam cikin zuciyar ta ayyana yadda za ta yi ƙuli-ƙulin Kubra da Naomi ta ke yi…
Kai tsaye sama su ka wuce. Sabreen na ta cewa ta yi a hankali saboda condition ɗin ta.
Su na isa office ɗin kuwa Naomi na fitowa daga office ɗin Najeeb.
Belt ɗin Najeeb da ta sa a jaka ta ciro, ta yi kan Naomi da sauri. Naomi ba ta ankara ba ta ji saukar belt a bayan ta. Dama ta gan su, ta kau da kai ne kawai, saboda yanzu ta gama convincing Najeeb akan ya aureta kuma ya ma ta alƙawarin zai auretan. Tunda za ta zama matar Najeeb mi zai sa ta wani tsaya ba wa Farida girma…
Farida ta sake warɓa ma ta belt ɗin tana masifa “shegiya mai kaman Aladu, ke ce sheɗaniyar da ki ka haɗa ni da miji na ko”
A na huɗu da ta kai ma ta dukan ne Naomi ta riƙe belt ɗin tana huci.
” ‘yar iska ramawa za ki yi? Bismillah, rama” ta jawo gashin Naomi ta falla mata mari. Naomi ta challa ƙara tana kiran sweetheart.
“Kan Uban chan, mijina ne sweetheart ɗin ki” ta sake yowa kan ta. Naomi ta shige office ɗin Najeeb da gudu.
“Ayshah take it easy” abinda Sabreen ke ta faɗa kenan.
Farida ta cire gyalenta ta miƙawa Sabreen ta ce ” yau yarinyar nan za ta san da wa ta ke ja, sai na chanja ma ta kamannin ta”…
Numfashin ta sai da ya kusa ɗaukewa saboda abin da idon ta ya ci karo da shi. Najeeb ne tsaye gaban Naomi yana goge ma ta hawaye da hankerchief ɗin sa.
“My Champ” kawai ta iya faɗa bakin ta na rawa.
Ya kalleta da idon sa da su ka rikiɗa su ka koma ja….
SAKATARIYA TA
…….(My Secretary)…….
Azizat……✍
Wattpad @000Azee
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
0️⃣5️⃣3️⃣
“Mi ya sa ki ka dake ta”
Najeeb ya faɗa da ƙarfi.
Mamaki, tsoro, kishi, baƙin ciki su suka haɗu su ka hana Farida Magana.
“Sorry, sorry dear” ya faɗi yana bubbuga bayan Naomi.
Sabreen ma dai mamakin ne ya cikata. Da ƙyar ta iya cewa ” Noory what’s this?, what’s happening here?”
“This should be the last time da za ku taɓa min ita, she’s very special to me, duk abinda ya taɓani ya taɓa ta”
Maganar da yai ya sa hawayen da Farida ke tarewa su ka fara zubowa.
“Najeeb akan wannan Kafirar ka ke min walaƙanci tun shekaranjiya? Akan wannan fasiƙar?”
“Please ku bar min office ba na son hayaniya” ya faɗa tareda kwanto da kan Naomi jikin sa.
“Noory what’s wrong with you?” Sabreen ta faɗa ganin yadda Najeeb ya bada hankalin sa kwacokam a wajen Naomi.
Zuciyar Farida kaman za ta bulluƙo tsabar yadda ta ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. A hankali ta tako gaban su tana kallon cikin idon Najeeb.
Naomi ta sake narkewa jikin Najeeb tana kukan munafurci.
“Wallahi yau ka ce kana son Sabreen za ka dawo da ita rayuwar ka. Zan yi kuka, zan ji baƙin ciki, amma daga baya zan rarrashi kai na na amince ma ka. Amma wannan?”
Ta faɗa tana nuna Naomi.
“Ba zan taɓa amincewa ba har abada”
“Fine, dama ba amincewar ki na ke nema ba. Infact we are getting married soon”
Ta buɗe baki za ta yi magana amma sai hawaye. Ta juya da sauri ta fita, Sabreen ta bi bayan ta da gudu…