SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ganin halin da ta ke ciki ya sa dole Sabreen ta raka ta gida. Kuka ta ke cikin motar kaman ranta zai fita. Da ƙyar Sabreen ta dinga rarrashin ta saboda abin cikin ta…

Kwanciya Farida ta ce za ta yi hakan ya sa Sabreen ta ma ta sallama tareda cewa za ta gayawa Mom abinda ya faru dan abin ya ɗaure ma ta kai…

Sabreen na tafiya Farida ta shiga haɗa kayan ta.

………………………

“Wato dai ba za ki gaya min mi ya dawo da ke gida ba ko”
Farida ta juyar da kai ta cigaba da hawaye.

“Ki tashi ki koma gidan ki kafin Baban ku ya dawo”

“Ummi kafira ce fa, wai kafira zai aura. Akan ta ba irin walaƙancin da bai min ba. Ni na haƙura, ya je ya auretan zai gani ai”

“Najeeb ɗin?”

“Ummi cikin ido na fa ya kalla ya ke faɗa min wai zai aureta. Ko na amince ko ban amince ba babu ruwan sa aurenta zai yi” ta fashe da kuka.

Ummi ba ta yi ƙoƙarin hanata kukan ba sai ma nazarin maganganun Faridan da ta fara yi wanda ta ke ganin ba lafiya ba. A yadda ta karanci Najeeb yana tsananin son Farida ba zai taɓa ma ta walaƙanci haka kawai ba musamman yadda ta ke da cikin nan.

Rarrashin Faridan ta shiga yi saboda cikin jikin ta…

Sabreen na zuwa ta sanar da Mom abinda ya faru. Mom ta ka sa gaskata hakan, ta ɗau waya ta shiga kiran Najeeb amma bai ɗauka ba. Mom ta ce ba ta ga ta zama ba dole su je har kamfanin ta ji bahasin wannan sabon salo na shi…

Da su ka je ba su same shi ba. Shi da Naomi sun fita. Mom ta je office ɗin Anas shima baya nan ya fita. Haka su ka dawo gida tana jira Daddy ya dawo ta sanar da shi komai…

Farida kashe wayarta ta yi lokacin da ta ga Anas ya dameta da kira. Bayan ta yi sallar Azahar ta samu ta kwanta saboda baccin da ba ta samu ta yi jiya ba.

Anas kuwa ya ga lokacin da Najeeb da Naomi su ka fita. Yana kiran Najeeb amma ya ƙi kula shi. Farida ya shiga kira amma ba ta ɗauka ba, ƙarshe ma aka kashe wayar. Hakan ya sa ya je ya shiga mota ya wuce gidan su. Da ya isa gidan Tasallah ke gaya ma sa Farida ta tafi gidan su kuma yanayin kayan da ta ɗauka kaman yaji ta yi.
Hankalin Anas ya kuma tashi yana tunanin mi ke faruwa tsakanin wannan masoya.
Gidan su Farida ya wuce direct. Da ya isa ya aika yaro akan ya kira ma sa Farida inji Anas. Yaron da ya shiga ya samu Ummi ya gaya ma ta. Ummi ta aiki Zainab ƙanwar Maijiddah akan ta cewa Anas Farida ba ta jima da bacci ba. Za ta kirashi idan ta tashi.

Anas dai ya tafi ne amma ya so ya ga Farida ya tambayi mi ke faruwa. Yana hanya saƙon Mom ya shigo akan idan ya tashi a waken aiki ya zo gida…

……………………

Bayan la’asar ta farka. Kuma Alhamdulillah zuciyarta yai sanyi.

Sai da Ummi ta tabbatar ta ci abinci sosai sannan ta shiga ma ta nasiha tareda faɗa ma ta illar baro gidan ta da ta yi.

“Ummi to na koma na ma sa mine? Bayan ya samu ‘yar ma su fitsari a tsaye yace yana so”

“Farida kenan, har yanzu da sauran ki. Wa ya gaya miki zaman aure zaman jin daɗi ne na dindindin. Ki koma gidan ki ki cigaba da yiwa mijin ki addu’a har Allah ya warware mu ku matsalar da ku ke ciki. Ni ina tunanin ba haka yarinyar nan ta bar shi ba. Amma addu’a ya fi ƙarfin ko wani sharri dan haka shi za ki riƙe”

Maganganun Ummi ya sa jikin Farida yai sanyi. Sai yanzu ne zuciyar ta ya fara wannan tunanin. Ƙila Naomi ta yiwa Najeeb wani abu ne…

Cikin ruwan zamzam da su ka zo da shi daga saudiyya Ummi ta ɗauko ta kawo ma ta. Sai a lokacin Faridan ma ta tuna su ma na su da su ka zo da shi bai ƙare ba. Ta amsa tana yiwa Ummi godiya.

“Kar ki saka damuwa a ranki dan Allah, ki riƙa tashi da dare kina yiwa mijin ki addu’a, sannan wannan ruwan zamzam ɗin ki dinga haɗa ma sa a ruwan shan sa, abinci dama shayin da zai sha. Ki riƙa tofe makwancin sa da kuma inda ya saba zama da Suratul Falaƙi da Naasi saboda suna maganin asiri da sheɗanu”…

Ƙarfe bakwai saura ta isa gida. Kunna wayarta da ta yi ta ci karo da saƙonni. Biyu daga Anas sai ɗaya daga Mom sai ɗaya daga Lukman inda ya ke ma ta godiya domin Sabreen ta amince da shi. Na ƙarshen ne ta ga Abdullahi dreba inda ya ke cewa “Hajiya dan Allah akwai maganar da na ke son gaya mi ki gameda Oga”.

Ta turawa Lukman saƙon taya murna kafin ta kira Abdullahi. Da ke yana tareda Najeeb a mota sai bai ɗauka ba. Da aka sake kira sai ya ɗauka ya ce ” ina tuƙi Hajiya, mun ma kusa isowa gida”

Farida ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta kashe kiran.
Numbar Mom ta kira dan saƙon na ta cewa ta yi ta kira ta dan Allah.

“Ayshah ki na lafiya?”

“Lafiya Mom” ta amsa tana ƙoƙarin saita maganarta.

“Anas ya ce min kin koma gidan ku, dan Allah ‘ya ta ki dawo, zan zo gidan na ku gobe”

“Mom na dawo ma, yanzu haka ina gidan”

“Allah ya miki albarka”
Farida ta amsa da amin…

Bai fi minti shabiyar ba sai ga Najeeb ya shigo gidan. Tana zaune a falo tana kallo ya shigo, a zahiri za ka ga kaman kallon ta ke amma ba kallon ta ke ba, hannunta akwai carbi tana jan Ya Hayyu Ya Qayyum.

Ba ta ma sa magana ba haka ya hau sama da gudu kaman zai tashi sama.
Tana ganin ya shiga ta kira Abdullahi akan ya shigo…

Duk yadda ta yi ya zauna a kan kujera ya ƙi. A ƙasa ya zauna su ka gaisa.

“Malam Abdullahi ina fata lafiya?”

” Hajiya dan Allah ki yi haƙuri da abinda zan gaya mi ki”

Farida ta ce ba komai.
Nan ya shiga gaya ma ta abinda ya lura tsakanin Najeeb da Naomi. Ya faɗa ma ta jiya da ya kai su hotel ne Najeeb ya fara ciwo amma da lafiyar sa ƙalau. Ya ƙara da cewa ” Hajiya kar ki tsorata amma akwai asiri ajikin Alhaji. Wannan cegiyar arniyar ta yiwa Alhaji asiri”

Duk da gaban ta ya faɗi amma hakan bai sa ta ji tsoro ba, dan tunda Ummi ta ba ta shawarwari ta sa a ranta sai inda ƙarfinta ya ƙare akan yiwa Najeeb addu’a.

Ta yiwa Abdullahi godiya ta sallameshi…

Sai da ta leƙa ɗakin sa ta ga yana bacci kafin ta wuce na ta ɗakin. Ɗazu ta tsiyayi ruwan zamzam a hannunta ta tofa ƙula’uzai a ciki sannan ta yayyafa a gadon sa da duk kujerun sa…

Ƙarfe biyu da rabi ta tashi ta fara gabatar da sallah tana addu’a ba ta kwanta ba har asuba. Ƙarfe shida ta fito ta taya Tasallah haɗa ma sa breakfast duk da ma Tasallah ta ce tea kawai ya ke sha yanzu. Acikin tea ɗin ta tsiyaya ma sa ruwan zamzam kaɗan wanda shima ta tofeshi da addu’o’i…

Da za ta haura sama ta ce da Tasallah ta kai kuɗi gidan da ake musu kunu da ƙosan sadaka lokacin da Najeeb bai da lafiya su ma ta sadaka.
Ita kan ta Tasallah ta san akwai matsala a gidan dan masoyan da kullum su na manne da juna sai ga shi yanzu ko kallon kirki ba sa yiwa junan su.

Saboda bacci da ke idon tana shiga ɗaki bacci ta yi. Ba ta farka ba sai ƙarfe tara. Ta yi wanka ta shirya ta sauko. Kaman yadda Tasallah ta ce tea ɗin kawai ya sha ya fita.
Ta zauna a dining ta ci abinci sosai, ba wai dan daɗi ba sai dan ɗan da ke cikin ta.

Ƙarfe shaɗaya ta wuce gidan su Najeeb. Mom ta riƙa ba ta haƙuri tareda da nuna ma ta Najeeb yana cikin matsala dan jiya sa’insa su ka yi da Daddy akan ya ce zai auri Naomi.

Cikin kuka ta ce ” he has never raised his voice to his father, amma jiya…” kuka ya kufce ma ta.

“Mom dan Allah ki dena kuka, addu’a za mu dinga ma sa har Allah ya kawo ma na ƙarshen wannan bala’i”…

Ta jima a gidan dan sai bayan Azahar ta tafi.
Anguwar su ta wuce amma ba ta kai gida ba ta tsaya a gidan su Saminu.
Saminu abokin Yakubu ne, amma tun secondary school ya lalace da shaye-shaye. Yanzu haka ba shi da aikin yi sai maula gidan ‘yan siyasa, idan lokacin zaɓe ya zo sune ‘yan bangan siyasa.
Duk da halin su da ya banbanta amma ba su dena mutunci da Yakubu ba. Lokaci zuwa lokaci yana zuwa wajen Yakubu ko kuma su haɗu a majalisa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button